CHAPTER 5

545 24 2
                                    

       *CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724
Arewabooks ayshercool7724
YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
What's app 08081012143

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

*BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_

Tsari👯🏻‍♀️
Duk page ɗaya 200
Duka littafin kuma 600
Shafi biyar a littafi ɗaya 1000
A littafai uku kuma 3000
Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻‍♀️🫶🫶🏼

P5

Har suka je tasha, jan ƙafa kawai mariya take yi, dan bata gane komai, hankalinta yana kan ummi, wace irin rayuwa ummi za ta yi a wannan gidan? Tana nan ma a ya aka cika, balle yanzu da babu idonta, kuma ya zamana ba ayi rabuwar arziki ba.

"Allah ka kula mini da ƴa ta, Allah kar ka sanya ƴa ta ta lalace, Ubangiji Allah ka duba mini ita, ka tsare mini ita, Allah kai ka san dalilin da ya sanya, ka karɓi mahaifinta ka rabani da ita, Allah ka kula mini da ita. Haka ta din ga wannan addu'ar, jin abubuwan take tamkar a cikin nannauyan bacci, da take fatan ta farka.

Har suka shiga mota suka kama hanya, duk wata nasiha da maryam ke yi mata, ba ji take ba, balle ta fahimta.

Mariya ji take tamkar ta sauka daga cikin motar nan, ta koma ta rayu da ummi, ta san ummi wahala kawai za ta sha, dan iya ba ƙaunarta take yi ba.
Tunawa da tayi da cin zarafin da aka yi wa ummi, ya sake karya mata gwiwa, ta sake fashewa da kuka mai sauti.

"Idan ba zaki rufe mana baki ba, a tsaya ki sauka ki koma, ki je duk uban da za su yi miki, su yi miki, sai ka ce a kanki aka fara haihuwa, duk cin zarafin da suka yi miki bai isheki ba, ba dai ƴa ba ce su je su cinye ta, ai ta su ce da ma, dangin uba su ke da ɗa" tun da ya fara yi mata masifar ƴan cikin motar suka yi tsit, sai da ya gama ake bashi haƙuri.

Maryam ta san abun da mariya ke ji, dan haka ta rungume ta tana rarrashinta, haka tana ji tana gani ta bar garin da duka goma da ashirin, ga rashin miji ga rashin ƴa.

Ummi kuwa sai can daf da magariba aka saka yara suka rakata gida, dan can gidan wata ƴar uwarta ta sanya aka kai ta.

Ta ci kuka ta ƙoshi, sai ajiyar zuciya take yi, ana zuwa gidan da sauri ta shiga ta nufi ƙofar ɗakinsu, sai dai ta tarar da shi da ƙaton kwaɗon da su mariya suka rufe ɗakin da shi.

Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar ɗakin, ta cigaba da rera kuka.

Babu wanda ya saurareta, balle ya kula da ita ya rarrasheta.

Sa'adatu ce tayi sallama, ta kawo wa iya tuwon dare.

Ta ajiye mata suka taɓa hira, ta tashi fito, tana daf da shiga sashinta, ta ji ana bin ta a baya, ta tsaya ta waiwayo taga ummi.

"Ke, lafiya ki ke bina?"

"Dan Allah ina mama? Haryanzu ba ta dawo ba, ta buɗe mana ɗaki in yi salla, sanyi nake ji"

Sa'adatu ta yi shiru tana kallon ummi, sam ba ta ga dalilin da zai sanya iya raba mariya da ƴar ta ba, ta san iya ba iya riƙe ta zata yi ba, saboda tsabar mugunta da rashin imani.

"Ummi babarki ba zata dawo ba, ki tafi wurin iya ki je ki kwanta, gari da sanyi"

"Ita ma maman ta mutu? Ba zata dawo ba kamar baba?"

"Ba mutuwa tayi ba, nan kusa dai ba zata dawo ba, ki yi addu'a Allah ya sanya ta dawo ta tafi da ke, can in da aka kai ki kin ci abinci?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "Mama ta hana ni cin abinci a gidan mutane"

CUTARWA!Where stories live. Discover now