16

91 9 4
                                    


TARİHİ
Sarki Alhaji Sulaimanu bn İdrissa, shine sarki na Ashirin da uku a garin Bauchi a wancan zamanin. Su goma sha daya mahaifin su Sarki İdrissa ya haife su amma a kap dinsu su biyu suka rage domin duk sauran yaran da ya haife su komawa suke. Sarki İdrissa Yayi bakin cikin rasa ya'yan sa da yake yi, mutane aka dinga cewa ko ya saba ma Allah ne, yasa yake jarraban sa da rashin yayansa.
A lokacin matansa uku da kwarkwarori biyu, amma dukkan su babu wanda bata haihu ɗan ya koma ba, imma mace imma namiji.

Auren sa da Aminatoú yar Sarkin Agadéz ne Allah ya basa dansa na farko da ya rayu wato Sulaiman wanda ake ta jita jitan cewa a kap garin Bauchi a zamanin sa ba'a taba haifan ɗa kyakkyawa kamar sa ba, kasancewar mahaifiyar sa kyakkyawar gaske ce ko a Niger din ma, kasancewar su buzaye da sirkin fulanin asali
Haifan Sulaiman da Aminatoú tayi ya jawo mata bakin jini haikam a gurin abokan zaman ta da ma wasu daga cikin manyan masarautar.
Domin kuwa yaro kwarjini da kyau da hankali gare shi. Ga haiba da cikar zati, duk shi kadai, shekarar sa biyu ta haifo Jafar wanda shima ba baya bane wajen kyau da kwarjinin.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya inda shekaran Yarima Sulaiman ya cika Ashirin cif cif, a lokacin ne kuma emmata suke ta rububin samun sa, ciki kuwa harda yar Wazirin wancan lokacin me suna Sadiya.
Aminatoú wacce take amsa sunan Sarauniya Babba a yanzu ne ta sama ma Sulaiman Hauwaó karamar yar yayanta, wacce baza ta wuce shekaru goma sha uku ba, Sulaiman yayi na'am da wannan hadin take suka fahimci juna aka sa musu rana, soyayya suke a tsaftace, Sadiya kuwa hakan da akayi ya bakanta ranta domin har ta samu Jafar a boye ta gaya masa manufarta, toh sanin halin mugunta irin na Sadiya da rashin kamun kai yasa Jafar yaqi taimakon ta kamar yadda ta bukata, instead se yaje ya fada wa yayan nasa, har shi kuma ya mata rashin mutunci, daga karshe da magana takai kunnen me martaba, se yace ya baiwa Jafar auren ta, dan itama baza ta wuce sa'ar Hauwaón ba, koma ta baiwa Hauwaón shekara daya.
Da jin haka Jafar yace shi besan zance ba baze aure ta ba, akayi akayi yaqi yadda, lokacin shekaran yayansa daya da aure, da Sarki İdrissa yaga haka se ya fusata ya aura wa Sulaiman ita, ita kuma ta dauki tsanar duniya ta ɗorawa ahalin, shi kansa Sulaiman din bata kyale sa ba.

Yin auren ta da Sulaiman da wata daya akayi auren Jafar da Zulaiha yar galadiman wancan lokacin, bayan auren su da wata biyu ciwon ajali ya kama Mai Martaba Sarki İdrissa, sati be juyo ba seda yace ga garinku
Nan da nan aka naɗa Sulaiman, kwana biyu tsakani Hauwaó wacce ake kira da Fulani ta aihu ƴa mace aka saka mata sunan Sarauniya Babba, bayan shekara biyu aka haifi Yarima aka maida masa sunan Mai Martaba Sarki İdrissa, a lokacin watan Sadiya biyu da haifan tata ƴar me suna Asiya, sannan Jafar ma matar sa bayan wata biyar ta haifa masa yaro namiji, ya sawa yayan sa takwara.

Shekara biyu da haifan Yarima, Sadiya wacce take Kilishi a yanzu ta haifi yaranta ýan tagwaye, Shamsu da Hayatu, se bayan shakara biyar Fulani Hauwaó ta haifi Bilkisu, wanda yayi daidai da lokacin da matar Jafar ta haifi tata ýar me suna sameera.

Yara sun girma har sun kai munzalin Shekara ashirin da hudu zuwa da biyar, wato Yarima da Sulaiman kenan, domin Aminatoú an dade da mata aure tana masarautar Agadéz, se kuma Asiya da take birnin Sokoto da aure.
Wannan kenan.

