CHAPTER 8

544 25 1
                                    

                    *CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
What's app 08081012143

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P8

Tuni ummi ta zabura, ta jefar da kwanon hannunta, jikinta ya hau rawa, a fusace ya ƙaraso kan ummi, yayi ball da ita ta hantsila cikin kwanukan da take wankewa.

A cikin azama hashim ya ƙarasa, ya hankaɗe idiris, yana faɗin "Idirs meye haka?"

"Ban gane meye haka ba, ba kaga abun da ta yi mini ba? Dabbar ina ce? Ko makauniya ce?"

"Kai za a cewa dabba,  ya za ayi ka shigo babu sallama, ya za ayi ta san da zuwan ka? Idiris zaluncin da ka ke yi wa yarinyar nan yayi yawa fa"

Ummi kuwa karo tayi da ƙafar tukunyar ƙarfe, fiƙarta ɗaya ta karye, nan da nan bakinta ya rine da jini, kuka take yi sosai, saboda ciwon buguwar da tayi, har cikin kanta take jin azabar ciwo.

Babarsu da ta jiyo hayaniya ta fito tana faɗin "Wai lafiya ku ke yi mini hayaniya da tsakar ranar nan?"

Idonta ya sauka a kan ummi, da yawun  bakinta ya gauraye da jini".

"Ita kuma wannan meya sameta?"

"Ga wanda ya yi ball da ita cikin kwanuka nan" Hashim yayi maganar cikin takaici, yana nuna idiris.

Nuna wa mahaifiyarsu kayansa yayi, da ummi ta ɓata da miya.

Hashim bai tsaya jin abun da mahaifiyarsu za ta ce ba, ya ja hannun ummi, ya tafi da ita.

Sun sha yawo sosai, kan su samu chemist, kasancewar salla ce, aka bawa ummi magani.

Haka aka gama bikin salla, ummi ba kayan salla sai jinyar baki, da ya sanya ta ciwon kai sosai da sosai.

***
Mariya na zaune a ɗaki tana ninkin kaya, fuskar nan kamar wadda aka yi wa mutuwa, tana jiyo hirar da mama, da jimmai maƙwanciyar su suke yi, wadda ƴar ta aka kai gagarawa, suka haɗu da balarabe suka yi aure.

Tana bawa mama labarin ƴar ta mijinta ya samu sauyin wurin aiki zuwa ikko, sun bar gagarawa.

Mariya ta yi shiru, tana tunanin ya aka yi ba tayi tunanin ta din ga bayar da abu, idan an samu mai zuwa gidan ƴar jummai a kai a bawa ummi ba.
Sai dai ta tuna ba shiru suke yi ba, dan ƴar gidan jimmai, tana ganin tana auren mai kuɗi mijinta ɗan sanda ne, idan suka haɗu da mariya a hanya, kamar ba su san juna ba, saboda yadda take jin kanta.

Tunaninta ne ya katse lokacin da ta jiyo jimmai na cewa "Ai nan asalamiyya ke bani labari, ƴar da mariya ta baro, wahala kawai take sha, ranar ta ganta ko takalmin kirki babu a ƙafarta, na ce ta ɗan din ga taimaka mata, to kin ga ma yanzu sun bar garin, na ce da kun je kun ɗaukko yarinyar nan"

Mama ta ce "Da zai yiwu da anyi hakan ai, ba yadda ba ayi ba su bayar da Yarinyar sun ƙi, shiyasa muka ƙyalesu, ba su da mutunci ko kaɗan, da aka je musu da maganar cikin mariya, cewa suka yi ba nasu bane ba, shiyasa malam ya ce babu mu babu su, a ƙyale su idan yarinyar ta girma ta nememu"

Jimmai ta ce "Ashsha! To Allah ya kyauta".

Mama ta amsa da "Amin"

Mariya ta ajiye ninkin, ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka.

Bayan tafiyar jimmai, mama ta shiga ɗakin, dan ta san mariya na jin su, ta ce "Mariya na san kin ji abun da jimmai take faɗa, amma haƙuri zaki yi ki kawar da kanki, ki sakawa zuciyarki salama a kan yarinyar nan, idan ba haka ba kuwa ciwo zai cigaba da cin jikinki, kin san dai ki na da hawan jini"  shiru mariya ta yi, ta cigaba da rera kuka, mai ƙona zuciya, tana ji a ranta ba zata taɓa yafe wa Iya ba.

CUTARWA!Where stories live. Discover now