29

62 6 2
                                    


Maman Habiba da uwargidan me anguwa da Lantana ne suka rakata a hakan sai da aka yi rigima da Mama Kulu dan tace itama sai taje, dakyar aka samu ta koma, sai kuma a yammata Habiba da Jamila ne suka je. Itama Jamilan seda ta nace kapın,  sai kuma yaya fati da yaya halime, suma suna kaita suna ganin sashen nata basu jima ba aka dawo dasu gida, tare da yi musu kyauta, ɗan nasihan nan ma da ake ma amare ita Hafsa an manta ba'a mata ba, dakyar kuwa aka raba Hafsa da Jamila, dan ƙanƙame ta tayi sosai, da suka dawo suka dinga bada labarin kyawun Masarautar, Dije harda kukan ta na bakin ciki, Azima ce dai ta danne nata.
Jamila da suka dawo ta wuce dakin maman su, ta dinga tausar ta, dan Mama Zainabu sai kuka take yi, ita tsoron ta bai wuce ace za'a kashe mata ƴa ba, ganin haka har seda maman Habiba tasa baki kan Mama Zainabu tayi shiru.
Da suka kwanta zasu yi bacci, Jamila ta dinga baiwa Mama labarin kyan sashen Yarima, da ma masarautar baki daya, duk da mama itama daga can tazo ai shekaru sun ja, daga baya Mama ta fara murmushi, amma ita tsoron ta daya, tana hakikanin tsoron GIDAN SARAUTA.

___________
A bangaren Hafsatu kuwa wani keken aka sake aiko wa ya dauke ta akai ta harabar sashen Sarauniya Babba, saidai wannan ba na doki bane, akan za'a musu karamar walima, a lokacin har anyi isha ma, tana zaman ta ita kadai wata baiwa ta shigo ta taimaka mata tayi wanka ta canza kaya kana ta fito da ita bayi mata sai take mata baya suke, shiga cikin keken tayi fadawa garada majiya karfi suka daga

___________A bangaren Hafsatu kuwa wani keken aka sake aiko wa ya dauke ta akai ta harabar sashen Sarauniya Babba, saidai wannan ba na doki bane, akan za'a musu karamar walima, a lokacin har anyi isha ma, tana zaman ta ita kadai wata baiwa ta shig...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Fadawa dauke da Hafsa a yayin da ake tafiya da ita haraban sashen Sarauniya Babba.

Mutane ne a wurin a cike, dukkanin su yan familyn sarauta ne, kowa yasha kayan alfarma, dukkan su dai mata ne, sai kuma masu yi musu hidima, a gefen kujeran Gimbiya Bilkisu kujerar Hafsa take, tana isa kuwa bayi suka kama ta aka ajiye ta aka fara walimar, kide kide kawai kake ji da bushe bushe, bayan anci ansha ne, Sarauniya Babba ta gama musu nasiha aka kaisu gun da Fulani take zaune ita da yan masarautar su suka mata gaisuwa, sannan aka kaisu gun da Kilishi itama take zaune, daga nan aka kaisu gun da mama Zulaiha take zaune itama da nata dangin, daga nan aka dauke amaren aka kaisu sashen mai martaba dan ya musu nasiha
Da suka shiga ba kowa a cikin daga Mai Martaba da kansa sai Baba Waziri.
Nasiha aka musu mai ratsa jiki, sannan aka sallame su, Mai Martaba sai kallon Hafsa yake, tuni yaji ta kwanta masa a rai.

