27

138 7 0
                                    

"Ni Malam Sule Mai Rini na bada ƴata ma Yarima İdriss, halak malak, idan an yadda da hakan, na amince yanzu yanzu aje a daura musu aure".

Hakika sarki da waziri da ma duka manyan fada babu wanda bai girgiza da jin wannan batu na Malam Sule Mai Rini ba, mamakin karfin halin sa suke, Sarki ne ya zuba masa ido ko kyaftawa ba yayi
Can dai Galadima ya dubi Malam Sule Mai Rini, yace "Na so in wayi fuskar ka, amma na rasa a ina ne, sannan game da abinda kace, hakan ba mai yiwuwa bane,  akwai yar kanwata da take hannuna, duk da bata wuce shekara sha daya ba, sai a daura musu auren kawai".
Su garkuwa dai basu da ta cewa, tunda baza su bada ƴaƴansu ba ai basu ga bakin magana ba
Waziri ne yace "a'a baza ayi haka ba Galadima, tunda yace zai bada yarsa ai mai san mu ne, sannan kar yaga kamar be kai bane ba'a so a aurawa Yarima ƴarsa"
Daga nan ya dubi Mai unguwa yace, "Malam Kallamu me zaka ce game da hakan"
Mai unguwa ne ya buɗi baki yace "wannan mutumin makwafcina ne ,sannan da yayi aiki a cikin Masarautar nan, daga baya kuma aka sallame sa akan wani laifi da bashi ne ya aikata ba, yarsa kuma Hafsan da yake so ya baiwa Yariman itama tayi aiki a cikin wannan masarautar sannan Yariman da kanshi ya kawo ta, a lokacin har muka zo da shi da yayansa akan a bata sallama, sai galadima yace mu dawo bayan wata uku, in Allah ya yarda zeyi magana da Yariman a sallame ta daga bisani kuma en matsalolin da suka auku a cikin Masarautar nan tsakanin dan Sarkin Gobir da Yarima Hayatu yasa aka bata sallama. Toh bayan haka ashe shi Yariman yaje ya mata kyautar gida wai na hidiman da ta masa, shine mahaifinta gashi nan yanzu saukan sa daga zuwa sana'ar da yake yi garuruwa, da yaji labarin gidan da kuma abinda yake faruwa da matan da Yariman zai aura ne, ya sadaukar ma wa Yariman ita, shi yace koda Yarima yana da mata hudu, ze iya bashi ita a matsayin kwarkwara.
Sannan gidan da Yariman ya ba Hafsan ma har yanzu shi yaqi karba". Mai unguwa ya karashe yana mai fatan su amshi bukatar su na farantama Yariman, dan shi kanshi dakyar ya yadda Malam Sule Mai Rini ya bada yarsa.

Da jin haka sai Mai Martaba da kansa yayi magana kamar haka "Hakika kai ka cika mutumin asali, muna godiya da wannan karamcin naka, Kuma in Allah ya yadda baza kayi kuka da hakan ba, sannan kyautar gida an baku shi halal, bai kamata ka mayar da hannun kyauta baya ba, yanzu ita yarinyar ta san da batun auren ne"?
Malam Sule Mai Rini ne ya karba da "A'a Allah ya baka nasara, amma Hafsa yarinya ce mai biyayya, nasan baza tayi jayayya da Ni ba".
Da jin haka kuwa Sarki ya miqe nan da nan kowa ya miqe aka koma masallaci
Ana zuwa sarki ya harde, nan da nan Aka daura auren Yarima İdriss Sulaimanu bn İdrissa, tare da amaryar sa Hafsatu Sule, da kuma Sulaiman Jafar bn Idrissa tare da amaryar sa Gimbiya Bilkisu Sulaimanu bn Idrissa.
Kamar a mafarki Yarima yaji daurin auren da aka masa, kuma ma wai da Hafsa, shidai bai san farin ciki Yakamata yayi ba ko farin ciki, hakika yana san ya dinga ganin ta a kusa dashi, saidai yana mata tsoron mutuwan nan, amma kuma tunda har an riga an dauran, kila matar sa ce ta har illah Masha Allah.
Maroƙa da makiɗa kuwa kamar jira suke yi, nan da nan suka fara aikin su, masarauta gaba daya ta hautsine, har ma da cikin gari.
Sulaiman ne ya daga Yarima suka yi waje.

Hoton Yarima idriss a yayin da ake daura masa aure da Hansai

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Hoton Yarima idriss a yayin da ake daura masa aure da Hansai.

