*CUTARWA!*Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube Cool hausa novels
What's app 08081012143BRIGHT PENS
(FREE BATCH)3
Yanayin da suke ciki, bai sanya iya ja da baya ba, mussaman yadda suka rikice tamkar marasa gaskiya.
"Ina jin duk abun da ku ke faɗa ai, idan ta tafi ta barka ka yi yaya, tun da ta fini a wurinka, kar Allah ya sa ta zauna ɗin mana, ta ƙara gaba, wataƙila dama ita ce ƙashin tsiyar da ta tokare maka ƙofofin arziknka, har ni zan gindaya umarni, ka zo kana lallaɓata? Ki tafin mana waye ya riƙe ki? Ke idan ƴar mutunci ce ina uwarsa har sai ya nemi shawarar ki sannan zai bi umarnina?. To ke idan ban isa da ke ba, na isa da ɗa na, dan haka ki san abun da yake yi miki ciwo, idan ƙabilar ku kun saba asiri ku mallake mazaje, to ni na yi wa kaina da ƴaƴana dafa'i, asirinku bai isa ya kama ni ba"
Ba yau iya ta saba yi musu laɓe ba, dan haka yanzun ma mariya ba ta yi mamaki ba, dan idan da sabo ta saba.
Iya ta sake jaddada musu duk wanda ya fasa abun da ta ce a rufe, bata yafe ba.
Baban ummi ne ya yi ta bata haƙuri, mariya kuwa ta haɗe rai, wani abu mai ɗacin gaske na kaiwa da komowa a ƙirjinta, ji take kamar ta tashi ta ɗurawa Iya ashar, wanna ai shi ake kira da ga mari ga tsinka jaka, gaba ɗaya tsohuwar nan ba ta da imani, ba ta da mutunci, abu ɗaya take girmamawa a rayuwarta shi ne kuɗi.
Bayan sun samu ta fita, ya leƙa ya tabbatar ta tafi, sannan ya dawo ya cigaba da rarrashin mariya, ganin ya shiga tsaka mai wuya, ya sanya mariya ce masa "Ka kwantar da hankalinka baban ummi, ba wanda zai ji maganar nan, ina fatan Allah ya yi wa ummi sakayya, ba wanda zan bari ya sani"
Ya ce "Yauwwa, Allah ya yi miki albarka, in sha Allah zan san abun yi, zan yi ƙoƙarin neman fili a garin nan, na gina mana ko ɗaki ɗaya ne da makewayi, mu koma can, ko kema kya samu sassauci.
Kallonsa kawai take yi, cike da tausayawa dan kuwa ta san tun da iya ta gama raina masa wayo ba shi da abun duniya, ba zata taɓa barin sa ya bar gidan ba, ko dan kar ta huta.
A zahiri kuma ta ce "To Allah ya yassare" ya amsa da amin sannan ya tashi ya fita.
***
Jujjuyar lokaci ya sanya abubuwa cigaba da gudana, wasu da daɗi wasu marasa daɗi, sai dai lokaci ya wuce ba tare da ɗaci da raɗaɗin abun da ya faru da ummi ya bar zukatan iyayenta ba.Kuma babu kunya, wanda yayi laifin ya cigaba da sabgoginsa hankali a kwance.
Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta ɗaukkota, ta daina barin kowa ya raɓi ummi.
Mariya na zaune na ƙoƙarin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris.
Ummi taƙi mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana ɓata fuska.
"Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?"
"Mama ni bana son makarantar" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta.
Cikin damuwa haɗi da kulawa ta ce "Saboda me ummina"
Cike da ƙuriciya ummi ta ce "Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ƙibata"
Mariya ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?" Ummi ta jinjina kai ta ce "Eh, Ina son tarihi"
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...