CHAPTER 12

544 29 1
                                    

*CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P12

Kamar mai shirin tarayya da dabba, haka yayi kan ummi, ya fara yage suturar jikinta, yana ja tana ja, tana ihu tana bashi haƙuri.

"Ba zaki rufe mini baki ba?" Yayi maganar cikin fusata.

Warin bakinsa ya daki hancin ummi, kai ka ce an buɗe masai.

Sai dai ba ta gama shaƙe warin bakinsa ba, warin gashin kanta ya daki hancinsa, gashi ne fal Allah ya bata shi, sai dai kasancewar babu gyara babu tsafta, ya sanya yake wani irin tsami mara daɗin shaƙa.

Sai da ya ware gashin ya sauka bayanta, warin ya ƙaru har wani gafi gashi gashin yake yi, saboda tururin warin dauɗa da ƙazanta.

Ƙyale gashin yayi, ya cigaba da ƙoƙarin rabata da suturar jikinta, sai dai nan ma jikin ummi, warin dauɗa yake yi, da tsamin gumi, saboda rashin wanka da kula.

Har ɗauke numfashin sa yake yi, ita kanta ummin warin hammatar idiris ɗin ya hanata sukuni, yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amma ba ta gaza ba wurin ƙoƙarin kare kanta.

Duk da a duhu ne bai hana shi, kifa wa ummi mari ba da dukkan ƙarfinsa, Allah ya sa hannunta ya samu ba fuskar ba, amma sai da ta gigice.

Marin da yayi mata ya sanya ta saka kataɓus, har ya cimma in da yake burin zuwa, sai dai wari da ƙarni mai haɗe da zarni ya bugi hancinsa sai da yayi baya, take ya ji cikinsa ya yamutsa masa, kamar zai yi amai, nan da nan zuciyarsa ta fara tashi.

Duk yadda ya so ɗauke numfashin sa ya kasa, wani irin baƙin ciki da takaici ya ninku a zuciyarsa, ya laluba ya ɗaukko fitilarsa ya hasketa, ta kare jikinta sai kuka take yi.

Ya tashi ya rufeta da duka, abun da ta fi tsana, ya din ga takata da ƙafarsa, sannan ya janyota ya hankaɗata waje ana wannan ruwan saman, ba tare da imani ko tausayi ba. Kuka take iya ƙarfinta, tana danna ƙofar ɗakin, amma ya saka sakata ta ciki.

Tsakar gidan ya shaƙe da ruwa, saboda rashin magudanan ruwa a unguwar.

Jikinta duk ya yage mata sutura, kuma a haka tsirara ya hankaɗota waje cikin ruwan sama.

Ga wani irin tsoro take ji, balle ta tafi ɗaya ɗakin, haka ruwa ya din ga dukanta tana kuka. Tun tana saka ran ruwan zai ɗauke, har ta zubawa sarautar Allah ido, ƙafafuwanta suka gaji saboda tsayuwa, ruwan saman nan ya ƙarasa zuba a kanta.
Ta din ga buga ƙofar ɗakin a hankali ta na cewa "Dan Allah yaya idiris ka buɗe mini na ɗauki kayana, sanyi nake ji dan Allah" tayi bugun har ta gaji, jikinta ya din ga wata irin karkarwa saboda sanyi.
Ruwan, bai gama ɗaukewa ba, ta fara takawa a hankali ta na ƙanƙame jikinta saboda ƙyanƙyamin ruwan da ya kwaso dagwalon unguwar ya shigo ya taru a gidan.

Ɗaya ɗakin ta nufa, sai dai kasancewar ba taga babu ƙofa, a buɗe yake, shima ta tarar ya malale da ruwa, babu in da za ta zauna, ta samu wuri ɗaya ta raɓe tana cigaba da kuka.

Har garin Allah ya waye ummi na tsaye, babu wurin da zata raɓa ta zauna, saboda an yi ruwa ba ɗan kaɗan ba.
Gari ya fara haske tana sanya ran ya buɗe ƙofa ta suturta jikinta, amma bai buɗe ba, ta din ga fargabar kar a zo gidan a tarar da ita jikinta babu sutura.

Sai da gari yayi haske tar, sannan ya zare sakata ya fito ya shiga banɗaki, tana hangen sa ta taga, ganin ya shiga banɗaki, ya sanya ta fita ta shiga ɗakin, ta kwashi kayanta da duk ya yayyaga, ta saka, jikinta sai wata irin tsuma yake yi, saboda sanyi, ga ciwo da jikinta yake yi mata da ƙafafuwan ta.

A gurguje ta yi alwala, ta koma ɗakin yin sallar asuba, duk a ɗarare take cikin tsoro take yin ta.

Aikuwa a raka'a ta biyu ya dawo ɗakin, bai damu da salla take yi ba, ya hankaɗeta, saboda wata irin tsanarta da yake ji a cikin zuciyarsa.

CUTARWA!Where stories live. Discover now