18

601 34 7
                                    


18

Kan ka ce kwabo, hawaye ya wanke wa ummi fuska, har wata irin sheshsheƙar kuka take yi, dan kuwa da ace ta koma gidan Idris, gara a yanke mata hukuncin kisa, dan tana kyautatawa Allah zato a dukkan lamuranta, tayi imanin za ta dace da rahamar sa.

Iya cikin masifa ta ce "To kukan uban me ki ke yi, ba taimaka miki zai yi ba? ke a wannan munin naki uban waye zai aure ki? Kalli fuskarki fa kamar buredi ya ƙone ƙurmus, har wani zaɓi ne da ke? Ke gaki nan ba ke ba mutum ba ke ba aljana ba".

Kawu yahaya ya ce "Iya, lokacin da Allah ya halicci ummi fa, bai yi shawara da kowa ba, balle ace laifinta ne, ko wani abu ne ya sanya ubangiji yin halittarta a haka, halittar ummi hurumin ubangiji ne, dan haka bai kyautu a din ga ci nata fuska ba, kuma wallahi ummi ba ta da muni".

"Ka ga ni kar ka yi mini wa'azi, ai maganar gaskiya ce, tun da Allah ya sa ita ba wata mamora ce da ita ba, balle ace za a samu mai kwasa ai duk sai a manta da abun da ya faru a baya ko? Tun da har da kansa ya ce ta dawo ɗin, sai a ja masa kunne"

Dr. Ya kalli in da ummi ke zaune tana ta sheshsheƙar kuka ya ce "Ummana, jeki ɗaki abunki kin kwaso gajiyar sauka" ummi ta tashi zuciyarta na harbawa da sauri, ta tafi ɗakinta tana kuka, tare da adduo'i kala-kala a zuciyarta, tana fatan Allah ya sa kar kawu ya amince da abun da iya take faɗa. Dan har ta mutu ba za ta manta da azabar da ta sha a gidan idris ba, ko maƙiyinta ba ta fatan yayi rayuwa irin wadda ta yi a gidan idris.

Noor ta bita ɗakin tana kiran sunanta.

Kawu ya kalli Iya ya ce "Iya, ko ummi ta amince ko bata amince ba, ba zan sake bawa Idris ita ba, yaron nan gaba ɗaya jahili ne, wallahi da mutumin kirki ne, idan ta gama sakandare sai a mayar da auren, amma ni ba zan goyi bayan a cuci ɗan wani ba, yadda ya yi wa ƴar mutane ciki, ku je can ku nema masa mafita, dan baban yarinya bai yi laifi ba.
Iya kin manta lokacin da ya din ga terere da ummi, yana tona mata asiri ga larurar da ke damunta? Shi meyasa ba a tursasa shi ya shanye dauɗar gorar ba, sai ummi?
Allah da ya halicceta a haka in dai muna raye, zai bata abokin rayuwa na gari, haka zalika ba zan riƙe ƙato da bai san ciwon kansa kamar idiris ba, can ƙauye ya gagareku balle ni a nan, dan Allah kiyi haƙuri a bar wannan zancen. Ummin ma da kanta ta nuna ba ta so, dan haka dan Allah dan annabi a bar wannan maganar. Kuma ina baku shawarar mayar da idris makaranta kan a kuma bashi wata matar ya aura, dan kuwa jahilci ke ɗawainiya da shi".

Cike da takaici iya ta kalle shi ta ce "Haka ka ce?"

"Ba faɗa na yi dan na ɓata miki rai ba, amma gaskiya ce" Iya ta yi ƙwafa ta ce "Shikenan na tabattar da uwarka ce ba zaka tsallake umarninta ba, kuma da cikin ku ɗaya da baban Idris ba zaka so asirin sa ya tonu ba".

Ya girgiza kai ya ce "Iya ai kin san mu kallon uwa muke yi miki, amma kowa ya ɗebo da zafi bakinsa, kin riga kin sangarta Idris, komai yayi ba zaki bari duniya ta hora shi ba, sai kin kare shi, kema yakamata ki hutawa ranki, ba shikaɗai ne ɗa a dangi ba".

Ba ƙaramin takaici Iya ta kwasa ba, yadda ƙiri-ƙiri yahaya yayi burus da maganarta, ya zaɓi tonuwar asirin su.

Dan haka ta ce masa babu ita babu ummi, tun da haka suka zaɓa, ya ce bakomai, Allhan da ya yi ummin zai kula da ita.

Ko zama ba ta sake yi ba tun da ta tashi, ta ce magaji ya samo musu mota a tasha, kawu yahaya ya biya kuɗin motar, ya basu kuɗin kashewa, suka tafi.

Ummi sai da tayi sujjadar godiya ga Allah, ga saukar Alqur'ani mai girma, ga kuma fasa mayar da aurenta da idris da aka yi.

Duk da kuɗin da yahaya ya bawa Iya sun saka ta ɗan sassauta fushinta, amam ta sha takaicin rashin amincewa ya ɗauki Idiris a mayar da aurensa da ummi, ta din ga zagin ummi tana tsine mata, tamkar ba ita ta haifi baban ummi ba, tare da janyo mata jafa'i kala-kala.

CUTARWA!Where stories live. Discover now