14

80 7 2
                                    

Abu ake yi tun safe har yamma, amma ana daukan break domin yin Sallah cin abinci da kuma shan ruwa. Fara wasan keda wuya. Can na hango Yarima, se yanzu zeyi participating, sauran wasannin da akayi su Sulaiman ne da su shamsu suka yi contesting.

Hafsa na hango a ɓangaren da aka ware ma bayi suna tsaye ita da Murja ata gaba gaba, domin Hafsa make mutane ta dinga yi Seda ta ganta a gaba kapın hankalin ta ya kwanta, bayan an hura usur nan aka fara gudu da dawakai, wani ɗan Sarkin Katsina da ya zo se ya bige Yarima har ya so ya fadi daga kan dokin shi Allah ya taimake shi, nan ya tsaya yana maida numfashi kan ya ankara har anyi gaba an barshi, nan ya dago kan sa se a fuskan Hafsa, hannu yaga suna ta daga masa suna ta masa kirari, nan take yaji wani kwarin gwiwa a take ya fara gudu da dokin sa seda yaje ya wuce kowa sauran ɗan Sarkin Katsinan da ya kusa lashe gasan, kaman kiftawa da bismillah ya rupe idon sa yaga Hafsa tana ta daga masa hannu tana sakin murmushi me kayatarwa, ai be san sanda yaje ya wuce ɗan Sarkin ba, ya lashe gasan.
Nan aka saka wani uban ihu da shewa, wasu na rawa wasu na guɗa,

Yan garin Bauchi na ta murnar Yariman su ya lashe gasa, ko wane Sarki sai da yaba Yarima kyautan doki, sannan darajar masarautar Bauchi ta sake daguwa. Can dab da maghriba kowa ya koma masaukin sa, Hafsa na hango ita da Murja se zuba sauri suke zasu koma sashen su na bayi, zasu je su shirya dan yau akwai karatu, shan gaban su Ibrahim yayi
"Gimbiya Hafsa sarautar mata" suka tsinkayi muryar sa a cikin dodon kunnen su, Hafsa ne ta juya gabas da yamma kudu da arewa taga babu me lura da su kapın tace
"Ka rupa min asiri kar ka sa a kulle Ni a dakin duhu" Hafsa ta fada tana me zare ido
Dariya ta basa dan seda ya ɗan dara, can kuma ya nitsa tare da fadin
"Tabbas Hafsa kina matukar kama da wata wanda na sani, sede na rasa a inane, amma idan na koma masarautar mu zan sake bincikawa sa'annan in dawo masarautar nan in haɗa ku, amma kapın nan ina so ki bani adreshin ki domin gobe zamu yi haramar tafiya masarautar mu ta Borno, idan ya so in na samu sarari zan zo in neme ki"

Jikin Hafsa ne yayi sanyi, domin be pi sau hudu bane suke clashing da shi, yanzu abinda ya fada kuma se taji wani iri. Gaya masa Sunan unguwar su Wunti tayi, tare da basa cikakken adreshin ta, tace masa idan yaje ya tambaye gidan Malam Sule me Rini za'a kai sa har kofar gidan su, nan suka yi sallama jikin Hafsa duk a sanyaye ita kuma Murja mamaki tayi tunda suke da ita tayi tayi ta gaya mata adreshin gidan su taqi, amma ita kam kusan kullum se ta gaya mata adreshin gidan su da wahalan da ake bata, kawai dai Hafsan tasha alwashin duk ranan da tabar masarautar nan zata je ta koya wa matar baban nata hankali ne, amma bayan haka basa ma maganan, se yau da taji tana gayawa Ibrahim, ta ma san unguwan nasu akwai wani kawun ta a can, duk ranar da aka sallame su zata je mata ziyara In Allah ya yadda.

