11

91 9 0
                                    

Not edited

Wai Allah
Anya wannan yarinyar ba mahaukaciya bace? Ko dai aljanu gare ta, kai wannan sede aljanun ma, idan ba haka ba ina ya taba ganin jaza'i irin wannan?
Farko kwance take ba dankwali gashi a barbaje kaman kan mahaukaciya, yanzu kuma ta tashi tana uban ashar kamar wata bamagujiya.

Sulaiman ne ma ya bashi mamaki da ya ga yana dariya a gaban baiwar sa, wannan ai se ta rena shi ma, se yanzu ma ya tuna ashe ya sallame sauran ma'aikatan sa shi yasa yaji shiru
Tsaki yayi, yayi wucewar sa cikin uwar dakan sa, zama yayi ya hau zagaye a cikin dakin da idon sa, can idan nasa ya fada akan dardumar tare da kwanukan da suke kai
Tuno awaran da yayi ne yasa yayi wurin yawun sa na tsinkewa, har yaje ze bude kwanukan da kansa yaga ba girman sa bane, gara kawai ya bari baiwar nan ta zo ta zuba masa, alamar shigowar Sulaiman ya jiyo, shi kuma ya juya ya masa alama da ya kira baiwar, juyawa Sulaiman yayi ya kirawo Hafsa, ta shigo tana ciccin magani
Alama ya mata da tazo ta zuba masa abinci

Karasowa tayi tana zumbura baki, ji yayi
Kamar ya mangare ta, amma se suka zuba mata ido kawai

"Wanne za'a zuba maka ranka ya dade"? Ta tambaya tana sake haɗe rai

"Ki zuba masa awaran" fadar Suleiman kenan yana karasowa gun Yarima tare da zama,
Da jin haka take hantar cikin Hafsa ta kada, wuri wuri idon ta ya fara, tunani ta fara yi a ranta, 'wai yaushe ta zama mara tsoro ne, sannan shidin wai bashi da baki ne da baze mata magana ba har se ya fada wa wani? kuma ko zata ji tsoron ta rasa a gaban wa zata ji se gaban wannan mummunan Yariman'? Ina hakan baze yiwu ba, kafsewa tayi ta fara bude kwanon daya bayan daya kamar ba ita ta cinye awaran ba.
Se da ta gama bude dukkan kwanukan sannan ta kalli yarima tace
"Babu Awara a ciki ranka ya dade"

Hakikanin gaskiya yayi mamaki, amma kuma se ya bar zancen ya miqe yaje ya ɗan kishingida, bacci ne yayi awon gaba dashi Sulaiman kuma yayi dakin shakatawar Yariman ya zauna yan dan duba wasu littattafai a hakan shima bacci ya dauke shi

Hajiya Hafsa kuwa ta koma sashen su na bayi, ta iske Murja suka je suka amso abincin su suka zauna suna hutawa, kapın yamma yayi su ci su fita yawo.

____________

Kilishi ce tsaye a gaban sashen sarauniya babba, wato mahaifiyar Mai Martaba Jira take a mata iso

Can ba da dadewa ba bayan ta gama shaqan shanya tan da akayi, aka mata iso
Sashen Sarauniya Babba ya matukar tafiya da imani na, kamar ba sashen tsohuwa ba, A kishingide take akan tumtum ta riqe takaddar addini tana dubawa gaban ta kuwa su kayan marmari ne da kuma kayan makukashe, shigowar ta cikin sashen ta durqusa ta kwashi gaisuwa, ranta na matukar suya, na durqusa wan da tayi

Hannu sarauniya babba ta daga cike da ƙasaita wanda hakan ya qona ran Kilishi, ita a tunanin ta yin ƙasaita da ita ta dace tunda ita ce matar sarki amma dubi yanda tsohuwar banzan nan take yi

Baiwar Sarauniya Babba ce ta shigo ta isar da sakon Fulani tana neman iso
Murmushi sarauniya babba tayi ta mata nuni da ta shigo da ita
Be jima ba se gata ta shigo, ta durqusa ta kwashi gaisuwa
Nan suka dan taba hira, sannan suka sake yin magana akan gasar da za'a yi wani satin.
Kilishi se hararan Fulani take yi, domin ta tsane ta, zama ma guri daya da ita ba'a san ranta take yi ba, har Allah Allah take su gama tattaunawar ta kama gaban ta dan ranta a mugun bace yake.
İta da tazo dan wani abu gashi matar nan ta bata mata shirin ta.