_________________

Hafsa kam ko Sallah kasa tashi tayi, sai da Murja taxo ta dinga tallafa mata, abinci ma se an mata ɗure, ta sha wahala matuƙa, Seda ta kwana biyu tana jinya kapın ta samu sauki, a lokacin babu irin jita jitan da ba'a yaɗa ba akan ita da su Yarima, ɗadin abun ma ba'a iya yi a gaban ta, domin kuwa da za'a kwashi yan kallo ne, shima Yarima wannan na daya daga cikin dalilan da yasa be neme ta ba
Yau ta kama Laraba da wurwuri Hafsa ta shirya tayi hanyan sashen Yarima.
Sallama tayi, ta tura kofa ba kowa, nan ta kimtsa ko ina taje madafa ta kimtsa shi shima, alamu taga kamar babu kowa a cikin uwar dakan Yarima, nan ta yanke hukuncin ta shiga ta gyara masa, kutsa kai tayi wani Ni'imtaccen kamshi ya shiga kofofin hancin ta, nan ta shiga ta gyare ko ina tsafff, ta wanke makewayin sauran gyaran gado, gani tayi gadon ya birge ta, yau de kam se ta gwada kwanciya a kai taji yaya yake ji da yake wani huhhura wa mutane hanci, sannan daga gani katifar zata yi laushi, ga nan barguna nan masu matukar taushi da laushi a shimfide.
Wohoho yau zata dandana kapın ya dawo itama.

Sashen dardumar sa ta hango nan cikin ta ya bada kulululu, nan kuwa taje ta fara bude ko wane kwano daya bayan daya, still nan ma taga duk abinda ta bude sunfi karfin ta, kwanon karshe ne taga soyayyen dafaffen dankali da kwai, ga wata jar miyar da bata taba ganin irin sa ba, duk da an fara ci ba wani dayawa aka ci ba, nan ta afka hannu ta fara gabza, hannu bisa hannu ƙwarya. Seda ta cinye tass kapın ta samu salama nan ta kora da wani ruwa me daddaɗan zaƙi se kamshi yake, wanda ko ƙaffara baza tayi ba da inibi aka yi shi, nan take tayi kan gadon ta kwanta na sai barawon yazo ya sace ta ba? Su Hajiya Hafsatu hadda minshari an wangale baki, ƙafafuwa na kallon kudu da arewa, zani kuwa yana kallon gabas, dankwali kuwa daman tun a gurin dardumar abinci aka ya da shi.
Wannan kenan.

______________________

Yarima na hango ya fito daga sashen Sarauniya Babba, daga yanayin fuskar sa zaka gane ba maganar arziki suka yi da ita ba
Jikin sa har rawa yake tsabar ɓacin rai, sashen sa ya wuce, yana tafe yana saƙe saƙen abinda Hajiya Babba tace, da ya karaso kai tsaye ya shige dakin sa, yana zuwa bakin gado yaci karo da malama hansai ana sharbar bacci, harda ɗan jan dogon tsakin ta, tana zagin Jamila wai ta rena ta. Se sumbatu take tana faɗin
"Wallahi Mama Jamilan nan na lura tana da raini sosai, toh wlh zan koya mata hankali, har Ni zan aike ta taƙi zuwa, da badan ina da hakuri da hankali da hangen nesa tare da kai zuciya nesa ba, ai da kakkarya ta xanyi" shine fa ta karashe zancen tare da jan dogon tsaki.

Kawai kasa motsi shikam yayi, ya ma rasa me yake masa dadi, kawai ya tsaya yana kallon ikon Allah, lalle yarinyar nan ba kyal bace, yanzu fisabilillah wai itace take da hakuri da kai zuciya nesa? Shi da badan hakurin sa ba ai da ya kakkarya ta tun tuni, yanzu akwai ma rainin da ya wuce har ta tsallake dakin shakatawar shi ta shigo har cikin uwar dakan shi ta hau kan gadon shi ta kwanta tayi bacci? Tsabar asara hadda minshari? Ehhh lalle kam dole tace an rena ta, tsaya wa ma yayi yana tunanin wane irin hukunci ze mata tukunna, beyi aune ba ya ɗan gauce kadan, be zame ko ina ba se kan Hafsa da take bacci salamun ƙaulan.

Mu haɗe a shafi na gaba
Kar a manta ayi voting, sharing da commenting.

Fadrees 🖋️ 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now