Bayan sunyi mangariba suka je suka karbo abincin su, da suka ci sai suka doshi hanyar tafiya makarantar su na bayi.
Yau dai Yarima be neme ta ba, haka ta ringa leqa wajen ajinsu ko za'a aiko ace yana neman ta amma shiru
Har tayi kaman taje ta se kuma ta fasa
A haka da aka tashe su suka koma dakin su duk se tayi wani iri, tana zuwa tayi kwanciyan ta akan katifar ta, nan ta fara tunanin su Mama da ya zame mata jiki kullum

Tuna wani lokaci tayi da ake saka su girki ita da su Azima da Dije wai kar a musu aure suje basu iya girki ba.
Daman haka suke raba abun su, idan wannan yayi tuwo to wani miya zeyi, to ranan yin tuwon Hafsa ne, sannan daman ba wani iyawa tayi ba, shigowar ta kenan ta dawo daga yawon damben ta, tana saka kafar ta su Mama Lantana suka hau ta da masifa, wai tayi mangariba yaushe zata daura tuwo, ga Sadiqu se kuka yake, juyawa tayi ta ga Sadiqun har gwaliyo yake mata, ranta se yayi mugun ɓaci a ranta tace zaku ga tuwo, ranan tuwon ruwa ta musu, Hafsa tsabar mugunta hada saka daddawa a ciki, ranan tsabar bacin rai bakin su Mama kulu kaman ya cire, Mama kuwa Seda ta mata ɗan banzan duka, seda Yaya Lawan ya cece ta, ranan abincin siyarwar su Mama Lantana aka ci, duk da Hafsa tana ci tana mita, wai taga yawu a cikin kunu, tuna hakan da tayi seda tayi dariya har cikin ta yaso ya ƙulle, bata san sanda barawon yazo ya sace ta ba, se jin kiran Assalatu tayi.

Yau ta kama sauran wata daya da sati biyu Hafsa tabar masarauta idan tayi hankali kenan, duk da bata ma san da hakan ba

Da sassafe bakin Mai Martaba suka fara watsewa musamman wanda suke da nisa kamar su Masarautun Sakkwato da su Gobir, sauran ƙalilan wanda suma suke haramar tafiya gobe
As usual sukayi wanka suka yi breakfast suka kama hanyan zuwa aiki. A bakin sashen nasa taga wannan amintaccen bawan nasa mugun nan, tsaki Hafsa ta watsa masa tare da jefa masa mugun harara, tayi shigewarta ciki, shiko Bawa me suna Tanimu ransa yayi mugun ɓaci, ya so ya mangare ta ya kyale kar ya kawa kansa matsala, amma akwai ranan ƙin dillanci, ranar da Yarima ze sa shi ya zane ta, wlh se ya canza mata kamanni.

Ko da Hafsa ta shiga shara ta fara, kana tayi goge goge, ta jera komai yanda ya kamata saura dakin, jim kadan taji karar fitowar sa, yayi kyau cikin shigar sa na alkyabba kalar dorawa, zubewa kasa tayi ta kwashi gaisuwa, shi kuma se ya tsaya yana kallon ta har ta dago kapın ya amsa, taro zeje da za'a yi a fada, da babu abinda ze hana shi cewa ta biyo sa, ficewa yayi yabar Hafsa cikin kidima, Yarima ne ya amsa gaisuwar ta? Kai gaskiya yau zata zuba ruwa a kasa ta sha.

Dakin sa ta shiga ta gyara, da ta gama komai kamar bayan azahar haka ta fito da shirin komawa, a hanya ta ringa jin bayi na ƙus ƙus, wasu cewa suke an bada auren yar sarki da yar waziri a yaran sarakunan da suka zo, wasu kuma cewa suke an baiwa Yarima mata, nan take zuciyar Hafsa ta kusa bugawa jin abinda aka ce, ita dai tafiya take bata ganin gaban ta se kawai taga wani bawa wanda uniform nashi ba kalar na masarautar tasu ba, yasha gaban ta, daga kai tayi da niyar ta duddura masa ashar na rashin hankalin nan da ya mata, taga ba yaro bane, hade rai tayi tana kallon sa, domin ranta kuna yake, toh ma meyesa ranta ze baci ne, se kawai ta saki ranta, a zuciyar ta tana cewa matar Yarima zata ga miskilanci da hali iri iri

"İna mai neman alfarmar ki biyo ni dan Allah" ta jiyo muryar shi a tsakar kanta, da kaman baza ta bishi ba se kuma tabi bayan  nashi.
Wani waje ta gun sashen Hajiya Babba suka je, nan taga Isma'il a tsaye ya juya bayan shi tare da harde hannayensa a kirjin sa, karasowa tayo tare da dan durqusawa alaman gaisuwa. Murmushi ya sakar mata tare da kallon bafaden da ya kirawo ta, ido ya masa akan ya basu guri.

Read
Vote
Share and
Comment

Share pls🤧
Fadrees 🖋️ 🖋️

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now