31

79 9 0
                                    

Kasa furta komai Yarima yayi, ita kuwa jakadiyar ta sake maimaita masa abinda ya kawo ta
Yanzu shi cewa zai yi babu abinda ya faru tsakanin sa da Hafsa? Kai ba girman sa bane hakan, toh idan ta tafi zuwa zata yi tace ai Hafsa ba budurwa bace, yana dai ta sake sake a ransa can ya samu amsar da zai bata
"Wane kyalle kike magana"?
"Farin kyallen da Kilishi tasa aka shimfida a saman gadon ka jiya Allah ya baka nasara"
Ce mata yayi shifa baiga kyalle ba in kuma za taje ta duba da kanta ne, ganin haka sai tayi mamaki, kuma bata isa tace zata je ta duba ba, sai yanzu ta lura da Hafsa, kare mata kallo ta fara yi, itako Hafsa ta galla mata harara har seda ta ɗan tsorata.
Ficewa tayi taje sashen Kilishi ta fada mata abinda ya faru, hakan da ta faɗa ya bata ran Kilishi, nan da nan tasa ta akan aje a sake shirya wani farin kyallen akan yau ma a sake shimfida musu ficewa jakadiyar tayi ita kuma, har alla alla take ace amaryar Yariman nan, ba budurwa bace, Wallahi sai ta sa zaman masarautan nan ya gagare ta, sannan zata sanya ido sosai a kanta.

Sallama aka mata daga waje, baiwar ta taje ta bude kofan, wani dogari ya shigo har kasa ya durqusa ya kwashi gaisuwa, ido ta ma bayin ta da duk su fice su bata guri nan da nan kuwa suka fice kapın kiftawa da bismillah.
Magana bafaden ya fara cike da tabbatarwa;
"Ranki ya dade, Mahaifin ta da bafade ne aka kore sa bisa ga abinda yayi wa yar shamakin wancan lokacin(nan ya bayyana mata komai hadda ƙara gishiri), sannan mahaifiyar ta ma tayi bauta anan din daga bisani ya aure ta ya dauke ta dan ita annoba ce(nan ya sake zayyano dalili), ita kuma yarinyar ita ce baiwar da aka sallame ta akan Yarima, Yarima Hayatu da kuma Yariman Gobir. Sannan nayi bincike akan yarinyar, sam bata da tarbiyya gata fitsararriyar gaske ce wacce ta addabi kowa a unguwar su, wannan auren da aka mata shine samun zaman lafiyan yan unguwan nasu iya abinda na samo kenan", nan da nan Kilishi ta dauko tsantsar azurfa ta basa yana godiya da jin dadi ya fice.
Tayi masa kyauta da azurfan nan ne dan ba'a taba kawo mata labarin da ya burge ta irin na yau ba, ta so ta sa a zane sa saboda ya saka Hayatun ta a cikin shirmen sa, amma sai ta kyale sa sbd wannan daddaɗan labarin da ya kawo mata, idan ta lura da kyau wato ta jefi tsuntsaye dayawa ne da dutse daya tak.
Nan ta saki wani mummunan murmushi, ta lumshe idanun ta cikin salama.
Baiwar da ta jima tana nema Allah ya kawo ta cikin sauki, sannan ta tausaya ma Fulani domin surukannin ta gabaki dayansu bayi ne. Wannan information din da ta samu ya isa tayi amfani da shi ta hana Hafsa zaman lafiya a cikin wannan masarautar.
Tuno irin makircin da zata yiwa Hafsa gobe yasa ta sakin wata bahaguwar ajiyar zucciya.

______________

Hafsa ne ta tsinci kanta da fadin, "Kyallen me take magana ranka ya dade, kodai wancan farin kyallen da na naɗe ne jiya, meyesa zaka yi karya bayan kyallen yana a cikin dakin ka"?
Harara ya banka mata har seda kafar ta ya kama rawa, can kamar baze yi magana ba taji yace
"Kina so kisan amfanin kyallen"
Gyada masa kai tayi da wurwuri tare da kura masa ido
Sai yace "to ki jirani zuwa dare zan fada Miki", gama fadar sa kuwa nan da nan ya fice a sashen nasa ita kuma sai mamaki ya kama ta, meyesa bazai fada mata yanzu ba sai dare yayi? Toh ya fada da kar ya fadan duk uwarsu daya ubansu daya, amma ma, sai ya fada din, yana fita kuwa aka kawo abinci, itakam zaman ta tayi ta dibi abinci da ta gama ci tayi shigewan ta dakin da akace nata ne, tayi kwanciyar ta, da taso taje ta gyara dakin Yariman, sai bayin da suka kawo abincin suka dinga roqon ta akan ta bari suyi aikinsu kar ta jawo musu matsala, da ta kwanta akan gadon ta ta fara sake sake, kodai ta sa su kira mata murja ne, nan da nan ta canza shawara, tana kwanciya can ba'a jima ba bacci yayi awon gaba da ita, cike da tunanin su Mama da Jamila

