*JIDDO*
( _Gidan aurena_ )
By
*MAMAN NABEELA*
*DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION*
*Page:45*
______Yayin da kwanakin biki ke ƙara matsowa, shirye-shirye ta kowanne ɓangare ake. Sosai Jidda ta ƙara cika fatarta ta goge sakamakon gyaran da ta fara karɓa, duka-duka sati biyu ya rage bikin inda Jidda ke ta shirin komawa Kano a yau. Tsaye ta ke ita da Anty Maimuna da itama tare zasu Kanon.
Ƙarfe 10:am muka ɗauki hanya don ni dama tun jiya da A.Rashed yazo muka yi sallama kuma a jiyan ya bani envelop wanda nake kyauta zaton kuɗi ne a ciki, ban buɗe naga ko menene ba har sai da na koma ciki.
Anty Maimuna na miƙawa ita ta farke envelop ɗin kuɗi sababi ƙal ne a ciki ƴan dubu-dubu rafa uku. Shawara muka yanke kan sai munje Kano sannan za'a san abin yi da su don ɓangare gyaran jiki dama Anty Maimuna ta ce ita zata biya.
Ko da muka isa Kano sosai gidan mu naga ya sauya don har flaster da painty aka sake, abinda na kula shiri Baba Yaya Ahmad harma da Annar mu suke sosai a kan wannan auren.
"Anty JIDDO kinga yadda kika sauya kuwa! Yasiiin babu me cewa kin haifi Ƴa kamar Asma'u, bari ma kiga na kirata na sheda mata kin dawo don bata da labarin ko auren da zaki yi" Azima tayi maganar cikin dariya kafin ta fara neman lambar Asma'u cikin wayarta.
Dariya kawai nayi kafin na ce "da gaske Autar mu!".
"Yasin Anty kinji ma wayar ta shiga, hello Asmey" Azima tayi maganar.
Daga chan ɓangaren Asma'u da ke tare da Salma da Zainab suna kallo ta ɗaga ta ce "hello Mama Azii na kin wuni lafiya!"
"Lafiya lau al ishirin ki!"
"Goru fari ƙal Mama Azii tawa me saƙon alkairi amaryar ya Ustaz" Asma'u ta amsa ta cikin dariya.
Cikin ɓata fuska Azima ta ce "au haka zaki ce! To Allah ya kiyaye kuma na fasa ma yi miki albishir ɗin"
"Wayyo Allah Mama Azii na kiyi haƙuri ta Musty bada kanki a sare kije gida ki ce kin kyautar" tayi maganar cike da kuɗa zaɓin Azima wanda dama tsukana ce tasa ta yi mata maganar Ustaz don bata so sa ko kaɗan.
"To ko ke fa da kina neman ɓata min rai" Azima ta yi maganar da dariya.
"To menene albishir ɗin? Na fa ƙagu na ji" Asma'u ta yi maganar cike da zaƙuwa.
"Ammeyn ku ta dawo yanzu ita da Maman Ihsan"
"Dan Allah fa!" Asma'u tayi maganar cikin tsan-tsan farin ciki.
"Wallahi" Azima ta bata amsa.
"Yasin kuwa yanzu zan taho dama ai na kwana biyu banzo ba"
"To shikenan sai kin zo, ki gaida Salma" Azima tayi maganar jin kamfanin layin sun fara yi mata worning.
"To zata ji, ki ce ina yiwa Momy da Ammey sannu da zuwa kan na ƙaraso" Asma'u tayi maganar tana cire wayar a kunne ba tare da ta ƙara jiran me Azima zata ce ba.
Cike da zumuɗi ta ce "Yaya Salma Mama Azima na gaishe ki kuma Ammey ta dawo daga Kaduna yau"
Cike da farin ciki suka nufi ɗakin Lubabatu don su faɗa mata zasu gidan. A bakin ƙofar ɗakin ta suka yi kaciɓus, wanda ihun da Zainab take na murna da kuma haya niyar su yasa ta tasu don ganin abinda ke faruwa.
"Umma Ammeyn mu ta dawo yau zamuje mu ganta" Asma'u tayi maganar cike da farin ciki.
Lubabatu dake tsaye cikin wata doguwar rigar less sai uwar rama da tayi tace "to amma ku tabbatar kun dawo da wuri kunga Babanku ya yi tafiya bamu san yaushe zai dawo ba ko wanne lokaci zamu iya ganin sa ya dawo"
