*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
40
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
AYSHERCOOL
08081012143MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
41
Galala mami ta buɗe baki tana kallon raihan, ba ta taɓa zaton wannan kalaman daga bakinsa ba ko a mafarki, ta rasa wace amsar ma yakamata ta bashi, ganin ba ta da abun cewa ya sanya jiki a sanyaye ya fice, zuciyarsa na wani irin zafi.
Har ya nufi motarsa ya ji an riƙe hannunsa, ya waiwaya ya ga Salim.
Ya gyara nutsuwarsa cikin girmamawa ya ce "Yaya ina wuni?"
"Meyafaru ne?"
Raihan ya kalleshi ya ce "A ina?"
"Dambe ka yi ne? Ba ka ga yadda ka ke gumi ba, idonka ma yayi ja?"
Ya girgiza kai ya ce "Bakomai, dama mun dawo ne na zo gida mu gaisa ban zaci ma kana nan ba"
Salim ya kama hannun raihan ya wuce da shi ɗakinsa, Sagir na kwance a falo yana kallon tv suka shigo, sallamar su kawai ya amsa ya cigaba da abun da yake yi.
Ya zaunar da raihan a kan kujera, shima ya mayar da hankali a kan kallon ba tare da ya cewa raihan ɗin komai ba.
Sun shafe a ƙalla mintuna talatin a haka, sannan Salim ya numfasa ya kalli raihan ya ce "Are you ok now?"
Ya jinjina masa kai ya ce "Yes, na gode sosai"
Salim ya sake tattara nutsuwar sa a kan raihan ya ce "Me yake faruwa? Kar ka ɓoye mini" raihan ya yi shiru yana yi wa Salim kallon mamaki, dan sam ba mai shiga abun da bai shafe shi ba ne ba.
Kamar ya san me raihan yake tunani a kai ya ce "Na san zaka yi mamakin tambayarka da nake yi, na samu labarin matsin lambar da ake yi maka a kan ƙara aure a wurin Hajiya, kuma daga dawowarka ba zai yiwu ace har wani abun ɓacin rai ya faru da za ka shiga cikin tashin hankali ba, in dai ba a kan maganar ba ne ba.
Ka san meyasa na titsuyeka nake tambayar ka?"Raihan ya girgiza masa kai alamar a'a.
"Alƙawarin da muka ɗaukko wa mahaifiyarta da ni da kai, Allah ya sani ina tausayin baiwar Allah nan sosai, kuma kai ka bani labarin irin wahalar da take sha a rayuwa, idan har ka rabu da ita, ka yi wa mahaifiyarka biyayya haka ake son ɗa na gari amma ka sa a ranka ko da ranka ko bayan ranka sai wani ya auri ƴar ka ya saketa!.
Haka zalika idan ka auri wannan yarinyar ka zalunci ummi, ko ita wadda zaka aura ɗin, shi ma ka shirya kare kanka a gaban Allah"Gaba ɗaya raihan ya sake rikicewa ya ce "Wallahi yaya na rasa yadda zan yi, ina son ummi muna zaune lafiya tana kyautata mini, me zai saka na saketa ko ace sai na yi wani auren? Ni ba na son safiyya a matsayin matar aure, kuma bana son saɓa wa mami"
Salim ya kaɗa ƙafa ya ce "Am sorry to say, iyayenmu mata wasu lokutan na da gajeren tunani, iyayenmu da suke aure fa, ba daga sama suka faɗo ba, su ma ƴaƴan wasu ne. Anyway Allah ya kyauta, na kira ka ne dama dan na yi maka tuni a kan amanar da ka ɗaukko, kayi ƙoƙarin gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka, ba tare da wani ya cutu ba".
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...