___________

A can gida kuwa, yau Mama da Baba da Jamila da su Ibrahim suka kama hanyar zuwa masarautar Borno dan sammako suka yi ma, dan tun asubahi suka kama hanya. Ba su suka isa ba sai da mangariba, gidan Galadiman Borno suka wuce direct, an musu tarba na musamman, a dakin shakatawar baki,  sai bayan isha da suka natsa sa'annan mai girma galadima ya samu isowa, da ya shigo ya samu guri ya zauna nan suka kwashi gaisuwa, tsaya wa yayi yana kallon Mama Zainabu, meyesa take masa irin wannan gaisuwan? Meyesa take tare da wadannan mutanen a zaune ma a kusa da wani namijin sannan meyasa take sanye da kaya marasa daraja?, sannan ba tace masa yau ita baza ta samu fitowa ba, ba girkin ta bane sannan bata jin dadi? Ko ma abun gaggawa ne ya kama ai dai ba ta saka wannan kayan ba, sannan shi dai a cikin kayayyakin ta in bai manta ba babu mara daraja haka ma,
Kar ku manta ita fa Mama Zainabun wai a haka ta zabo kaya mafi kyau daga cikin kayayyakin ta ne, su Ibrahim ne suka shigo, nan suka kwashi gaisuwa, Abubakar ne yayi magana "Baba nasan mai kake tunani, amma kadan jirani kadan ina zuwa, hakan da ka gani yana da alaqa da tafiyar da na ce maka zanyi zuwa ƙasar Bauchi, amma ban fada maka dalili ba" ficewa yayi can sai gashi sunyi sallama sun shigo da Mama Maryamu, malam sule mai rini ne ya miqe cike da kaɗuwa, bayan shi Jamila da Mama Zainabu ne suma cikin tsigar tsoro.
Ita kanta Mama Maryam din seda taja da baya, galadima ne kaɗai bai kadu ba a gun amma Seda ya kasa motsi tsabar mamaki, se su Ibrahim da suka riga da suka san komai.
Kasa motsawa Mama Maryamu tayi, Seda Abubakar yaja hannun ta ya karasa da ita, Suwaiba yar Mama Maryamu wacce ke biye da ita ne ta kwalla kara tare da yin baya zata afka a guje tsabar tsoro Ibrahim da yake gun kofa ya damko hannun ta, kowa da yake wajen ya kadu iya kaɗuwa, Mama Maryamu ne ta karasa wurin Mama Zainabu ta zuba mata ido, kallon kallo suke ko kyaftawa basa yi, kare musu kallo nayi, kamar su ɗaya sakk, babu abinda ya raba su sai kayan jikin su, kamar su tayi mugun baci, rungume juna suka yi, musamman Mama Maryamu da take cewa ina kika shiga Maimunatu? Babu inda ba'a duba ba, ba gun neman ki da ba'a bi ba, ba'a samu ba, Har buga ƙasa akayi akace kina raye, Baba ya mutu da kewar ki, ya mutu da baƙin cikin rashin ki, ina kika shiga Maimunatu? Se kuka Mama Maryamu take tana me yiwa Mama Zainabu mugun runguma, ita dai ido ne nata dan wani banbaraƙwai take jin abun domin bata san maganan me wannan matar me kama da ita take yi ba, sede jikin ta yayi sanyi, mugun sanyi ma kuwa, sannan ita gaskiya bata jin komai a game da matan, ita a ganin ta kama ce kawai suke yi daga Allah, duk da cewar baza ta iya tuna Asalin ta ba, ai be kamata tayi concluding kan cewar wannan yar uwar ta bace, yanzu misali idan ta amince yar uwar ta ce akayi bincike aka gane akasin hakan fa?
Se tayi yaya kenan? Amma kuma tsaya, taji wannan matar da aka kira da mama Maryamu ta kira ta da wani suna, sunan wanene kenan?
'Maimunatu'?.
A ina ta taba jin sunan nan, nan da taji hajijiya na shirin kama ta, tabar tunanin.

Ayi following account din
Ayi voting
Ayi commenting
Sannan ayi sharing.

Show some love Wattpadians, especially ghost readers .

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now