50

250 8 0
                                    

FLASHBACK

Su kansu ganin malam na bakin rafi a gun ya matukar basu mamaki Sede sun samu relief sosai dan har seda Sulaiman yayi murmushin jin dadi tare da sakin ajiyar zuciya

Ashe koda Malam na bakin rafi ya iso masarauta aka kawo sa sashen Yarima direct, da ya shigo shine yaga yariman da sulaiman din kowanensu a zaune akan tumtum guda daya Sede kamar babu ruhi a jikin su, karasowa yayi kusa dasu, Hamisu na biye dashi, ganin hannayensu duka biyu yayi riqe da kyalle ɗaya daukan kyallen yayi ya karanta, daga karantawa shine ya ganshi shima a kogon.

_________________

Ganin allon sihirin sa ya tsaya ba ƙaramin mamaki boka kafoor yayi ba, juyowa yayi gun Kilishi yace mata
"Yau kwata kwata ban baiwa allon sihiri na jinin bil'adama ba, sannan Wannan allon sihiri shine gaba daya tsafi na, ina so ki sama min jinin wani yanzu yanzu"
Ya karashe yana me kallon Malam na bakin rafi cike da tsana.
Shikam malam na bakin rafi taɓe bakinsa yayi dan yau kam ba jini ba ko meye zasu yi Sede suyi dan se ya tarwatsa su, shi daman hanyar da ze same sa yake nema, kuma gashi cikin sauki ya same san, toh ai Barka, ya kuma gode Allah.

Kilishi ce ta kalli shugaba tace,
"Ga wadannan shugaba ka dauki jinin dayansu kasha" ta karashe tana me nuna sulaiman da Yarima, hantar cikin sulaiman ce ta kaɗa ganin abinda Kilishi tace, shi a rayuwarsa be taɓa tunanin Kilishi haka take ba, yasan cewar ita makira ce amma be taɓa zaton bata da imani ba sai yau, ashe dama azzaluma ce? Ashe dama mushrika ce? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, shi kanshi Yarima abinda ke ransa kenan, gaskiya yayi underestimating din Kilishi sosai, ashe ita so take taga bayan su, Allah me iko.

Muryar shugaba ne ya dawo dasu daga duniyar tunanin da suka fada
"Wannan aikin da zamu yi dan ke zamu yi shi yar tsogai, sannan jini me ƙarfi muke bukata, gashi wannan tsohon banzan ya ma wadannan wasu siddabaru, in dai har kin amince kina san burin ki ya cika, Sede ki bada jinin ɗaya daga cikin ya'yan ki"
Sanda ya karashe fadan haka Seda Kilishi taja da baya, meye????😳😳
Ta bada jinin ya'yan ta inaaa, toh amma fa burikan ta zasu cika, kawai ta hakura da daya, ya zata yi.
"Ka dauki jinin dayan su kayi kawai"
Suka jiyo muryar Kilishi cike da tabbatarwa, wallahi wallahi Seda Yarima ya kusa faduwa da yaji batun ta, Seda Sulaiman ya riqo shi, wallahil Azeem Kilishi ba bil'adama bace, sam sam ita ba mutum bace, ɗanta fa fisabilillah, ɗanta na cikin ta fa, suna kallo ta cikin madubin sihiri sanda shugaba ya aika aljanin sa ya dauko masa ƙurwan Shamsu ya shanye, gani suka yi Shamsun yana ta burburwa kapın yazo ya dena motsi gaba daya.

