JIDDO
(Gidan aurena)
By
MAMAN NABEELA
DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION
Page 44
Yana fitowa ya nufi lafiyayiyar Motarsa Marsandis Benz fara sul, Gads ɗinsa dake zaman dakon fitowarsa a ko yaushe ne suka buɗe masa cike da girmamawa.
Hannu ya ɗaga haɗe da cewa“Marwan key”
Cike da girmamawa wanda ya kira da Marwan ya miƙa masa key ɗin sanin in dai ya buƙaci haka baya buƙatar fita da kowa, fatan dawo wa lafiya suka yi masa har Motar ta bar harabar wajen ta nufi Get.
Kira ya tura ta wayar sa da ya jona da spiker Motar.
“Barka da yammaci M.D” muryar Tahir ta fito ta cikin spiker Motar.
“Barkanka dai T. Ina hanyar gidan ka fa” ya yi maganar yana ci gaba da tuƙinsa.
Dariyar Tahir da sautin muryasa ne suka fito lokaci ɗaya “ehyyyee! Yaushe ka dawo? Kace kana hanyar zuwa tsinkar fure” Tahir ya ƙarashe maganar cikin zolaya.
“Hmm! Ɗazu yahh kana gida ne?” A.Rashid ya yi maganar muryarsa da alamun murmushi.
“A'a bana gida, amma zuwa nan da One hour in'sha'Allahu zan ƙaraso”
“Ok sai ka ƙaraso” A.Rashid ya yi maganar yana ƙoƙarin katse kiran
“Asha love lafiya Oga na Jidda”
Muryar Tahir ta kuma fitowa ta jikin spiker Motar, murmushi ya kuma saki yana katse kiran.
Tahir yana ji ya yanke wayar ya fara neman Maimuna tana ɗagawa yake tambayar ta tasan M.D Rashid yana hanyar zuwa gidan gurin Jidda, tace bata sani ba bata tunanin ma Jidda ta sani don gata a tare da ita.
Umarni ya bata da a shirya masa ɗan abun taɓɓawa mara wahala sannan ya yanke wayar.
Jidda da tunda taji an ambace ta ta dakata da danna wayar da take tana sauraren Anty Maimuna tana gani ta gama wayar ta fara tambayar ta me ya faro?
“M.D ya faɗa miki yana hanyar zuwa gidan nan?”
“A'a Anty ai rabonmu da yin waya dashi tun safe kuma ai yana Abuja” na bata amsa cikin mamaki.
“To dai yana hanyar zuwa gidan nan dan yanzu abinda Abban su Ihsan yake faɗa min kenan, ta yiyu so yake yayi miki zuwan bazata” Anty Maimuna ta ƙare maganar cikin murmushi.
“Wanne bazata kuma Anty? Idan kuma aka yi rashin sa'a bana nan fa!”
