17

99 7 0
                                    


Zo kaji wani irin ashariya da Hafsa ta danno, domin ita idan abu ya firgita ta, badai tayi salati ba kam, sede tayi ashar saboda tafi karfi a harkan fada. Tukunna ma tsaya, wannan din wane kalan abu ne me nauyi haka da ze fado kanta, sumbatu ta fara yi  "Wayyo mama kiga Jamila ta fado Miki kyauren dakin ki kuma tsabar rashin kunya a kaina? Gaskiya wannan kyauren mugun nauyi gare shi kamar buhu wlh yau Jamila me raba Ni dake sai Lillahi dan Ubanki zanci yau" ta karashe tana kokarin ware idon ta da kyau.
'Gamo tayi, tabbas kuwa gamon tayi, mugun gamo ma kuwa'
Wayyo Allahnta, yau dai kam tasan Yarima Idriss karya ta zeyi ko yasa wannan mugun azzalumin bawan nasa ya karya ta
Yau kam kasa bada hakuri Hafsa tayi domin harcen ta ya sarƙe, wlh ita kanta tasan tayi ba daidai ba, toh me ma ya kaita. ita kam yanzu meye mafita? Nan da nan wani tinani ya ɗarsu a ranta, kawai za tayi haukan karya, ehh kawai cewa zata yi aljanu gare ta. Daman ance tabarmar kunya da hauka akan naɗe ta.

Se yanzu ma ta lura da kyau ai shi kam gaba-daya ma akan ta yake, ita ba wannan bane ba ma matsalar ta, maganganun da tayi ne matsalan ta wanda ko rantsuwa baza tayi ba akan kunnen sa tayi shi, gashi fuskan su yazo kusa sosai da sosai kamar wanda yake shirin haɗe bakinsu wuri ɗaya, kallon juna suka tsaya yi na kusan minti biyar, Hafsa ce ta fara janye idon ta kapin shi, bai san me yake shigen shi ba a yanzu amma ji yake kamar ya rungume ta, se yaga ta mishi kyau, ji yayi baze iya rabuwa da ita ba kamar yadda Sarauniya Babba ta shawarce shi, "Kai ina, sam hakan ma ba me yiwuwa bane" idan ya rabu da ita waye zai dinga yi masa aiki kamar yadda take masa, sannan wa zai sa shi nishadi kamar yadda take sa shi, duk da wannan wani sirri ne daga zuciyarsa da shi kadai ya baiwa kansa sani sai a sa'annan ya gane irin taɓargazar da yayi, na jimawan da yayi a kanta, yanzu ai sai ta rena shi, daman ya lura yarinyar sam bata da kunya ga raini ga shegen rawan kai, a gurin neman fada kam zai iya cewa ita din babbar gwana ce.
Kapın ya Ankara yaji ihun Hafsa, se sumbatu take tana zare idanu tare da kikkifta su kamar wanda ta fara ciwon hauka, kan ya ankara yaji "Dummmm" daidai da faduwar ta daga kan gado kenan. Tsayawa yayi yana ganin ikon Allah
Sai ji yayi tana faɗin "ba zamu fita ba, ka dena kallon godiyar mu" can kuma yaji tace
"Ka tashi kayi waje, kar ka sake dawowa se dare ya tsala"
Nan da nan ya danji wani tsoro, shi dai tsoro yake kar yarinyar nan ta haukace masa ya shiga uku.
Fita yayi dakin shakatawar sa, can zuwa wasu en awanni lokacin har duhu ya fara tsalawa ya dawo ya hango hajjaju se maida numfashi ake, nan yayi tunanin ya tallafa mata ko dakin shakatawar shi ya kaita kar ma Sulaiman ko wani yazo yayi wani tunanin na daban.

Tsugunnawa yayi kamar baze iya ba, dan a ganin shi ba girman shi bane ba, can yayi tunanin yaje waje ko wata baiwa ya gani ya kira ta ta raka ta dakin su se yaga kamar in yayi hakan girman sa ya zube, can dai da yaga ba sarki sai Allah nan da nan ya ciccibe ta, shigar shi cikin dakin shakatawar tashi kenan ɗauke da ita a hannun sa yaci karo da Kilishi zaune akan wani katon tumtum tana taunar tuffa, fuskar ta dauke da wani mummunan murmushi, nan take jikin shi ya saki, Hafsan da tayi likimo a jikin shi ta ware idon ta ganin abinda ke wakana,  ai nan take ta zube ƙasa a take, wani irin ihu suka ji an saki, daga nan shigowan sarauniya babba da Maimartaba da Fulani da  kowane member na gidan suka gani nan take Hafsa ta sume dan firgici
Shi kuma gogan tsaye yake ƙiƙam fuskar shi ba annuri kamar kullum, sannan ko da wasa babu alamun tsoro a tattare da shi.
Juyawa mai martaba yayi suka hada ido da Yarima kapın yace kowa ya same sa a bangaren sa bayan Isha.

