JIDDO
(Gidan aurena)
By
MAMAN NABEELA
DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION
PAGE 43
A washe garin suna bamu muka gama aikin soye-soyen Naman suna ba sai kusan ƙarfe uku na yamma dole tasa su Amma fasa tafiya saboda yamma ta yi sosai suka bari sai washe gari sannan su tafi, nikam dai Anty Maimuna ta dage kan sai fa tayi ar'ba'in sannan zan koma Kano tana ta faman lalaɓa Anna kan ta saka baki Babanmu ya barni daga ƙarshe dai da taga baza su amince ba sai Tahir ta samu da maganar ta ke ya goya mata baya ya kira Baba ya roƙi ya barni na zauna har ta yi arba'in.
Da yake Baba na matuƙar jin nauyinsa ta ke ya amince,washe gari kuwa da wuri su Amma suka ɗauki hanyar Kano bayan Anty Maimuna da Tahir sun cikasu da abin arziƙi.
Bayan kwana biyu sosai soyayyarmu da A.Rashed ta ƙara ƙulluwa tamakar wata buduruwa haka yake rawar ƙafa a kaina tare da ɗokin son ya mallakeni,sosai soyayyar da ya ke nuna min take bani mamaki da sake tsunduma ni cikin kogin son shi. Gama wayarmu kenan dashi na nufi kitchen gurin Anty Maimuna na tarar har ta sauke Girkin da na keyi tana zubawa a cikin wermas, wanke-wanke na nufi sink ɗin na fara ina dariyar jin waƙar da ta ke.
“Soyayya daɗi tafi zuma zaƙi Jidda ta ta samu Miji na gari ina ta taya ta murna nai sama-sama na kwaso......”
Dariyar da na kuma kwashewa da ita ta hana ta ƙarasa waƙar itama ta kama dariya.
“Allah Jidda ina faɗa miki kin gama dace don a wannan karo ina me tabbatar miki zaki san kinyi aure da izinini Allah”
“Allah yasa Anty amma ni har yanzu wani ɓarin na zuciya ta fal yake da fargaba”
“Wace fargaba kuma Jidda? Kinga ki kwantar da hankalinki ki ci-gaba da Addu'a in sha'Allahu babu abinda zai faro a wannan gidan auren naki sai ababen alkairi, don wallahi ina faɗa miki MD a iya sanin da nayi masa bashi da wani hali na Allah wadai” Anty Maimuna ta yi maganar tana dafa kafaɗa ta.
“To Anty Allah yasa” na yi maganar ina ci-gaba da wanke kwanuka.
ENAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL EIRPOT
Cike da murmushi wanda ya daɗa baiyana asalin kyawunsa haɗe da taku irin na ingarman Namiji ya nufi jirgin da zai shiga don komawa Kaduna yana sane yaƙi faɗawa Jidda zai dawo ba don komai ba sai don yana so ya yi mata surprise yana so haɗuwarsa da Jidda ta zamu ta musamman kamar yadda yake jinta ta musamman a zuciyar sa, Mamey kaɗai ya sanarwa yau zai dawo. Cikin mintuna ƙalilan jirginsu ya sauka a Kaduna international eirpot Or Redy Gards ɗinsa da suka iso tun tuni ne suka firfito daga falla-fallan Motocin da suka zo ɗaukarsa masu ɗauke da tambarin MAI NASARAH ɓaro_ɓaro jikin lambar Motocin ƙamewa suka yi lokacin da ya fara saukowa daga cikin jirgin cike da girmamawa suka rufa masa baya bayan gama saukowarsa har ya shiga cikin Mota.
Direct unguwar koran ganye jerin gwanun Motocin suka nufa, wani katafaren tsalelan estate suka kutsa kai wanda tun daga nesa kake hango wasu ƙartin sojoji daga bakin gate ɗin estate ɗin, tun kan su ƙara so Sojojin suka wangale makeken gate ɗin cike da girmamawa.
Bisa ga al'adarsa ta tsayawa ya gaisa da ma'aikata tasa suna zuwa gate ɗin farko Drivern ya sauke glass tare da rage gudun Motar.
Gaisuwa tarin Sojojin suka fara miƙo masa yana amsa su kafin Motocin suka wuce, gate na biyu ma haka ce ta faru haka gate na uku ma kafin Motocin suka nufi ƙatun compound ɗin da ke gaban sashen Mahaifiyarsa suka faka.
Cikin sauri Gards ɗinsa suka fito suka buɗe masa Motar haɗe da ƙamewa, ƙafafunsa dake sanye cikin haɗaɗen rufafen takalmi ya zuro waje kafin gangar jikinsa ta fito gaba ɗaya.
Ƙofar falon Mamey ya nufa haɗe da danna wasu lambubi take ƙofar ta buɗe ya kutsa kansa ciki bakin sa ɗauke da sallama.
Jannat da Ammar da suke cikin falon da gudu suka tahu suka rungume shi.
