CUTARWA!
AYSHERCOOL
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
48
Cikin tsananin takaici, Abdul yake kallon Idris da yake ta rarraba ido, kamar an kwashe wa karya ƴaƴa.
"Amma ga alert ɗin da banki suka yi maka, na kuɗin, kuma sannan ga wanda suka yo maka kana ta cirar kuɗi, ga sunana da komai da sunan bankina".
Nan ƴan ɗakin suka hau salati da salallami, iya ta ɗago idanunta da suka yi ja, saboda azabar ciwo da wahala, ta kalli Idris kawai ta sunkuyar da kai.
Wata ƙanwar iya ta fara masifa ta ce "Amma Idris an yi mutumin banza, kana kallon yadda matar nan take kwana tana wayyo ciwo, an rasa kuɗin yi mata abun da yakamata, saboda kai azzalumi ne ka cinye kuɗi ka ce ba a turo maka ba, yanzu duk soyayyar da iya take nuna maka wannan ne sakamakon abun da zaka yi mata?"
Yaya magaji ne yayi sallama, suka amsa masa, ya kalli yadda suka yi jugun-jugun ga dai iya a zaune, balle ya ce mutuwa ta yi suka jimami.
Suka gaisa da kowa, suka gaisa da ummi cikin girmamawa, sai dai bai ko kalli in da Idris yake ba, dan tuni ya daina yi masa magana ba ya shiga harkarsa.
"Wai lafiya na ga kowa ya yi shiru?"
Kawu Ilyasu ya ce "Ɗan uwanka ne ya cinye kuɗin da aka turo masa ayi wa Iya magani, yayi magana ma ya ƙi yayi shiru"
Hashim ya ɗan kwaɓe baki ko a jikinsa, dan gaba ɗaya yana danasanin kasancewarsa a tsatson iya. Da ƙyar matarsa take tursasa shi ya zo dubata.
Ya ce "To Allah ya kyauta, ai da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, balle a tsine masa na hannun daman ta ne"
Kawu sagir ha haɗe fuska ya ce "Wane irin iskanci ne wannan? Uwarmu na kwance ba lafiya kuna faɗar abun da ku ka ga dama"
Ummi ta ce "A'a kawu, Allah ne ya kawo wa iya lokacin shan dauɗar gora, dan duk wanda zai sha barinta ne, ita da take yawan faɗa, kuma da sauƙi tun da shi ya ci ba wani ba, sai ta fi jin daɗin shanyewa"
Abdul ya kalli ummi yana girgiza mata kai, amma tayi burus da shi, dan lokaci yayi da yakamata ta amayar da damuwarta, ayi mata fyaɗe amma iya ta ce a rufa dauɗar gora ciki ka sha ta. Duk wani abu in dai a kan Idris ne ko son zuciyarta, sai ta ce dauɗar gora ciki ka sha ta. Ita ma gashi Allah ya kawo nata lokacin.
Kowa ya din ga tofa albarkacin bakinsa a kan Idris, yayi shiru ya kasa magana.
Wata maƙwabciyar su idris, mai suna ɗahara ta zo duba iya, sai dai matar kamar ba ta da saiti, kamar wadda ta taɓa hauka, saboda yadda take magana take sakinta yadda ta ga dama.
Cikin tsantsar ƙauyanci da rashin iya magana ta ce "Kai Innalillahi wa... me ye ma ƙarashen na manta, Iya haka ki ka koma? Wannan naɗai da aka yi miki a ka, kamar shugabar bokayen gagarawa? Rayuwa kenan, ai baban Nana, gidanka da na higa kan na taho, na ce wa Shindatu ta zo ta rakoni na duba gyatumar nan Iya, amma ta ce mini wallahi ba za ta zo duba tsohuwar banza da ba ƙaunarta take yi ba.
Nana ta ce Allah ya sa daga Asibitin nan ba za a maidota gida ba, na ce ke Shindu ki ji tsoron Allah, da gyatumar ki ce a ba kya ce haka ba". Ta yi maganar tana dariya, kamar abun da ta faɗa ɗin ba wani abu bane a wurinta.Ta sake cewa "To dai jin abun da suka faɗa, ya sa jikina yin sanyi na taho, to Allah dai ya bata lafiya, ni dai idan ta warke to, idan ba ta warke ba dai dan Allah ina bin ta jaka ɗaya da muttala biyu kuɗin surfe na, gara a fara sauke mata nauyi tun tana raye".
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...