Daukan ta aka sake yi a keken aka kaita sashen Yarima, itama Bilkisu aka dauke ta a nata aka kaita sashen Maigida Sulaiman.
Da isan su Hafsa bayin da ke mata hidima suka dauke ta suka shigo da ita cikin dakin shakatawar Yariman, da sai a yanzu ta kare masa kallo, an canza komai, an saka launuka daban daban, kayan ado da gyaran palon da aka yi amfani dasu da gani zaka san an ɓatar da sulalla, idonta ta sauke akan teburin takaddun sa, shima gun sai kyalli yake, shiga tayi cikin uwar dakan shi, taga shima an canza komai hatta gadon dake ciki an canza, komai da komai zubin sarauta, nan da nan hantar cikin ta ya kada, wannan uban ganima anya ba saida ta akayi ba? Ko dai itama mutuwar zata yi ne?, shiga makewayi tayi, tayi alwala tana kare ma makewayin kallo, shima pa an canza komai da komai.
Can dai da taji shiru bai shigo ba, tayi shimfidar ta a kasa ta kwanta, ita daman tasan sam ita ba tsaran auren sa bace, kila ma yana can rai a ɓace a aura masa baiwa, ko kuma yana can yana tunanin kalan azaban da zai dinga bata, ai nan da nan kuka ya suɓuce ma Hafsa, gashi jiya jiya taji labarin an samu en uwan Maman ta, Allah Sarki Allah ya sa mama ba kuka take yi ba, dan jiya bata yi bacci ba kwana tayi tana kuka, ko yaya injiniya yake ji? Shida yake shirin wai da Baba ya dawo yazo asa musu rana? Allah ya sa bai daga hankalin sa ba. Rayuwa kenan, dubi yadda rayuwar ta ta canza a kasa da shekara, ita idan aka ce mata za tayi aure a yanzu ma, musawa zata yi, amma yanzu da ta tashi auren wa ta aura? Ta auri Yariman gaba-daya garin Bauchi wanda ake sa ran shi zai zama Sarki a nan gaba, wai itace nan gaba zata zama matar babban Sarkin daya daga cikin manyan masarautun Kasarsu. Allah Sarki wa yaga Hafsa sarauniya, cap za'a ga hauka wallahi, motsin bude dakin taki, nan da nan ta matse idanun ta tayi likimo kamar tana bacci. Ta wutsiyar idon ta take hango shi yana kokarin cire rigar jikin shi, ai nan take ta damqe idanun nata da kyau kar tayi gamo. Tana gani ya shige makewayi bai jima ba ya fito, jikin sa sanye da ƴar shara da wando gajere, wayyoooo Allahnta ai a take ta sake damqe idanun nata, itakam meyesa take ta ganin abinda yafi karfin ta ne? Daga karshe harda sa hannun ta a wurin rupe idanun nata, Shi kuwa Yarima ganin haka ya saki murmushi, shi daman tun kallon farko da yayi mata ya gane cewar ba bacci take ba, bai tabbatar da hakan ba kuwa seda yaga ta sa hannu ta rupe idanun ta, gaskiya yarinyar nan akwai wauta, shidai zaiga ikon Allah, shi har yanzu bai san me zai ce game da wannan auren ba, gaskiya ba girman sa bane auren baiwa, toh amma ba wanda ma yasan da tayi aiki a Masarautar, sannan shine silan kawo ta, ƙila da be kawo ta ba baze santa ba, yanzu dai zeyi managing nata ko ba komai zata dinga ɗebe mishi kewa.

Gaban ta yaje ya tsaya, yace mata "ki tashi kizo kici abinci" Hafsa yi tayi kamar bata san me ake ciki ba, dan sai minsharin dole take ja, shiko da yaga haka sai yace "toh tunda haka ne, baza ki tashi ba, Ni bari na dauke ki na kai ki gurin abincin" shi da gatse ya fada amma Hafsa sam bata fahimta ba, sai gani yayi wai ta tashi kamar mai bacci sai miqa take tana goge idanun ta da hannun ta, wai da ta ware idanun nata sai tace "Mama waye a kaina? Ya nake ganin kamar suffan bujimi, bujimin ma me kama da wannan mummunan Yariman"
Murmushi ya saki a ransa lalle ma yarinyar nan ta raina sa sosai, wato dai shine mummunan, kuma shine bujimin, lalle kam. Well done.
Samun bakin shi yayi ya furta "fara kyakkyawar budurwa mai hankali da sanin Yakamata, Hafsatu Sule, Ni ne ma mummunan, baya da hakan na koma bujimi, toh Ni yanzu wanne kalan hukunci Yakamata in baki ne? Ya karashe da alamar tambaya yana mai kallon Hafsan, zubewa a kasa Hafsa tayi tana mai neman yafiya, domin in shi bai san menene dakin duhu ba, toh ita ta sani,
"Barka da warhaka Yarima mai jiran gado, Allah ya baka sarautar Bauchi" ta karashe da yin yaqe, wai sai yace mata "zaki so haka mana, ai idan ya bani kece sarauniya ta, shiyasa kika roqa" murkuda masa baki tayi, cikin rashin sa'a sai akan idanun sa.
Giran sa daya ya daga, nan da nan, yasa hannu daya ya dago ta gaba daya ta fada jikin sa hannun sa zagaye a ƙugun ta.
"Sake in gani?" Ta tsinkayi muryar shi
Amma sai Hafsa tayi shiru tare da sunnar da kanta kasa, bakin nata ya mutu
Jikin bango ya kaisu sa'annan ya sake tambayar ta
"Sake maimaita wa in gani?"
Jikin hamsatu ne ya kama rawa, can ya tsinkayi muryar ta tana cewa "Wallahi Ni bada kai nake ba, kuma kai ai kyakkyawa ne ba mummuna ba, nidai ka sake Ni inyi kwanciya na, na fasa sallan" ganin irin kusancin nasu yayi tsanani ne ya sata fadin haka, amma abinda ya mata next ya bata mamaki da tsoro da  kuma kunya.
Yarima ne ya haɗe bakinsa da nata yana mata abinda bata taɓa mafarkin sa ba.

Mu haɗe a na gaba.

Fadrees 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now