Kama hannun Yarima Sulaiman yayi suka koma dakin, Mai Martaba da kansa ya aika a kira masa limamin garin, yana zuwa suka fara ma Hafsa addu'o'i shida almajiran sa, se can maraice lis, Hafsa ta farfaɗo, a take kowa ya fice a dakin bakin su dauke da fatan alheri da kuma farin ciki
Wani wawan runguma Yarima ya bata, kamar wadda ake shirin kwace masa ita, da Hafsa ta raba jikin ta da nasa sai taga hawaye yana zirara daga idanun sa, Allah Sarki tayi missing nasa sosai, so take ta fada masa halin da ake ciki akan Kilishi sede ba dama, itama hawaye ne ya ziraro a fuskan nata, ya shiga goge mata, suna a haka sarauniya babba ta shigo tana tambayan sa ya jikin Hafsan yace mata da sauki, cewa tayi yaje yayi Sallah lokacin mangariba yayi, ficewa yayi yana me waiwayen ta, Allah Sarki Hafsan sa, ashe jinya take yi shi kuma yayi tafiyan sa ya barta a cikin wahala.
Sai da ya jira akayi Isha ya dawo, sarauniya babba ce tace masa yabar Hafsa a sashen ta zuwa sanda Malami daga Yoben zai zo kapın nan zasuga abinda Allah zeyi, be musa mata ba ya gyara musu shimfida shida Hafsa suka kwanta, dora kanta tayi bisa kirjin se shi kuma hannun sa bisa cikin ta, bacci ne me dadin gaske ya kwashe su basu ma sani ba, sarauniya babba ce ta ɗan leqo taga yaya, da taga haka ta juyo da baya, ta koma dakin ta itama ta kwanta, Bilkisu kuwa tun da akayi mangariba suka musu sallama suka wuce sashen su.____________
A kogon boka Kapoor kuwa ransa ne ya ɓaci ganin daga dawowar su Yarima har sun fara aikan nemo malamai, bayan da kansa ya rufe tunanin en masarautar gabaki ɗaya akan kar ma ayi zancen nemo wani wai malami, Kilishi ce ta ɓaco, ta kwanta flat har ƙasa ta kwashi gaisuwan sa, tare da fada masa wai an tafi ƙasar Yobe dakko wani babban malamin gargajiya dan a duba me yake damun Hafsa
Dariya me matukar ban tsoro da Muryar sa me uku uku ya saka kana yace
"Gobe nan da marece ma bayin suna gaban malamin, sede har yanzu shawara ne ban yanke ba, shin in kashe malamin ne ko in bari yazo ya kuma kasa bada maganin? Kawai zan barshi yazo ya bata maganin, Ni sai in warkar da ita, in yaso nan da mako shida daman muke tsammanin dawowan Gopal sai mu kashe ta gaba-daya kawai, duk da na lura malamin da zasu kawo din shima hatsabibin malami ne, yasha kashe aljanu da bokaye, amma dai kamar yanda kika sani, Ni ba kowane kalan boka bane, Ni Boka Gagara Badau ne, duk me iya ja dani sai yayi da gaske, nan ya saki wata mummunan dariya"
Jin abinda yace tasan ya gama magana, tashi tayi ta ɓace abinta, ta koma dakin ta, dama bata yi Isha ba, tana yin sallan ta tayi kwanciyar ta, se kuwa bacci me armashi yayi gaba da ita.________________
Bayan su Hamisu bawa sun kwana a hanya washegari kusan rana suka isa ƙasar Yobe, da suka yi tambaya aka musu kwatancen mutumin suka ce eh shine, ce musu aka yi ai a garin nangere yake, dan haka suka kama hanyan Nangere, da tambaya suka je su lokacin marece yayi lis, tambaya suka yi ta inda gidan Malam na bakin rafi yake, nuna musu akayi suka tafi, ilai kuwa, gidan nasa a bakin rafi yake, dakyar da siɗin goshi suka samu ganawa da Malam na bakin rafi dan mutanen da suka tarar a gidan nasa basu ƙirguwa saboda yawansu, wasiqa Hamisu ya baiwa malam na bakin kogi, da ganin haka ya amshe su hannu bibbiyu kana ya basu dakin kwana, washe gare da sassafe suka bar kasar Yobe suka kama hanyar Bauchi, kwana ɗaya takk suka yi suka isa, inda aka ma Malam tarba na karamci, ko hutawa beyi ba yaje ya duba Hafsa, yana ganin ta yasan aikin jinnu ne saboda haka ya bata magani me bala'in karfi yanda ko nan gaba baza a iya nasara a kanta ba, bayan ya kwan biyu yana lura da Hafsa a kwana na uku ya kama hanya bayan uban alherin da aka masa a Masarauta, me martaba shi kansa besan iya alherin da ya masa ba, a haka ya koma Kasar sa ta yobe a cewar sa yabar majinyata dayawa suna jiran sa
Daga nan Hafsa ta samu lapiya, suka sake gina sabuwar rayuwa ita da Yariman ta.
