*CUTARWA!*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
BRIGHT PENS
(FREE BATCH)P9
Gaba ɗaya Ummi ta ji ƙafafuwan ta sun yi mata sanyi, har suna neman gaza ɗaukarta, tayi ta maza ta ja jikinta ta shiga, kai tsaye ɗakin da take ta wuce, ba ta tsaya a in da Iya ke banbaminta ba.
Wucewar ta bai sanya Iya jan baki tayi shiru ba, sai ma haƙiƙancewa da tayi, tana cigaba da masifa "Ni dai na gaji da wannan maitar da masifar, dole in miƙe in nemi tsari da bala'i da tashin hankalin wannan mutanen su daina yi mini sintiri da bibiyata, ba dole mariya ta haukace ba, hakkin ɗa na ba zai taɓa barinta ba, daga haka ma in Allah ya yarda sai ta fara yawo tsirara, ni bai dame ni ba, hakkina da na ɗa na ba zai bar ta ji daɗin rayuwa ba, hauka ma yanzu ta fara ba ta ga komai ba tukuna".
Ummi ta ja ta tsaya a cikin ɗakin, tana ƙare masa kallo, kasancewar haddar yaro ƙarami, ba abu ne da yake gogewa cikin sauƙi ba, ya sanya take ummi ta shiga hasaso abubuwa da dama da suka faru a ɗakin nan.
Yanayin jeren ɗakin, ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke da mamanta ke yawan kunnawa, yadda take zama a kan cinyar mahaifinta ta ci abinci, yadda daren da aka yi mata fyaɗe ya kasance, ko ba komai ummi ke iya tunawa ba, ba ta manta yadda mamanta take iya ƙoƙarin ta wurin yi wa Iya biyayya, ta kalli yadda ɗakin ya zame mata a yanzu baƙi ƙirin, tamkar dajin da wuta ta cinye bishiyun da suke ƙawata shi.
Durƙusawa tayi ta fashe da kuka tana sheshsheƙar kuka, tana jin Iya na cigaba da ci wa mahaifiyarta mutunci, tare da yi mata fatan masifa kala-kala da aibantata da sharruka.
Ummi ba ta samu fitowa daga ɗakin nan ba, sai daf da la'asar, dan ma Allah ya taimake ta zuwa makarantar allo da take yi, ana horasu a kan kula da ibada, wanda dama ta samu wannan horon daga mahaifiyarta, amma dan ta Iya, ko za ta shekara ba ta yi salla ba, babu ruwanta da ita.
Ta yo alwala ta dawo ɗakin tayi azahar da la'sar, ko tunanin zuwa makarantar allon ba ta yi.
Tana jiyo yadda duk wanda ya shigo sai Iya ta gaya masa ai Mariya ta haukace, tana can an sakata a turu, hakkin rai yana bibiyar ta, ta fara bi bola-bola tana tsince-tsince.
Ummi ta sha kuka, sai da idanunta suka kumbura, dan duk kukan da za ta yi idonta baya ja, sai dai ya ɗan sirka, kuma su kumbura.
Ta kalli kuɗin da yaya ɗanlami ya bata, ta watsar da su a tsakar ɗakin, ta ƙanƙame jikinta, tana sauke numfashi hawaye na tsiyaya daga idonta.
Ba tsammani ta ga magaji a kanta.
"Ummi" ya kira sunanta a hankali.
Ta ɗaga kai tana kallonsa. "Kukan me ki ke yi?"
"Yaya magaji"
"Na'am ummi".
"Wai mamana ta haukace?" Tayi maganar wasu hawayen na gangarowa saman kumatunta.
"Subhanallah waye ya gaya miki haka?"
"Wanda ya tafi da ita ne yazo, shi ya bani wannan kuɗin"
Hashim ya ce "Kar ki sake cewa ta haukace, bata da lafiya dai, tana ganin likitan ƙwaƙwalwa aka ce"
"Likitan ƙwaƙwalwa? An ce sai mutum ya haukace fa ake kai shi wurin likitan ƙwaƙwalwa"
"Ba haka bane ba"
"To meyasa Iya take cewa mama ce ta kashe baba, ba hatsari yayi ba?".
"Ki daina damuwa da maganar Iya, ki kwantar da hankalinki, ki ta yi wa mamanki addu'a Allah ya bata lafiya"
![](https://img.wattpad.com/cover/359344510-288-k508497.jpg)
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...