44

101 8 1
                                    

Basu suka bar gun ba seda la'asar, sashen sarauniya babba ya raka ta, inda suka iske Sulaiman da Bilkisu, Bayan Yarima sun gaisa da Sarauniya Babba, suka wuce masallaci shi da Sulaiman din, suma su Hafsan sallan su suka yi, aka kawo musu abubuwan taɓa baki suna ci suna hira a tsakanin su, a lokacin suka fahimci juna ita da Bilkisu, ashe tana da saukin kai da kirki, ita ta dauka duk yaran sarki masu girman kai ne, itama Bilkisun a lokacin ta fahimci wacece Hafsa, nan kuwa suka ɗinke gashi ma cikin ta yayi nauyi, zata ce ma Yarima ya dinga barin Hafsa tana zuwa sashen ta suna debewa juna kewa.
Suna a haka Shamsu ya shigo ya jona su, Hafsa da shamsu suka hade kai sai tsokanan Bilkisu suke da katon cikin ta, ita kuwa kamar zata yi kuka, sarauniya babba ce ke karɓan mata.
Karan budewar kofa suka ji, tare suka juya gaba dayan su, suka ga ashe Hayatu ne, nan kuwa Hafsa ta haɗe rai dan bata manta da kashedin Me girma Yarima ba, shiko kamar ya samu tv ya dinga kallon ta har Bilkisu ma mamakin kalan kallon da yake ma hafsan take, shamsu ne da ya lura da hakan ya ɗan buga sa ya masa ido, duk akan idon sarauniya. Can sega su Yarima sun shigo, shamsu ne suka gaida su, Yarima kam ko amsawa beyi ba se Sulaiman, yana ganin Hayatu kuwa a gun yace ma Hafsa ta tashi su tafi, sarauniya babba ce ta hana ba'a san ransa ya zauna ba, da mangariba ma hada kai suka yi suka fita salla, da suka dawo aka kawo musu abinci da abubuwan taba baki, basu ne suka koma sashen su ba sai bayan Isha.
____________

Kilishi bata zame ko ina ba daga lambu sai dakin ta, Seda ta tabbatar da ta tura ƙyauren dakin nata da kyau kana ta ɓace kogon boka Kapoor, tana bacowa gunsa ya daka mata tsawan da Seda ta girgiza, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, tayi salati
Ita da ta kawo masa kara kuma ya mata tsawa? Ita da ta kawo korafi? Toh me ya faru, Allah dai yasa lapiya, in dai ba lapiya ba ta shiga ukun ta, domin yaune rana na farko da ta taɓa bata masa rai, yau kam baza ta iya bacci ba sam
Muryar sa wacce take echoing uku uku ne tayi magana kamar haka
"Wannan shine karo na karshe da zan sake tuna Miki da kar ki sake ki sake yi mana salati anan, Kina ina da rashin kulan naki ta ɗauki ciki?", girgiza zuciyar Kilishi tayi
'Ciki kuma? Kai inaa wannan ƙarya kenan, ita ta tabbata bayin da ta saka su aikin sama Hafsan ido baza su taɓa mata ƙarya ba, gaskiya da sake'
Maryar sa me matuqar ban tsoro ta ƙara tsinta yana me cewa
"Gashi a dalilin rashin kulawar ki ta ɗauki ciki sannan baze yiwu a zubda ba, in aka zubda abun ze shafe ki, kawai yanzu za'a jira Gopal ya kawo maganin a aika mata kawai daman yanzu watan shi uku da tafiya, ki ɓace min da gani"
Ya karashe cikin rikitacciyar ƙara.
Ɓaco wa dakin nata tayi ran ta a matuƙar haɗe, bari zata san yanda zata yi ta zubar da cikin kawai.

Bayan anyi haka da wata guda, Kilishi ta baiwa amintacciyar baiwar ta wani magani tace a tabbatar an zuba a abincin Hafsa sannan a tabbatar da Hafsan ta ci shi idan ba haka ba hmmmm, boka ne kaɗai yasan me zata iya aikatawa.
Karɓan maganin baiwar tata tayi hannun ta na matuqar ƙyarma