Ai sai yanzu ma na kare masa kallo dan Fadin irin kyan da yayi ma bata lokaci ne, yasha ja da farar alkyabba, ga Amawali da wando mai zina ga rawanin sa shima fari sai kyalli yake. Shi kansa Sulaiman yayi mugun kyau, da ka ganshi kaga sabon ango
Maroƙa suka dinga musu kirari, su kuma sai dadi suke ji, burikan su na aure rana daya ya tabbata, sai zagba murmushi suke, musamman Yarima, duk daure fuskan sa idan ka ganshi yau zaka san cewar yana cikin farin ciki.
Su Hayatu da Shamsu sai kyautar kudi suke ta badawa, ba tare da sanin Hayatu cewa Hafsan da yake muradı bane

Kwanakin baya ya aika aka nemo masa gidan su, ashe Kilishi ta gane, ta kira sa ta masa barazanar zata tsine masa, daga nan ne bai sake bi takan Hafsan ba, amma be janye kudirin shi ba, yayi alƙawarin zai shawo kan Kilishi har tazo da kanta ta bashi goyon baya.

________
Bilkisu ne cikin dakin Sarauniya Babba sai kukan shagwaba take ta ma Fulani da Samira da Sarauniya Babbar, wai ita ta fasa auren bata so, suna a haka suka iski mummunan labarin mutuwar yar Malam, Fulani da jin haka ta fashe da kuka Bilkisu tana taya ta, saida Samira da Sarauniya Babba suka dinga rarrashin ta, suna a cikin haka baiwar Sarauniya Babba, Shafa'atu ta doko sallama tare da neman izinin shiga, tana shiga ta sanar musu da an daura auren Yarima da wata wai Hafsa, nan da nan farin ciki ya game fuskokin su, sallamar ta sarauniya babba tayi, tace ta dawo anjima, ita kuma ta koma sashen bayi, ba tare da sanin cewa Yariman Hafsa ya aura ba.
Wannan kenan.

________
Kilishi ce ranta a matukar ɓace, har ma tana jin zata iya kisa in aka matso kusa da ita, yanzu bai jima ba, baiwar ta tazo ta sanar mata da albishir din da har seda tayi kyautan azurfa, yanzu kuma azo a same ta da banzan magana, ranta a hade ta ɓace kogon shugaba, dariya mai cike da razanar wa ya saka da muryoyi daban daban kan yace "Za'a daidai ta komai kinsan babu abinda ya gagari shugaba kap duniyan nan, za'a daidai ta koma tashi ki tafi" ya karashe da wani murya mai ban tsoro.
Ɓaco wa dakin ta tayi cikin rashin walwala amma sai ta kanne, tabar abun a ranta

_________

A gidan malam sule mai rini kuwa ko da ya koma yamma har tayi, ba abinda ya fara yi, sai ya tara dukkan iyalansa yace suxo suyi magana, da suka zo sai ce musu yayi zasu kaura daga gidan nan zuwa sabon gidan jikin gidan su gobe da safe in Sha Allah, sannan dama gidan gida ne mai matukar kyau dan na siminti ne ma ba ƙasa ba, bai fada musu asalin zancen ba sbd sam basu da math, sai kawai yace musu idan sun yarda su koma toh, duk wanda bata yadda ba toh sai tayi zaman ta a tsohon gida, nan da nan su Kulu da Lantana yan kwadayi suka ce zasu koma ita Zainabu dai bata ce komai ba, guri suka samu ya fara mata magana kamar haka
"Bana san kimin kallon kamar mai son abin duniya, gidan nan gidan Hafsa ƴarki ne, baki ga daga dawowa na ko gida ban shigo ba sai yanzu? Tun daga bakin kofa Lawan yace inzo muje gidan mai unguwa, koda naje, (nan ya bata labarin yadda Yarima ya baiwa Hafsa gida sannan ya dora da) Ni kuma sai ban karba ba, mai unguwa yayi yayi in karba sai naqi, da yaga naqi karba shine yaban labarin mutuwan da matan da Yarima zai aura suke, Ni kuma da naji haka sai na dauki alwashin zan basa Hafsa da muka je sai Mai Martaba yace lalle lalle in karba yanzu in takaice miki zance An daura auren Yariman da Hafsa dazu dazun nan, ihu suka ji a bayan su, suna juyawa suka ga Hafsa da Dije a bakin kofar dakin malam sule mai rinin, Ashe Hafsa ne ta saki kara tare da zubewa akan gwiwowin ta ita kuma Azima ta saki ihun tayi cikin gidan nasu da gudu, Hafsa dai gata nan a tsugunne kamar mutum mutumi dan kafarta kasa daukar ta suka yi, Mama Zainabu ma suman wucin gadi tayi, dukkan su wannan batu ba ƙaramin girgiza su yayi ba. Wai yanzu Hafsan ce take da aure akan ta? Kuma na Yariman gaba-daya Bauchi? Yariman ma mai jiran gado?. Unbelievable!.
Ba wannan ba ma, ita Hafsa injiniya ne yace tazo ta masa iso da babanta, tazo shiga gida ta hango Ibrahim din masarautar Borno a kofar gidan nasu, shine fa ta shigo dan ta fada wa Malam Sule Mai Rini, Azima kuma ashe tana biye da ita, sai kuma taji labarin ƙaddarar rayuwar ta.

Fadrees 🖋️

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now