Fita kowa ya fara yi daya bayan daya aka bar Sarauniya Babba da Fulani
Sarauniya Babba ce ta karaso daf inda Yarima yake tsaye tace masa
"Ka sake yin tunani akan abinda na fada maka, domin a gaɓar da ake ciki yanzu, komai yana iya caɓe maka, Ni kuma bazan iya yi maka komai ba". Da fadin hakan ta juya sai Fulani da ta tsaya tana kallon sa hawaye taf idanun ta, tabi bayan Sarauniya Babba.
Shiko gogan yadda kasan ba abinda ya dame sa, hasali ma shi ba wani damuwa yayi ba kawai dai ya jinjina wa makirci ne irin na Kilishi, kenan duk abinda ke faruwa idon ta akansa yake, wuce wa yayi ya dakko ruwa ya watsa wa Hafsa, a firgice ta farfaɗo zuciyar ta ba abinda yake sai bugawa, tallafa mata yayi ta tashi ya maida ita kan wani shimfida mai laushi dake nan cikin dakin shakatawar, shi kanshi in an tambaye sa dalilin da yasa yake hakan baze iya fada ba, kawai dai yasan cewa yana da sanyin zuciya ne.
Wucewar sa makewayi yayi, dan yayi alola yayi sallan mangariba.
_______________

Ana yin sallan Isha sai ga kowa a sashen Maimartaba an hallara ana zaune, zaman jiran aji mai zai ce.
Can aka ga shigowar sa, kujera ya samu ya hakimce a kai, daga gefen sa Waziri Jafar ne zaune akan kujeran sede girman nasa be kai na Mai Martaba ba, se kuma sarauniya babba da ita ma take a kan nata kujeran, matan kuma akan tumtum suke zaune, sai matasan da su kuma suke zaune akan kafet.

Da addu'a aka bude taron kapın waziri ya fara koro jawabi kamar haka
"Munji labarin komai da yake wakana tsakanin wata baiwa da Yarima, kwanaki munji hatsaniya a sashen Mai Babban daki, akan Yariman Gobir da Hayatu da Yarima akan wata baiwa, wadda dakyar aka samu magana ta lafa a cikin masarauta domin kimar Yarima har ta so ta ragu a idon mutane domin kalar labarin alakar rashin mutuncin da yake tsakanin Yariman da ita baiwar da ake magana, mun kira sa har nan bai ce komai ba, daga nan aka rufe maganar kwata kwata, domin an fara tsegumi mara dadin ji a cikin bayi.
Sai yau kuma da Amaryar Mai Martaba Sadiya ta aika da kowa yazo Yarima yana lalata da wata baiwa, wanda ka'idar masarautar nan ne, bayi mata basa ma yaran sarakuna maza hidima, tsakanin su dafa abinci ne, su baiwa amintaccen bawan sa ya kai masa, sai muka samu akasin hakan domin ita wannan baiwar da ake magana akan ta, ita ke masa ko wane irin hidima. Da Sadiya ta aika da aje sashen Yarima a ga meke faruwa mun dauka kawai dai ta fada ne, domin tace mana tasha kiransa tana masa nasiha ya sallame yarinyar yayi biris da ita, daga karshe har ya so ya mata rashin kunya ma. Toh zuwan da akayi yau kowa ya ga a yanayin da ya gansu, wanda kowa yasan hakan bai dace ba, saidai bamu gansu ido da ido suna aikata wani abinda bashi kenan ba. Saboda hakan ne ma, yasa muka zartar da hukunci akan Yarima da ita baiwar.

Hukuncin mu shine za'a tsare Yarima na wata daya a sashen sa, ba tare da ya fita ba, ita kuma baiwar an sallame ta daga aiki a wannan masarautar.
İdan akwai me korafi zai iya yin magana".

Mu haɗe a sashe na gaba
A rubuta comment ayi voting da sharing

Fadrees 🖋️ 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now