Bayan kamar sati biyu suka sake fita cikin gari ita da Yarima akan keken doki, sede kamar wancan karan kayan talakawa suka sanya a jikin su, dan kar suje a dinga basu girmamawa na musamman, da suka je wurin wani me saida su ƙoyaye dasu gasassun kaji Hafsa tace tana so zata ci, yarima yace baza taci abincin kan hanya ba bayan tasan tana dauke da ciki ga abincin kan hanya ba tsafta, nace masa tayi a karshe dai sai da ya siya aka soya musu kwai aka zubo musu gasassun kajin, cewa tayi a baki ze bata, ba yanda ya iya ya dinga bata har ta ƙoshi, shima tace masa se ta basa, yace baze ci, karshen ta dai ɗure ta masa, tsabar yanda suka cika cikin su dakyar suke tafiya, da zasu tafi suka biya wa duk wanda suka zo siyan abu a gun kudi, zo kuga murna a gun mutane, se kirari ake ta musu da addu'o'in Allah yabar su tare, da suka fito suka samu wani waje a waje suka zauna suna kallon wata da taurari, hafsa ne tace masa
"Mijina ka kalli taurarin can yanda suke haskaka sararin samaniya, amma kuma ka lura ai wata yafi haske, su taurarin ƙawata saman suke yi"
Murmushi ya mata dajin haka, kana yace mata
"Kece tauraruwa ta Abar ƙaunata, bazan taba dena sanki ba har abada"
Ita kuma dariya tayi tace
"Ni kuma kaine Wata na, bazan taba dena sanka ba har abada"
Murmushi me cike da kasaita ya sake saki, kana yace ta miqe su koma masarauta dare ya fara tsalawa sosai,
Miƙewa tayi suka shige keken doki har a lokacin suna rungume da juna, acikin keken dokin take ce masa
"Kasan lokacin da kake saka fadawan ka su dake Ni irin ashar din da nake ɗura maka kuwa?"
Murmushi yayi sosai yace
"Na sani mana, ai Allah ne ya dora ki a kaina"
Ya bata amsa
"Wato baza ka bani hakuri ba ma, ai wlh naso dana aure ka in hukunta barau, kawai na kyale sane saboda haƙuri na"
Ta karashe tana hade rai
Dariya yayi a ranshi wai 'hakurin ta', chap in ka taɓo Hafsa ai ka taɓo bala'i.Haka rayuwa taci gaba da tafiya, inda yau Gopal ya dawo daga kasar sin, riqe da maganin da yaje dakkowa, sede yana kawowa ya mutu, dan rabin jikin shi ya shanye a garin fafutukar nemo maganin, domin yasha bakar wahala, dan a cikin Sardaunan aljannu she sadauki me sosai Seda yakai inda ake bukata kamin ya tafi, ganin haka aljanu suka fusata suka daura lefin akan Hafsa, boka Kapoor yana karbar maganin ya saka wata razananniyar dariya me ban tsoro tare da yin hawayen jini, kamin yace
"Lalle in ban kashe yarinyar nan nasha jinin ta na baiwa aljannu na jinin ya'yan ta ba ban cika zama shahararren boka 'Gagara Badau kafi kowa ba', na rantse da tsafin kakanni na se na dauki fansar Gopal na sadaukar da rayuwar sa da yayi, dole ne in dauki fansa, fansa, fansa, Hahahahaha"
Ya karashe cike da dariyar mugunta, wani siddabarun tsafi ya fara, kamin ya raba maganin da Gopal ya kawo kashi biyu, kashi daya ya aika zuciyar Hafsa, kashi dayan kuwa dashi ze dinga bawa duk mai neman taimako a gunsa taimako.
Wannan kenan.Ghost Readers 🙄 😡
YOU ARE READING
YARİMAN HAFSA
Historical FictionA 1950's Love Story Labarin Rayuwar Yarima Idriss, ɗan Sarkin Bauchi, tare da wata fitsararriyar yarinya me suna Hafsa. Ku biyo domin ku ji yadda zata ƙaya Share please. Fadrees_20