________________

Bilkisu ce ta shirya ta tafi gidan waziri gurin Samira, Da yi mata iso ta samu Mama Zulaiha ta kwashi gaisuwa sannan ta wuce dakin Samira ta same ta shame shame tana kwasar bacci
Daka mata duka tayi, ta tashi a firgice se zare idanu take, me Bilkisu zata yi in ba dariya ba. Can dai ta tashi suka sha hira, anan suke hiran gasar da za'a yi, Bilkisu na cewa Allah ya hada ta da kyakkyawan Yarima ta aura, ita dai Samira cewa tayi se sun gani. Sai da suka ci abinci kapın Samira ta raka Bilkisun.

________________

Tashin Yarima a bacci yayi daidai da lokacin sallar la'asar miqewa yayi, yayi alwala yayi Sallah ya miqe da nufin yayi wa wannan baiwar yarinyar da ko sunan ta be sani ba magana tazo ta ta zuba masa abinci, to shi meye damuwarsa da sanin sunan ta ma, dubawa yayi ko ina be ganta ba, shigowar sa dakin shakatawar sa ya hango Suleiman a sheme yana bacci, tada shi yayi yace masa yayi Sallah, sannan ya tambaye sa ina baiwar, shi sai yace ya barta a dakin, wucewar sa makewayi yayi, yabar Yarima Idriss da qunan zuciya, gaskiya yarinyar nan, ta wuce tunanin shi, wato be bata izinin tafiya ba shine zata tafi? Lalle ze koya mata hankali.
Bayan Suleiman yabi ya zauna a dakin yana kumbura fuska, shi ala dole an bata masa rai, bada jimawa ba Sulaiman ya fito a makewayin ya gabatar da Sallah sannan ya jawo hannun Yariman suka dawo kan dardumar ya fara serving dinsu
Sunci sun koshi sannan suka yi haramar fita training, a can suka hadu da su shamsu sune basu dawo ba se dare.

Nan suka dunguma zuwa sashen Mai Martaba zasu masa sallama
Bayan an musu iso suka tadda shi, shida Waziri, nan suka musu nasiha, sannan aka sake tunatar dasu akan gasan da za'a yi wani makon da yardan Allah.
Da suka fito sashen Sarauniya Babba suka je suka zauna suka dinga hira, se tsokanan Yarima suke amma yayi fuska, ita ko se cewa take su kyale mata miji ya huta.
Nan Sarauniya ta ringa basu labaran yanayin sarautar su lokacin da take budurwa.

Seda dare ya tsala tukunna ko wannan su ya nupi sashen shi da niyan yayi bacci. A yayin da wasu suke haramar bacci a lokacin wasu suke tashi. Bayyana wannan halittar ta sake yi a gaban Boka Kapoor, tayi masa sujjada, ta kora masa dukkanin bukatun ta, shi kuma ya bata tabbatuwan nasara.
Nan ta zama wata kalar halitta ta bace.

_________

Kilishi ce kwance akan gadon ta kamar mara rai, domin sam bata motsi ko kadan, can se ga wani abu a ta sama shiba aljani ba shi ba fatalwa ba. Tsira masa ido nayi da kyau domin gane ko menene, can dai abun yazo ya shige jikin kilishi, nan take ta sauke ajiyar zuciya ta miqe
Hakikanin gaskiya na tsorata, tashi tayi taje gaban wani madubi dake jingine a dakin nata tana kallon kanta, ta cikin madubin kuwa mutum ce kamar tsohuwa me matukar ban tsoro, dariyar mugunta ta saka sa'annan ta rikida ta dawo ainihin siffanta.
Wannan kenan.

________

Hajiya Hafsatu kuwa kwanan dadi tayi ranan, domin yawo ta dinga yi kusurwa kusurwa tana me neman tsokana, duk inda ta samu kuwa kaga fada ta kaure, da kanta seda ta gaji sannan suka koma daki, Murja kuwa se dariya take tayi, tana mamakin taurin ran Hafsa da kuma rashin tsoro
Da dare yayi suka koma gun karban abinci suka karbo suka ci abun su. Hafsa tsabar taurin kai ƙin komawa sashen Yarima tayi, tana ganin Murja taje sashen sarki ta dawo.
Da dare tsabar gajiya ko fitina bata tsaya nema ba bacci yayi awon gaba da ita, da asuba ma kin tashi tayi wanka tayi, Seda wajen karfe tara ta tashi tayi wanka taci abinci kapın tayi haramar tafiya sashen makiyin nata

Let's meet in the next chapter
Vote and comment and follow.
Fadrees🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now