CUTARWA!
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
(BRIGHT PENS)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
50
Jikin farida na tsuma, ta karɓi takardar ta duba, ga saki nan rangaɗa-rangaɗa guda biyu.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai meyasa duk maza halinsu ɗaya ne? Butulci kawai suka sani? Ita ma uwar ta sa shegiya mummuna mai baƙin hali. Ɗaukko mini wayata maza na kira babanku, na shiga uku ni farida wannan masifa hawa-hawa" ta kira wayar dr. Amma bai ɗaga ba.
Ta dungurar da wayar ta ce "Ai na sani, ba zai ɗaga ba yana tare da wannan mahaukaciyar, na shiga uku ni farida".
Dr. Kuwa sallama yayi ya dawo daga salla, mariya ta shirya masa abinci, ya lumshe ido ya ce "ƙamshin abincin kawai ya sa na ji na ƙoshi" tayi murmushi ta ce "Ka dai fara ci tukuna"
Ta zuba masa faten wake doya, yana ci ya ce "Yauwwa, noor ta dawo ta zo ki fara koya mata irin abincin nan, kar tayi aure ba ta iya girki ba"
"Waye ya ce maka ba ta iya girki ba? Idan ta zo gidan nan tana yi ai, noor ɗina ta iya girki sosai ta ce a wurin ummi ta koya"
Dr. Ya ce "Ai tun da ummi tayi aure, na yi kewar abinci mai daɗi"
"Son kai, saboda ƴar ka ce ko?" Yayi dariya yana kashe mata ido ɗaya.
"Yauwwa ga wayarka, an kira ban ɗaga ba"
Ba tare da ya karɓa ba ya ce "Ki na tsoron kar ki ɗaga ki ji budurwa ta ce ko?"
Tayi dariya ta ce "Haba dai, ko ma budurwar ce na san ba za ta wuce maman ummi ba, maybe ko tana buƙatar wani abun ne, idan ka gama kar ka manta ka kira ta" ya ɗan ƙura mata ido. Ita har cikin zuciyarta tsakani da Allah take son su zauna lafiya da farida, wai ko ba komai ta riƙe mata ummi, daga baya ta haƙura ganin faridan ba haka ne abun a wurinta.
Ya gama cin abincin, ta kawar da kwanukan, ta zauna tana matsa masa ƙafa ya lumshe idonsa.
Ta ce "Baban ummi, ba ka ce mini komai ba a kan zuwa maiduguri"
"A'a" ya faɗa a taƙaice.
Ta sunkuyar da kai ta cigaba da abun da take yi masa.
Ya ɗago haɓarta ya ce "Kin yi fushi ne?"
"A'a, amma in anjima ma zan kuma tambayar ka, dan Allah baban ummi, ka san menene?"
Ya ce "A'a sai kin faɗa"
"Taron family aka shirya mana, wai an binciko tun farkon asalinmu, an gayyato mutane da dama da muke da alaƙa, ba tare da mun san mu ƴan uwa ba ne, dan Allah baban ummi"
Ya ɗan yi murmushi ya ce "Na ji, amma ni kin ga bani da lokacin kai ki, bana son kuma ki hau motar haya, kin ga kina da juna biyu kar ki wahala"
"Ai zan gaya wa ummi, idan ya barta sai mu tafi da Abdul da noor, dan Allah kar ka ce a'a" yanayin yadda ta kwantar da kai take lallaɓa shi ya sanya shi jin daɗi a ransa tare da jin kansa eh shi ne maigida. Saɓanin yadda farida ke yi masa magana gatse-gatse, wani lokacin ma sai ta yi abun da take so yake sani.
"Shikenan, Allah ya kaimu lokacin, za ki je in sha Allah"
Faɗaɗa murmushinta ta yi tana yi masa godiya.
Sai magariba ya je gidan farida, dan duba su.
Sai dai ta fara da yi masa ƙorafi, da zazzaga masa masifa, sannan ta miƙa masa takardar da inteesar ta zo da ita.
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...