CUTARWA!
AYSHERCOOL
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
46
PAID ADVERT
*Hajiya ina zaki? Saurin me ki ke yi haka? Ɗan bani aron mintuna biyu kacal, na gaya miki albishir ɗin da na zo miki da shi. Shin ko kin san sirrin sheƙin fatar ummi, da ya sanya ta kama zuciyar MD raihan ta hana shi sukuni? Kai ba ma skin care ba, har da sirrin gyaran gashi, ina masu fama da amosani, karyewar gashi ko kuma sanƙo, jan gashi ne da ke? Ko taurin gashi kamar soson ƙarfe. Idan matsalar ki budurwar fata, tare da rashin glowing, Annur skin scrub da hair bliss sun shirya tsaf domin magance muku kukanku, me ku ke jira ku tuntuɓe su a kan lambar wayar su dan ƙarin bayani 07045971194 ko 08140450950*
46
Wata irin zabura farida ta yi, ta fizgo babbar rigar dr. Ta ce "Ni! Ni yahaya wai da gaske ka ke ko wasa?"
"Na taɓa yi miki irin wannan wasan ne? Na yi aure kamar yadda na gaya miki"
Girgiza kai ta yi ta ce "Ni zaka ci wa mutunci, wallahi idan bacci ka ke gara ka farka, dan baka isa ba, da can da ƙuruciyata ba ka yi mini kishiya ba sai yanzu? Wallahi ba zai yiwu ba ba a gidana ba"
Ya fizge hannunta ya ce "Ni nake aurenki ba ke ki ke aurena ba, farida rashin mutuncinki da wulaƙancin da ki ke yi mini, ya sanya na yi miki koma menene. Aikin gama ya riga ya gama, zan gyara tsohon gidana na sakata a ciki, nan da sati ɗaya zuwa sama idan visarta ta zama ready zan tafi da ita uganda. Zan saka miki dubu ɗari biyu da hamsin a account ɗinki, kya sayi wani abun"
"Dubu ɗari biyu da hamsin ɗinka ta banza da ta wofi, wallahi ba zai yiwu ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ya riga ya yiwu ma, ba wata ba ce na aura a waje, mariya ce mahaifiyar ummi, abun da yakamata na yi ne tun a baya, ban samu dama ba, sai a yanzu"
Farida ta ce "Ka rasa wadda zaka auro a matsayin kishiyata sai mahaukaciya, wallahi yahaya kai butulu ne azzalumi wallahi ba zan zauna da mahaukaciya ta kashe ni a banza ba, kai ba zai taɓa yiwuwa ba ma wallahi ni zaka tozarta?"
Ya tsaya ya ƙare mata kallo ya ce "Farida, duk abubuwan da suke faruwa a baya, kallonki kawai nake yi, tsantsar zaluncin da ki ka yi wa yarinyar nan a zamanta da ke, ina kallonki, saboda ba ki da mutunci kin mayar da ni ɗan iska da son nuna wa duniya ban isa da gidana ba, auren ummi ya samu matsala ta zo gidan ki koreta ga dare, saboda baki da hankali kin san yadda nake jin yarinyar nan a raina kuwa? Ita kaɗai take babu wa ba ƙani, ki yi mini alfarma ki riƙeta da mutunci ki ka gaza, bayan ni na riƙe taki ƴar uwar babu cuta babu cutarwa? Wannan dalilin ne ya sanya na ga lallai yakamata ummi ta ƙara shigowa cikin iyalina in sama mata farinciki ta hanyar auren mahaifiyarta, na san kome zai sameta a rayuwa ba zata taɓa korarta ba"
Tayi wata irin shewa mai cike da takaici ta ce "To ayi mu gani? Wannan dai ba abun da zata tsinana maka, ba uban da zaka tsinta a tare da ita, ka ce auren na ramuwar gayya ne? To ka yi mu gani, wallahi sai ka yi bankwana da farinciki da kwanciyar hankali har abada".
Ya nufi gadonsa yana faɗin "Allah ba zai gwada mini rashin kwanciyar hankali ba, in sha Allah auren nan alkhairi ne a gareni"
***
Cikin mamaki da takaici mami take kallon hajiya, da take yi mata dariya cike da son tura mata takaici.
Ta ce "Wato Alhaji a duniya mace ta samu nagartaccen miji irin raihan, to ta ɗaga hannu ta godewa Allah ta haye, yaron kirki Allah dai ya ja zamanin babban mutum"
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...