3

159 15 2
                                    

Nan take sai ta fashe da kuka
"Kaje kaima kar na jawo maka" Abinda tace kenan
Haba baiwar Allah me yasa meki? Ya tambaye ta
"Duk namijin da ya nuna damuwarsa akaina sunansa 'GAWA'"
Ai ko Sule dajin haka sai yayi baya jikinsa ya soma ƙyarma nan take ya soma jan addu'ar da yazo bakin sa sai da ya ɗanji nutsuwa sannan yace, '
me kike Nufi da haka?
"Ni bansan koni wacece ba, nidai kawai nasan nabuɗe idona na tsinci kai na acikin Masarautar nan a matsayin baiwa, kuma mutum uku dogarai sun dade da zuwa barzahu saboda na farko ya nuna yana son aure na, a daren ya margaya sauran biyun kuma don sun nuna tausayi akai na kawai, kamar yanda kake ƙoƙarin yi a halin yanzu suma suka fece" sai kuma ta sanya kuka
Taci gaba "ina cikin mawuyacin hali a cikin masarautar nan kowa hattara ta yake yi wai don.... "
Ai bata ƙarasa ba ya rufe mata baki da hannun shi yana rarrashin ta
"Ni zan aure ki"
Ai a take ta mike tsaye
Karki damu Gobe ma haɗu'
Da haka ya tafi,

Kasancewar shi almajiri a da sai ya kwana yana addu'o'i da ikon Allah babu abinda ya same shi amma yayi mafarkai barkatai
Da sassafe ya tara matan shi akan ya faɗa musu zai ƙara aure
Ai da jin haka suka fara ashar dalilin da yasa bai faɗa musu da dare ba da sun hana shi baççi
Bai saurari ko wacce ba yayi sammako zuwa gidan yayanshi ya faɗa masa
Dajin haka yace sai ahaɗa da na ƙanwarsu Hansatu
Hakanan yaje ya samu yarinyar jiya da ya naɗa wa suna Zenabu
Tayi matuƙar mamakin ganinshi da rai
Ya tambaye ta in ta yarda ta aure shi tare da faɗin yana da mata biyu da yara
Aiko ta amince, yaje ya samu Sarkin gida suka gama zance sati biyu da ya zagayo aka daura musu aure ta tare tare da ƙanwarsu Hansatu. Besha wahalar shawo kan Sarkin bayi da Sarkin gida ba domin akan a 'yantata ba kasancewar ta ƙi kowa a cikin masarautar

Ai babu irin habaicin da su Kulu basa mata da sukaga bata kula su ne yasa suka sanya mata Salama
Shekara da ta zagayo Kulu ta haifi Dije
Ranar suna ta zo masu Malam sule da Malam Musa da baqin ciki Sanadiyyar rasa qanwarsu Hansatu da sukayi, tazo haihuwa ita da abinda yake cikin ta suka rasa rayukansu a ranar kuma Zenabu ta haifi yar ta ranar bakwai aka maidawa yarinyar sunan Hansatun ana kiran ta da Hafsa wani Sati me zuwa kuwa Lantana ta Haifi Azıma

Shekarunsu biyu Zenabu ta qara haifan mace aka sa mata Jamila daga nan haihuwa ta tsaya mata
Shekarun Jamila biyu Lantana ta haifi Sadiqu. Wannan kenan

Suna nan suna zaman su har turawa suka zo da karatun boko aka saka su Lawan a makaranta duk da Kulu bata so hakan ba.

Shekarar su Halime sha bakwai bakwai akayi musu aure. Fati aka haɗa ta da Salisun kawu Musa, Halime kuma dama da saurayinta, Lokacin Ramatu yar kawu Musa ta daɗe da yin auren ta.
Lokacin su Garzali sun daɗe da barin makaranta ma, su kulu sun hana su zuwa
Shi Lawan yana yar sana'ar sa ta hannu amma yana zama a majalisa Garzali kuma shida Adamu an kai su Birnin Gombe dan yin Sana'a Adamu yana zuwa wataran, amma Garzali kam sai ya ga dama yake zuwa yanzu haka ma ya kusa shekara açan amma har yanzu bai zo ganin gida ba
Sanadiyar koran Malam Sule me rini a Fada kuma shine, shi ya kasance mutum ne mai san aiki da kula ga hakuri, hakan yasa ya zama babban dogari, abin ka da mahassada sai akai mai sharri wai an gansa da yar Shamaki wai zaiyi lalata da ita, aka kira yarinya tazo ta fada gaskiyar zance, Yarinya kuwa harda barbada gishiri akan zancen shine Sarkin Fada ya basa sallamarsa.
____________

