13

77 8 0
                                    

A matuƙar razane Hafsa ta kalle shi, jin sautin abu ya fadi ya sa ta juyawa cike da mugun tsoro ta kalla menene ya fadin, wani Akwati ne yazo faɗawa a kanta shine ya janyo ta jikin shi dan kar abun ya sauka a kan ta.
Wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tayi lamo a jikin shi kapin ta ankara da abinda tayi.
Nan take ta fara bashi hakuri tare da tsugunnawa, shiko gogan se kallon ta yake, shi tunda yake be taba kusanto mace kamar yadda ya faru yanzu ba, hasali ma shi ba me san sha'anin mata bane, sannan Bilkisu tasha rungume sa amma ba wai shigen haka ba, besides Bilkisu kanwar sa ta jini ce so baze sa ta a lissafi ba se kuma yayyen sa da suke aure a wata nahiyoyin

Daga idon ta tayi ta kalli fuskar sa, Namiji ne shi kyakkyawan gaske, yana da zubin mazajen da kowacce macen da takai mace zata so shi, kamannin sa ta hango da Fulani, yanayin idonsu da bakin su, sai hancin mai martaba da ya dakko, wanda shi kuma ya gaje shi ne daga mahaifiyar sa sarauniya babba.

Aƙalla sun kai minti Uku zuwa biyar suna kallon junan su. Ita Hafsa yaba kyawun sa take, lalle mummunan Yarima kyakkyawa ne, No wonder take jin matan bayi suna yaba kyawun sa, ita dai tana aiki ne a karkashin sa amma gaskiya bata taɓa kallan fuskan sa na rabin minti ba domin kanta a kasa take masa magana, sannan ko ta masa kallon minti dayan ma, ba kallon kyakkyawa take masa ba, kallon goggon biri take masa, shi kuma Yarima on the other hand kawai yana mamakin yanayin ta ne, ashe dai akwai side nata me tsoro, shi kallon fitsararriya yake mata wanda zata iya dambe da maza goma ma (be san zata iyan ba😂🤌), sannan yana mata kallon mara kunyan gaske dan shi tun da yake a rayuwarsa da bayin gidan su babu wanda ta taba yaɓa masa magana kamar Hafsa, babu wanda ta sha masa kuskure ya kyale ta kaman ita. Hafsa ne ta fara janye idon ta se shima ya janye nasa, "zaki iya gyara dakin, kapın nan, ki ware min kayan da zan saka gobe" ya karashe Yana ciccin magani, zama yayi akan wani kujeran katako dake dakin yana me lumshe zara zaran idanuwansa kamar me bacci, se da ta gama kimtsa dakin sa'annan ta ware wasu kaya kala biyu da suka mata masifar kyau

"Gasu nan Ranka ya dade" bude idon sa yayi ya kalla. Pantalon ne da wata yar shara da alkyabba mai zaiba, daya kalar ruwan kasa daya kuma shuɗi. Ga rawaninnika daya ruwan kasa daya shudin, Masu shuɗin yafi tafiya da hankalin sa, nan ya sa ta ta kimtsa su a jikin mahangar kayansa, can dai da yaji alamun duk ya'yan sarakunan nan sun watse, se ya sallame ta tare da gargadin ta akan gobe tazo da sassafe.
Fitowa tayi tana mitan yawan aikin da yake sa ta, kiciɓus tayi da Isma'il, durqusawa ta ɗan yi ta gaida shi, shiko se sakin murmushi yake yana ta jan ta da magana se yaba kyawun Hajiya Hafsa yake, nan kuwa se ga Hafsa ana zuba dariya har da tsugunnawa kasa, daga kanta ke da wuya ta ganshi ya sha mur, fuskan shi kamar na mutuwa ai Hafsa bata san sanda ta ruga ba, ko wai waye bata yi se ganin ta tayi akan katifar ta tana maida numfashi lokacin dare yayi already.
Murja ta hango tana shaqar bacci, gefen katifar Murja ta kalla taga akwai kwanon silba ciki kuwa dambu ne kusan rabi, nan take taji yunwan cikin ta ya dawo, ai ba shiri ta fara jefa hannun ta tana mikawa baki, seda taga bayan kwanan kapın ta wanke hannun ta ta kora da ruwa se kuma da taji kiran Assalatu.