________________

Zaune Hafsa suke ita da Gimbiya Bilkisu a dakin shakatawar Yarima, daman kusan kullum ita ke zuwa sashen Gimbiyar duba da yadda tayi nauyi, shine yau ta aika mata akan baza ta samu daman zuwa ba, shine ita Gimbiyar tazo ta, suna cikin hirarrakin su aka kawo musu abincin rana, da aka buɗe kwanon farkon wata funkasau ce abun birgewa, ai kuwa se ya shiga ran Hafsa a take, gashi funkason ɗan kaɗan ne, kapın tace a zuba mata, Gimbiya Bilkisu tace a zuba mata ita, Hafsa ne tacewa Gimbiya "Dan Allah Gimbiya ki bar min inci Ni, wlh ya biya raina sosai da sosai, har ina jin in banci ba za'a samu matsala", itama Gimbiyar cewa tayi se taci yaron cikin ta yana sha'awar funkasau, ana haka se Hafsa tace toh suci tare mana, Gimbiya tace ita ɗaya zata ci
Gimbiya ce tace
"Haba matar yaya ki dubeni da tsohon ciki baza kiji tausayi na ki bar min in cinye ba"?
"Wallahi Gimbiya ya shiga raina ne, ji nake in banci ba akwai matsala".
Hafsa ta bata amsa tare da marairaice wa
Jin haka se Gimbiya Bilkisu tace mata "Toh ki cinye din, amma baza kici naman zabuwan nan ba"
Ta karashe da haɗe rai, dan bilhaqqi ya shiga ranta sannan duba da yadda Hafsa ta nace zata ci ne yasa tabar mata, dan bata taɓa mata tana san abu sosai har haka ba sai yau.
Can bayan sunci abinci suna ɗan hutawa lokacin har marece yayi suna kan hira Hafsa ta fara muqurqusu, kafin kace meye Hafsa ta fara ihu tana kuka, kan susan me yake faruwa suka ga jini ya ɓalle mata, lokacin bayi ne kuyangu ne gaba ɗaya an taru ana jira meke faruwa, da ikon Allah ba wanda yayi gigin taɓa ta, Gimbiya Bilkisu se ihu take ma bayi akan su dauki Hafsa amma an rasa me taɓa ta, su tsoron Yarima suke, saboda watannin baya da bayi suka taɓa jikin ta ya basu azaba me tsananin gaske, hadda larai me magani da take mace kuwa, shiyasa dukkanin su suka kasa taɓuka komai.

Suna zaune a fada an kira su shida Sulaiman akan Mai Martaba zai aike su ƙasar chadi, wani bafade ya shigo ya fadi yayi gaisuwa
"Tuba nake ranku ya dade, Gimbiya Hafsa ne a kwance rai a hannun Allah"
Yarima be san sanda ya miqe zeyi waje ba, riqo sa Sulaiman, kana ya neman musu izini daga fada suka wuce sashen Yariman
Yana shiga ganin halin da take ciki besan sanda ya ciccibe ta yayi hanyar dakin maganin masarautar ba, bayi kuwa sai ƙus ƙus ake tayi sede ba me iya magana a fili.
Da sauri Zuwai me magani tazo ta fara bata taimakon gaggawa tare da koran su Yarima da su Gimbiya waje, jiƙa wani sassaqen ta tayi ta bata tasha  a take jinin ya tsaya, fara bincika ta tayi, a ƙalla takai kusan awa tana abu daya, su ko su Yarima da su sulaiman sunyi jugum a waje
Can sega ta ta fito, gaishe da sarauniya tayi dan bata ma san sanda ta zo ba, kallon su Bilkisu tayi kamin tace
"Cikin jikin Gimbiya ne ya kusa zubewa amma da yardar Allah be ƙarasa zubewa ba, za'a barta anan har ta samu lapiya domin kwata kwata juna biyun nata na mako huɗu ne"
Kowa Seda ya cika da mamaki da jin wannan bayani, bayama sarauniya babba da ta kasa gane Hafsa nada ciki bayan ko shekaran jiya Seda suka wuni a sashen ta ita da Bilkisu
Bilkisu da mijinta Sulaiman kamar sun fi kowa murna dajin wannan batu, suna shirin su taya Yarima murna suka neme shi suka rasa, ashe shi har ya shige dakin, yana kokarin ɗaga ta, ma'aikaciyar jinyar ta hana shi, tace masa yanzu ba'a so tana motsa wa, zuwa nan da nan domin cikin ze iya ɓarewa, daɗi kamar ya kashe Yarima wai shine ze zama uba, ita kuma Hafsa da taji labarin cikin da take ɗauke dashi, jikin ta mugun sanyi yayi, nan da nan hawaye ya fara zuba mata, wai yau ita ce Hafsa yar Malam Sule Mai Rini take ɗauke da cikin Yarima, ikon Allah, wa yaga Mama Hafsa amma fa ɗan zega hauka wlh 😂
Fadin irin farin cikin da masarautar ta dauka ɓata lokaci ne, Fulani da me martaba daɗi kamar ya kashe su, on the other hand Kilishi kuma zamu iya cewa saɓanin hakan take a wajen ta.

Seda Hafsa tayi wata guda cur kapın aka sallame ta tare da saka tsattsauran tsaro akan cimar ta da ma komai nata, bayan kwana biyu tace wa Yarima tana so taje gida, da farko ya hana ta dan yana gudun a taɓa lafiyar ta ita da cikin se daga baya ya kyale ta ta tafi, tare da saka kwakkwaran tsaro akan ta domin wasu wani slight chance suke nema dan su taɓa ƙimar sa.

Hallo Y'all's
What do you think about this novel? Vote and drop a comment please, sannan ayi sharing ma
Fadrees che.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now