Daga ƙarshe Hafsa shigewarta ɗaki tayı, da tagama dariyanta ta canza kaya.
Jamila ce ta shigo tana gimtse nata dariyan
"Allah Allah nake dare yayi mu fita gaaɗan nan zanga ko Ashiru zaizo hira" Hafsa ce ta faɗa hakan tare da pashewa da sabon dariya
Aiko suka jiyo muryan Mama Lantana tana balbala masifa
Har mangariba tayi Lantana tana abu ɗaya wato masifa
Suna cin abincin dare kowa ya shirya suka tafi Dandali

Acan filin gaɗa Hafsa ta hango Taron maza tsabar jaraba ta tasamma gurin haiƙan tana zuwa tace "a'a manyan samari ina tauraron naku?" Ta ƙarashe tana dariyan mugunta
"Yana gidan ubanki"
Wani daga cikin su mai suna Talle ne ya bata amsa
Bantan Ubancan ubana pa ka xaga ?
Ta ƙara tambayar sa,
dama yan unguwansu sun san halin Talle da neman faɗa Hafsan ma ba baya ba ga kuma rashin kunya
Aiko suka fara zage zage
Atake hankalin kowa ya dawo kansu
Talle ko sai zıga shi ake
Suna shirin fara dambe Su Yaya Lawan da suka zo wucewa ta gun ganin abinda ke faruwa suka zo suka raba (ikon Allah mace da dambe da namiji)
Nan aka watse, kowa sai faɗan albarkacin bakinsa yake
Suka koma gida

Bayan wasu kwanaki da misalin tara da ƴan mintina na dare bayan sun dawo daga gaada Malam Sule mai rini ya tara su babba da ƙarami suka taru
" Dalilin tara ku da nai anan shine akwai wani abokina daya ke zuwa gari gari sana'a toh yace mun zan bishi mu tafi tare saboda haka nake so ku zauna lapiya, kuma sana'ata ta rini tana nan domin Lawan ne zai cigaba dayin shi yabar zaman banza, aƙalla zan iya yin wata kafin na dawo saboda haka dan Allah ku riƙe sana'ar ku kuma (yafaɗa yana nuna su Lantana), nabar abincin da zai ishe ku har na wata hudu, sannan ku kuma Azıma ku ringa zuwa makaranta kun ga dama kun kawo ƙarshe da kun gama sai in muku aure ke da Hafsa da Dije Allah ya muku albarka za ku iya tafiya"
Yaran ne suka mike aka bar iyayen mata suna shawara da Malam Sule
Su Kulu kuwa banda harara babu abinda suke aikawa Mama Zenabu.
Bayan da ya gama musu nasiha
Suka mishi addu'a albarkacin bakinsu suka watse.
Da sassafe Malam Sule yai sammako suka tafi
___
Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya musu
Watarana su Hafsa sun tashi a makaranta suka hango wani kamar Malam Sidi a lungu shi da wata yarinya.

Habibah ƙawar Hafsa itace tace bari ta leƙa taga waye ne
Leƙawan da zatayi sai ga Malam Sidi da Zaliha a cikin lungun hannun Malam Sidi na hagu bisa kafadar Zalihan na daman kuwa yana shirin antaya shi cikin gyauton ta. Ganin su Hafsa akan su a take suka yi wiki wiki da idanu saboda sun san asirin su ya tonu
Me su Hafsa zasuyi banda shewa ai a take ta sheƙa da gudu ta koma makarantar Domin lokacin shugaban makarantar bai tafi gida ba, daman ta tsani Malam Sidi ta dade tana neman hanyan da zata rama dukan da ya mata ta rasa sannan haushin Zaliha take ji na sosai da sosai
Tana zuwa tace 'Malam Habu kazo kaga abinda ke faruwa'
Malam Habu yabi bayan ta suka je suna zuwa sai ga Malam Sidi yana neman hanyar guduwa cikin sa ya birkice
Zaliha kuma kuka ta saka a gurin
"Ku muje Ofishina"
Abinda yace kafin ya juya zuwa ofishin nashi
Su Hafsa kuwa tafiya gida sukayi kowa na tofa albarkacin bakinsa, ita Hafsa harda rankwashin Malam Sidi aikuwa Seda ya saki karan azaba, Zaliha kuma zunguri takai mata a goshi
"Na mutu na lalace"
Zaliha ne ke ta faɗin haka har suka ida shiga cikin ofishin Shugaban makarantar, wanda ransa a mugun haɗe bisa ga wannan mummunan abun da ya faru.

Masarautar Bauchi
________
Let's meet in the next chapter
Don't forget to vote and comment please

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now