37

945 59 14
                                    

                           *CUTARWA*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

37

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143

MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.

Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.

*Alhamdilillah ala kulli halin, ina amfani da wannan damar, wurin isar da ɗimbin godiyata ga ƴan uwana marubuta, tarin masoya makaranta, da sauran al'ummar da suka yi mini ta'aziyyar rashin kakata, ina fatan Ubangiji Allah ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, ya kuma bar zumunci, yayi mana jagora a rayuwa baki daya, Allah ya sanya kaburburan magabatanmu ya zama dausayi daga aljanna, idan tamu ta zo ya sanya mu cika da imani*

37

A razane yake kallon ummi daga sama zuwa ƙasa, iya kuma ta miƙe tsaye da sakakken baki ta kasa magana.

Ummi ta durƙusa ta ɗago yarinyar da take zubar da wani irin yawu daga bakinta, saboda wahalar duka.

Noor kuwa na gefe tana tsuma, duk da basu saba ba, tare suka yo cefane, har noor ta bata shawarar su sayo taliya sai tafi sauri, tun da ummi ba ta gaya musu me zasu sayo ba.
Suna tafe a hanyar ta kalli noor ta ce mata "Ya sunanki?"

"Sunana mariyatul kibɗiya, ana ce mini noor"

"Masha Allah, sunanki me daɗi"

Noor ta ce "To ke ya sunanki?"

"Wai hajara, sunan kakata aka saka mini, ni kuwa na ce wallahi bana so, na canza suna ake ce mini Nana"

"To meyasa ba kya so, ba kakarku ba ce? Au kamar sunan iya ne ai ko?"

Nana ta ce "Eh mana, baki ga yadda ta tsane ni ba, ni ma kuwa na tsaneta, yauwwa idan kuɗin yayi ragowa muka sayi kifi, ba za ta ce komai ba?"

Noor ta ce "Ai idan ma kifin ki ka saya da duka kuɗin babu abun da za ta ce miki, yaya ummi fa babu ruwanta"

Nana ta ce "Na gani, kin san wani abu, wallahi ta burgeni, ga muryarta mai daɗi, a nutse take komai, sau ɗaya na taɓa ganinta sun zo da kawu yahaya, ƴar sa ce?"

Noor ta ce "Ke, ni ma fa ƴar sa ce, iya duk kakarmu ce kenan? To ya aka yi ban sanki ba"

Noor ta ce "Ni ba kakata ba ce ba, kakana ta haifa dan haka babu abun da ya yi mini zafi da ita"

Wani yaro suka haɗu da shi a hanya ya ce "Nana, ana ta nemanki a gida, wallahi ki je gida baba yana nemanki"

"Ba zani ɗin ba, in je a jibgi jaka, gidan iya zan je, tayi baƙi za a dafa abinci, sai na ci na dare zan dawo gida"

Mamaki ya kama noor, jin amsar da ta bayar, da aka ce babanta yana nemanta.

Sai dai sun shiga sashin iya sun yi sallama babu jimawa, Nana ta fara ɗaukko kwanukan da zasu yi amfani da su su yi girkin, Idris yayi sallama da itacensa a hannu, ya fara jibgar Nana.

CUTARWA!Where stories live. Discover now