Yau Hafsa dambe suka kwasa a gurin wanka dan tace ita zata fara shiga kuma an riga ta, Murja se jan ta take tana fusgewa, kunsan halin mutumiyasss seda tayi kapın hankalin kowa ya kwanta, nan kuwa ta hankada murja ciki ta janyo kofan suka fara chachan baki da yammata sa'annin ta, ganin ba yadda suka iya da ita ne yasa suka kyale ta, gashi babu dogarin da yake dukan ta ballantana su kai karan ta, can sega Murja ta fito suka wuce dakin su suna dariya.
Bayan sun shirya suka karbo abincin su suka zauna suka ci kapın suka fice.

Tun daga sashen su suke jiyo kararrakin tambura, dasu kade kade da kuma bushe bushe.
Ta tabbata yau ne ranar gasa. Sashen Yarima ta wuce ta same dakin a rupe alamun be ma tashi a bacci ba, se a lokacin ta tuna bata mayi sallar asuba ba, nan ta miqe ta iyo sa domin tayi wankan sallah.
Ta ɗan kishingida akan kafet kenan bacci ya fara fusgar ta taji karan bude kofa, nan take ta miqe tsaya, ta gaida shi ya mata alama da ta shigo, abun se ya bata mamaki, domin bata shiga dakin sa a irin wannan lokacin domin kamar lokacin wankan sa ne, ilai kuwa da shigan ta ta gan shi a tsaye dakin ya kaure da kamshi, alama ya mata da ta saka masa kayan, murkuda masa baki tayi akan baza tayi ba, se kuma ta rupe bakin nata da hannun ta tana me zare idanu.
Kallon irin kallon da yake mata ne ya sata daukan kayan nasa cikin sauri ta fara sa masa. A garin saka kayan taje ta gogi fuskan shi da tafin hannun ta, nan ta fara bashi hakuri shiko ko a jikin sa, rawanin ne bata iya daura masa ba, se ga Sulaiman yayi sallama, durqusawa tayi ta gaida shi, tayi waje ta tsaya, can Sega su sun fito nan tabi bayan su, se sashen Mai Martaba, ashe an shirya karın kumallo da za'a yi da dukkanin sarakunan da ya'yan su, sannan an hana bayi shiga se wasu daga cikin manyan bayi, nan Hafsa dake binsu ta dawo daga baya tana dan juye juye, hannun ta aka damqa ta juya da niyan yin masifa taga Murja ce, nan suka samu wani wuri suka zauna suna ta ɗan tattaba hirarraki da gulmace gulmace.

Seda suka dan dauki lokaci kapın suka gama, aka tafi filin polon da za'a yi wasan, girman gurin fadar sa bata lokaci ne ma, tambura da kide kide ya cika ko ina har ma baka jin maganan na kusa da kai ga mutanen gari da waje anzo an cika gurin har ba'a cewa komai
Can aka fara gudanar da wasannin inda za'a fara da harba kwari da baka, yaran masarautu biyar ne suka fara
Nan aka fara yi masarautar Zaria yazo na daya, wasa na biyu kuma da takobi aka yi inda masarautar Kano ta cinye, anyi wasanni a ƙalla kusan goma masarautu daban daban na cinyewa, Seda aka zo wasan karshe, wanda shine idan mutum ya cinye masarautar su ce tayi nasara, wasan doki hawan doki.

Let's meet in the next Chappy

Vote
Share
Comment

Fadrees🖋️🖋️

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now