*CUTARWA*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
35
MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe.
FOLLOW AND SHARE
AYSHERCOOL
08081012143MASU BUƘATA DAGA FARKO WANDA BA SA WATPAD, KU YI FOLLOWING CHANNEL ƊINA, ZAKU SAMU DAGA FARKO IN SHA ALLAH.
Follow the COOL HAUSA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
Follow this link, to join my what's app channel, domin samun sabbi da tsofaffin litattafaina, tare da tattaunawa a kan abubuwan da suka shafi rayuwa na yau da gobe
35
Galala kausar ta buɗe baki tana kallon raihan.
"Ko ba ki ji me na ce ba ne?" Yayi maganar yana kallon kausar.
Ta kalli ummi, ta ce "eh lallai, zaki shigo zaki haɗu da maama"
Raihan ya ce "Idan ta shigo kar ku bar ta da rai" kausar ta juya fuuu ta tafi.
A rikice ummi ta ce "Raihan, meyasa zaka yi haka? Ka san me zaka jan yo mini ne?"
Ya ƙare mata kallo ya ce "Idan kin koma gidan, ki tsaya ki zuba musu ido su illata ki, ummi ba fa kowanne lokaci ne haƙuri yake maka amfani ba, meyasa da ba a ce sai kin yi girkin ba sai da na zo? Dole ki rage wannan shirun naki, kuma ki shirya tsaf, domin akwai ƙalubale a zaman da zamu yi, zaki fuskanci challenge daban-daban dole ki din ga ƙoƙartawa, a yanzu dai duk abu ba zaki daku ba, dan haka kar ki bari wani abu ya baki tsoro, idan ma dukkan ne ki rama, ki daina zama ana cin kashi a kanki, tun da kin kusa bar musu gidan"
Ummi ta yi shiru tana nazarin matsalar da raihan ya jefa ta a ciki.
Ya basar ya ce "Baki bani labarin Maiduguri ba, ya ki ka ga garin, ya kuma ki ka ji da ki ga mama?"
Duk da a tashin hankali take, sai da ta yi murmushi, ta ɗan saki jiki, ta bashi labarin yadda ta ga garin, da abubuwan da suka faru.Har ta fara mantawa da matsalar da raihan ya jefata a ciki.
Da zai tafi ya zura hannu a aljihunsa, ya ajiye mata kuɗi, ya ce "Na san ba zaki rasa buƙatunki ba, sannan ranar monday zamu je banki a buɗe miki account, zan saka miki kuɗin kayan lefenki a ciki"
Ta kalli tudun kuɗin da ɗan yawa, ta ce "Ka bar kuɗin nan mana, hidima ce a gabanka sosai"
Ya girgiza kai ya ce "Kar ki damu, ai ba wani kyautar kuɗi nake yi miki ba, kina buƙatar kuɗi kuma na san ba tambayata za ki yi ba, abu na gaba kuma shi ne, saura ki shiga cikin gidan nan, su yi miki magana ki zauna kina kuka, ina da cid na kin sani, idan ki ka bari noor ta ce mini kin zauna kin yi kuka, ni da ke ne, ki kula mini da kan ki amaryata" Ummi ta yi zuru da ido tana tunanin irin tashin hankalin da zata iya fuskanta.
Kausar kuwa jiki na tsuma ta je ta sanar wa farida abun da raihan ya ce, babu kunya a gaban ƴaƴanta ta kuza ashar ta miƙe tsaye jikinta yana tsuma.
"Wai wani ɗan iska ne ma wanda za ta aura ɗin? Wani matsiyacine ne, bari in je in ga ɗan gidan uban waye na ci mutuncin sa daga shi har ita".
Kausar ta tare ta ta ce "Wallahi wani ɗan yaro ne, dan dai yana da jiki ne, amma wallahi ba ki ganshi ba"
"A'a bari na ƙarasa na je na ga wani shegen ne, ita ma ba ta isa ba balle shi"
YOU ARE READING
CUTARWA!
RomanceKowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi...