36

122 7 0
                                    

Shamsu ne ya kama Hayatu suka wuce sashen su, taimaka masa yayi ya zaunar dashi a bisa kan gadon nasu, muryar Hayatu Shamsu ya tsinta yana me fadin
"Na rasa me yasa Umma ta kasa fahimta na, soyayyar yarinyar nan bani na ɗorawa kaina ba, bansan yaya zan yi ba Shamsu, nikam ba kaine kace min baka da kama ta ba? Me ya sa toh baza ka taimaka min ka cika min burina ba na san mallakar ta ba?, kwanaki da aka kore ta a masarautar nan me kace min? Toh bari Ni in tuna maka da kaina, cemin kayi ka sa an binciko ahalin ta? Yardar umma kawai ya rage min? Da muka zo muka wa Umma maganan tace bata san in sake koda kiran sunan ta bane, yanzu kuma me Yakamata kamin?, kamata naga yayi ka taimaka min in yaqi soyayyar yarinyar nan, ba wai kawai ka zuba min idanu ba, kodan baka san yadda nake ji bane, baka san ya nake jin zuciya ta bane shiyasa" Hayatu ya karashe muryar sa cikin kunci da bakin ciki
Maganan Shamsu ne ya dawo dashi daga kuncin zuciyar da ya shiga,
"Kar kace haka Hayatu, bawai ina kin taimakan ka bane akan wani dalilin, a'a ina yin hakan ne dan ina tsoron maka fushin uwa ya hau kanka, kaga dai umma ba ta san alaqar nan naku, kaga ai be kamata mu saba ma umarnin ta ba, kuma dagaske nake nasa an bincika min ita kawai dai ban wani maida hankali bane akai saboda furucin da Umma tayi, sannan yanzu alaqa a tsakanin ka da yarinyar nan baze yiwu ba domin ta riga da ta auri Yarima İdriss, ko babu komai matar yayanka ce yanzu, be kamata ma ka dinga furta irin haka ba gudun kar ma a jiyo ka a samu matsala, shi kanshi nasan da yasan itace wadda kake so bana tunanin ma zai aure ta, dan Allah Hayatu ina so ka saisaita zuciyarka ka rungumi ƙaddara, sai kaga abu yazo maka cikin sauki kaji? Ni sam sam bana san in dinga kallon ka cikin wannan yanayin, ka cire ta a ranka tunda yayanmu take aure kai kuma sai kaga Allah ya baka wacce tafi ta a komai ma".
Shamsu ne ya karashe cike da san kwantar ma Hayatun hankali.

Ajiyar zuciya Hayatu ya sauke, ba wai dan ya gamsu da abinda Shamsu ya fada masa ba, a'a shi tunanin neman mafita ma kansa ma yake ko ta halin ƙaƙa kuwa, murmushin yaƙe ya sakarma Shamsu, wanda hakan ya kwantar ma da Shamsu hankali har ya sarara tare da kashe musu fitilan dakin suka yi bacci.
_______________
Yana nan yana sake sake a ranshi har besan sanda bacci yayi awon gaba dashi ba.

Da sassafe suka farka, aka kawo musu abun karin kumallo suka karya, basu jima da karyawa ba sai ga Salman yazo bayi na take masa baya, bayan sun gaisa suka kama hanyar zuwa sashen Sarkin Gombe, iso aka musu suka shiga suka kwashi gaisuwa, bayan haka suka yi masa sallama suka wuce gun abun hawan su, bayan sunyi bankwana da Salman ya musu alkawarin in Sha Allah wataran ze zo Bauchi suka kama hanya

Seda suka kama tafiya hankalin Yarima ya kwanta dan Allah Allah yake ya ganshi gashi a cikin Birnin Bauchi, tafiyar awa biyar ya kai su garin Bauchi me tarin albarka, suna shigowa Yarima yace da Sulaiman akan zeje sashen sa ya dawo
Sulaiman ne yace masa "Gaskiya baza ayi haka ba Yarima, tunda gamu a kusa da fada can yakamata mu fara zuwa, mu bayar da sako sai mu wuce uzurirrikan mu, kar ka manta Nima fa banga matar tawa ba tun jiya, dan Allah ka jure muje kapın".
Ba'a san ransa yabi Sulaiman ba, dan hakan shine daidai amma wlh so yake yaje yaga yaya ake ciki.
Wucewa fada suka yi suka miqa gaisuwa bayan haka suk bada sakon da suka dawo dashi tare da fadin irin karramawar da aka musu a can ƙasar Gombe, hakika fada taji dadin wannan karamcin nan da nan ta sallame su da suje su samu hutu, sallama suka yi suka fice, Yarima ya wuce sashen sa.

Ko da Fulani taji labarin Yarima ya dawo har ya wuce sashen sa be neme ta ba for the first time, se taji ranta ya ɗan sosu, duk sanda zai yi bulaguro indai ya dawo toh sashen ta yake fara zuwa kapın yaje fada ma, amma yau guda taga sauyi ba ma haka ba, yarinyar da yake yi domin ita, ba tashi take ba, amma babu komai zata ci gaba da a'a masa idanu.

Tafe yake cike da ƙasaita da çıkar zati, ƙira ce ta jiki da Lillahi ya bashi me kyau ma kuwa, domin yau se naga ya kara min kyau sosai da sosai, hancin sa a miqe ras idanunsa kuwa har wani sake shudanye wa suke yi tsabar kyalkyali farar fatar nan tasa kuwa sai walwali take, duk inda ya gifta zaka ga ana ta kwasan gaisuwa, sede yau fuskar shi ba kamar ta kullum nace domin ranshi a mugun haɗe yake, ganin yanayin nasa na yau yasa mutane shiga taitayin su domin a asalin Yariman sa ya fito yau, wato Yarima Idriss me jiran gadon kasar Bauchin Yakubu, ko da ya isa sashen nasa se yaga kofar a bude, babban dogarin da yake masa gadin sashen nasa ne yace, "Allah ya baka nasara makullin sashen naka yana hannun sarauniya babba", ya karashe kansa a kasa, bece komai ba ya wuce sashen nata, yau masu gulma ma babu daman yi, dan yanayin fuskar sa in kayi magana ma zaka iya kwana a dakin duhu

Ko da ya iso ko neman iso yau beyi ba ya antaya cikin sashen nata, ganin haka fadawan da suke take masa baya suka koma can bakin gate din sashen nata domin su jira sa a ciki, abinda ya samu yana faruwa ne ya sa kafafun sa rawa
Muryar Kilishi yaji da Sarauniya Babba suna magana
"Yanzu ke Sadiya me kike so in Miki, bayan cin mutuncin da kikawa matar Yarima be ishe ki ba, kika sa aka kulle ta a dakin duhu, duk da haka kina so in sa Mai Martaba ya kore ta a wannan masarautar?, karki manta yarinyar nan fa yanzu haka tana kwance rai a hannun Allah bata san waye akan ta ba, kuma koda cikin shegen tayi kamata yayi a bincika komai a natse, bawai ki wani zo ki same Ni kina roqon wai insa ya sake ta ba, ko dai kina so kimar Yarima ya gama zubewa ne a gaban kowa da kowa na Masarautar nan"?.
Sarauniya Babba ta karashe ranta a kuntume, ita koda yarinyar ta zubda mutuncin ta a waje a hakan take san taci gaba da zama matar sa, amma ta lura wannan matar tana so ta shige mata cikin hanci, bari zata yi maganin ta kuwa.
Kar ku manta duk wadannan maganganun da ake yi akan kunnen Yarima, ya kasa motsi ne saboda jin irin mugayen kalaman da ake jifan Hafsa dasu
Muryar Kilishi Sarauniya Babba ta jiyo tana cewa
"Haba Allah ya baki nasara, Yakamata ki duba wannan maganan da nayi da kyau ki saka shi a mizani, Yarima yar kwalta ya auro, ki bani goyon baya ki sa hannu ya rabu...." Bata karasa maganan ba idanun ta suka hango Yarima a tsaye yana huci kamar zaki, kofin da yake hannun ta cike da ruwan itacen berry ne ya fadi, ta miqe a razane, tafiya ya fara yi cike da ban tsoro kamar saurayin zaki, idan da zaka taba kirjin Kilishi zaka ji kamar ze fado kasa saboda tsabar bugawan da yake, kaiii ita bata taɓa tunanin tana shakkun sa ba sai yau ɗinnan, karasowa gaban ta yayi ya tsaya, tun kapın yayi yunkurin aikata wani abu yaji ance masa
"Kul, kar ka kuskura"
Su uku ne kap duniyan nan suka isa su hana shi yin abu kuma ya hanu, be dauka zata shigo a irin wannan yanayin ba, amma baze bar matar nan ta sha ba, wato sai da taga baya nan zata wa Hafsa sharri?, juyawa yayi ya fice a sashen gabaki daya ya nufi dakin maganin masarautar domin yaga yaya jikin hafsan, domin Seda ya fada idan har ta tabbata yaga koda kwarzane ne a jikin ta, besan iya abinda ze iya aikatawa ba

Sarauniya Babba dai ko a jikin ta abinda ya faru, ita sam bata ga laifin sa ba, idan yace ze yi wa Kilishi abu tasan be dace ba tunda matar ubansa ce, amma still de ita bata ga lefin sa Ba gaskiya, hankalin ta ma ta maida kan Kilishi da take ta huci bakin ciki kwance akan fuskar ta, se Fulani da take kokarin zama domin ta gaida ta.

Vote and Follow and Share.
FADREES 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now