Nan da nan shugaba ya zama wani halittan da ba'a taba tsammani ba domin ido baze iya jure ganin hakan ba, girma ya kara sosai kusan sau hamsin har kogon ya so ya matse shi, Kilishi kuwa wani murmushin mugunta ta saki, imani yana ƙara fita a ranta, koda ganin haka Malam na bakin rafi shima ya fara nasa addu'o'in suka shiga fafatawa shida boka Kapoor, ganin haka Kilishi ta dauki wani kifiya tayi hanyan Yarima da Sulaiman zata Çaka musu, da gudun su suka yi bayan shugaba, dan wani bahaguwar karfi ne Kilishi take dauke dashi, ganin haka ta kasa tunkarar shugaba se taja baya tabar ma shugaba su, kafoor yana yin wani siddabaru ba sai aljanu suka fara fitowa ba ana yin faɗar dasu? Gasu da manyan akaifu ga mugunta, Malam na bakin rafi ne ya taimaka ya fara basu wasu addu'o'i suka fara yi, dakyar da siɗin goshi suka samu suka fi karfin shugaba, dan seda dukkanin su suka ji ciwo hatta Malam na bakin rafi da kanshi, koda malam ya gama kashe su saura shugaba da Kilishi, gashi kafoor din ya galabaita, ƙona allon sihirin shugaba Malam na bakin rafi yayi, yana ji yana ta ihun azaba da radadi yana me fadin
"Ni Boka Dan boka jikan boka tsatson bokaye nafi karfin kowa, wayyoooo kayan tsafi naaa, wayyoooo, nan da nan ya fadi matacce"
Ganin ya mutu Malam na bakin rafi yace Sulaiman da Yarima su kama Kilishi kar ta gudu, ai kuwa suka damqe hannun ta tana ta zillewa ta kasa, a take kuwa ya ƙona kogon, bayan yaga kogon ya kone kurmus neyayi addu'a suka koma dakin shakatawar Yarima, already daman ya saka yaron shi ya fara duba Hafsa, koda suka iso falon, fada suka wuce da Kilishi, suna shiga fada suka ga a cike tam da mutane, ana cikin alhinin rashin Shamsu, kowa da kowa jikinsa a sanyaye yake, sai gani sukayi Malam na bakin rafi ya shigo shida su Yarima ga Kilishi riqe a hannu, sannan duk jikin su a raunace, ganin haka yasa Sarkin gida ya aika da ayi kiran kowa da kowa na cikin gidan, nan da nan kowa ya cika fada, masu kuka nayi, masu jimami nayi, kuma duk akan mutuwar shamsu da ya riske su yanzu yanzu, Malam na bakin rafi ne ya fada abinda ya sani game da boka da kuma Kilishi da kuma niyyar su ita da bokan
Koda Kilishi taji haka sai ta saka dariya me ban tsoro kana tace
"Kai a zaton ka Sulaiman zan bar ahalin ka haka ne, a'a, na aure ka ne saboda fansa, fansar abinda kuka min kaida Jafar, sannan yanzu da asiri na ya tonu, nasan zaka ce zaka hukunta Ni ne, toh nafi karfin hakan, wlh Ni Sadiya nafi karfin bin umarnin ka na iska bare wani hukuncin ka, kai bari ma kuji abinda baku sani ba, duk wani mutuwa da ake yi a cikin Masarautar nan, nine nake sadaukar da su ma boka na domin ya cika min burina na san daukar fansa, hatta da mutuwar da ɗana yayi yanzu nine na bada jinin ba, wlh billahi ko bayan raina fatalwa ta baza ta barku ku huta ba, musamman ma ke Fulani, wallahi wallahi na tsane ki, na tsani me san ki, na tsane ki kema sarauniya babba, kai ɗaya ne na taba maka so na gaskiya Sulaiman, Sede ka watsa min kasa a idona a lokacin da nake muradin ka, Sede har yanzu ina son ka, amma kuma na tsane ka na tsane ahalin ka, kai kumaYarima na tsine maka, kuma wlh alqawari na maka seka rasa farin cikin ka na har abada kuwa, kai kuma Hayatu, ina so ka daukar min fansa sannan ina so ka mulki wannan Masarautar hhhhhhhh"
Ta karashe da wani mugun dariya, gaba ki daya kowa seda ya saki salati a cikin fadan harda me martaba, Bilkisu kuwa ita da sarauniya babba da Fulani bakin su kasa rufuwa yayi saboda mamaki, wai duniya ina zaki damu, Kilishn da suka sani ce haka? Kai ina wannan ba ita bace anyi mata musaya da aljan dai.
Suna a haka sai gani suka yi ta ciro wani abu daga rigar ta ta saka shi a baki tana me dariya mara kan gado me cike da tsana, minti Uku bata yi ba tace ga garinku, jini nata fitowa daga bakin ta, Hayatu ne yayi kanta yana kuka, kowa a fadan kuwa kasa motsi yayi saboda firgici, wai rashin imani har haka?
Ficewa akayi aka fitar da gawan Kilishi, me martaba ne ya bada dokar kar wanda ya sallace ta, ai kuwa kowa ya gudu yaqi yi mata salla, Hayatu ne ya saka bayi suka kinkimeta suka je suka mata salla aka binne ta, suma ba'a san ransu suka matan ba dan umarnin yariman su ne shiyasa, da suka dawo ya sake zuwa kan Shamsu dake kwance a dakin nasu yana sakin kuka me matukar ban tausayi da kuma tsuma rai, hakika yayi rashi, ya rasa mahaifiyar sa da kuma dan uwan tagwaicin sa, ji yayi inama inama, inama shima ya bisu, sannan wai mahaifiyar sa daman haka take, ashe mahaifiyar sa azzalumace har zata iya kashe masa ɗan uwa, ɗan da ta haifa da cikin ta? Kai kaicon shi shikam, nan ya zauna ya dinga kuka a gun kamar karamin yaro, can zuwa yamma akayi wa Shamsu sutura aka kaishi makwancin sa.

FADREES 🖋️ 🖋️ 🖋️
Vote and Comment pls 🤧.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now