*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
42
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
AYSHERCOOL
08081012143MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
42
Cikin sanyin jiki ummi ta ce "Dan Allah anty ko zuwa da safe ne, sai na tafi in sha Allah"
"Wallahi ba ki isa ba, ba zan sake zama inuwa ɗaya da ke ba, ai ni ba zan manta cin kashin da dr. Ya din ga yi mini saboda ke ba, a samu ki auru da ƙyar sannan ki dawo mini, bana maimaita kuskure, haka Allah ya yi ki da baƙin jini, kamar mai hatimin jaɓa duk in da ki ka je sai an tsaneki an kore ki"
Ummi ta yi shiru ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ina zata tafi ga duhun magariba.
Kausar ta nufo ummi gadan-gadan da niyyar ta hankaɗata ta koreta, ummi ta ja da baya ta kalli kausar ta ce "Kar ki kuskura, akwai banbanci tsakanin da da kuma yanzu, ko da aurena ya mutu da yardar Allah na fi ƙarfin komawa baya, ba sai kin hankaɗa ni ba, zan tafi". Duka suka kalli ummi, yaushe bakinta ya buɗe har haka da take mayar da martani.
Ta juya ta fita, ta ɗan yi nisa kaɗan sai ga noor, sanye da uniform ɗin islamiyya.
"Yaya ummi, da tafiya zaki yi ban dawo ba, to Allah ya kama ki" tayi maganar tana murmushi.
Sai kuma ta yi saroro tana kallon ummi, ganin ummi a saɓule."Ya na ganki a haka? Ina yaya raihan ɗin?".
"Ya sakeni noor" ummi ta samu kanta tana gaya wa noor.
Ta dafe ƙirji ta ce "An shiga uku, saki? Me ki ka yi masa? Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ashe da gaske maama take idan Abba yayi mata laifi ta ce namiji ba ɗan goyo bane ba, ashe da gaske ne me ki ka yi masa?"
Ummi ta dafa kafaɗarta ta ce "Kul ki ka sake faɗar haka, mata mukan yaudari kanmu da ɗorawa maza kaso mafi yawa na zaluntarmu, alhalin a zahiri mu ne azzaluman kanmu, mu yi ta ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, amma a zahiri kowace mace ciwonta na ta ne ita kaɗai, noor maza ƴan goyo ne, kuma iyaye ne, ɓata garin cikin su ba zai sanya ayi musu kuɗin goro ba. Mami ce ta saka ya sake ni, ba laifin sa bane ba, ni duka da na san baƙin cikin ɗa namiji a rayuwata, amma maza sun tallafi rayuwata fiye da yadda mata suka yi".
Tuni noor ta fara kuka ta ce "To ina zaki je? Ba dai gagarawa ba ko? wannan garin da ba sa sonki, me zaki je ki yi musu, ki zo mu tafi gida kawai"
Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a ai ni in da ba a so na da yawa noor, ki yi maza ki tafi, magariba ta yi"
"To ina zaki je?"
"Ke dai kar ki damu, zan dawo maza ki ƙarasa gida".
Noor ta tafi gida da gudu, sai dai ta tarar farida suna sake tattauna abun da ya faru, a nan ta ji korar ummi suka yi, suka ce ba zata zauna a gidan ba.
Duk da ƙarancin shekaru na noor, sai da ta jinjina mugunta irin ta mahaifiyarsu.
"Maama yanzu idan wani abu ya sami yaya ummi a hanya fa, dare ya fara yi ki ka ce ta tafi gida? Idan Abba ya ji fa?"
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...