22

120 6 0
                                    

Mai unguwa kuwa da suka shigo tare da Lawan, suka iske Yarima a tsaye yayi mutuwar tsaye, zubewa a kasa yaya Lawan yayi, ya kwashi gaisuwa
Nan da nan Yarima ya zauna, tare da daga masa hannu alaman ya amsa.
Guri mai unguwa ya nuna wa Lawan da ya zauna, shima ya samu guri ya zauna suka zuba wa Yarima idanu
Hannu Yarima ya daga wani saurayi ya shigo, Lawan ne ya lura da saurayin da kyau, sai yaga ashe yana yawan ganin sa a gidan simintin da ake ginawa na jikin gidan su.
Saurayin mai suna injiniya Kabir ne ya shigo ya zube ya diba gaisuwa kan ya fara magana kamar haka
"Ginin gidan ya kammala ranka ya dade, komai da komai an saka a ciki kamar dai yadda ka umurta da ayi shi saura kuma umarni na gaba"
Kallon jinjinawa Yarima ya masa, kamar da hadin baki sai ganin shigowar Sulaiman suka yi, nan da nan su Lawan da injiniya har ma da mai unguwa aka kwashi gaisuwa
Da ya natsa ne ya fara bayani kamar haka;
"Gidan da aka gama gina wa kyauta ce Yarima ya baiwa Hafsa domin irin jajircewar ta gurin aiki a Masarauta, idan ban yi kuskure ba ma, akwai saqon da aka rako ta da ita tun ranar da ta dawo, dayan makullin gidan yana ciki, sauran makullayen kuwa gasu a nan, za'a baku ku tafi dashi, wannan shine dalilin da ya sa aka nemi mahaifin ta sede baya nan, shiyasa aka nemi yayanta, sai kuma mai unguwa da aka biyo ta hannun ka dan ka zama shaida kai da Kabir gashi a nan.
Tun da aka fara bayani jikin Lawan ya kama karkarwa jin zancen yake kamar almara, haba inaaa, ai hakan baza ta sabu ba wai bindiga a ruwa. Da aka gama zance kuwa Lawan ya fada kasa yana mai fadin
"Kuyi min aikin gafara Allah ya baku nasara, wllh baza mu iya karban wannan gida ba, domin yapı karfin mu, sannan mutane zasu yi ta cece kuce ne, za'a ce ita Hafsan nawa take da za'a bata kyautan wancan dankareren gidan, sannan wane irin aiki tayi haka da mai girma Yarima zai bata wannan danqareren gidan"?

Da jin haka Seda Sulaiman ya murmusa, yasan za'a rina daman, wai an saci zanin mahaukaciya, can dai ya samu karfin halin budan bakin shi tare da cewa, "kenan bakwa san kyautar da Yarima yayi muku kenan" nan da nan Lawan ya kama karkarwa tare da cewa "tuba nake ranka ya dade, sam ba haka nake nufi ba, wane Ni in raina abinda ya fito daga fada, sam ba haka bane".
Budar bakin Sulaiman kuwa cewa yayi, "gidan nan dai kyauta ce Yarima yayi wa Hafsa, ga nan makullai, mai unguwa ka zama shaida, nan da nan mai unguwa ya fara koro godiya, tare da sanya alheri.

Miqewa suka yi, bayan sun ajje ma mai unguwa nasa rabon a wata jaka, budewa yayi yaga a cike suke da sisi ne, taro da kwabbuna, kudi kusan fam dari da wani abu, ai bai san sanda yabi bayan su ba, ya cigaba da surfo musu ruwan du'a'i.
Sai da suka shige keken dokin kapın ya koma gidan sa cike da matsanancin farin ciki mara misaltuwa. A nan ya tadda Lawan a rikice idanu ya firfito, nan yace ma Lawan ya dauki makullai ya tafi, Lawan yaqi dauka, karshe dai in takaice muku zance, barin makullan yayi yace ya bari idan Malam Sule Mai Rini ya dawo sai ya rako sa ya masa bayanin.
Wannan kenan

__________
Bayan da suka shige keken dokin, gidan gonan Sulaiman dake unguwar gaban na su Hafsa suka nupa.
A ciki akwai lambu babba sosai, akwai dabbobi kala kala, kama daga dawisu, jimina da agwagi da dai sauransu, a daya bangaren kuwa kayan marmari ne iri-iri, kama daga lemu, ayaba, kankana, tuffa da dai sauransu, sannan a ciki akwai shuke shuke kala kala, wanda in na tsaya zayyanowa, zan bata baki na ne.
Da isar su masu gadin gonan suka zo suka bude, kutsawa cikin lambun suka yi sai akayi parking din keken dokin a wajen ajje wa, aka bar dogaran suyi gadi, sai a lokacin su Yarima suka samu sukuni shida sulaiman daga su leqa nan sai su leqa can suna ɗan tadi jifa jifa, Sulaiman sai tsokanan shi yake na abubuwan da ya tsara lokacin da yake kulle na kyautar gida da kuma kudaden da yayi wa ahalin Hafsa, suna tsaye Sulaiman yace bari yaje ya samu babban mai gadin gidan gonan suyi magana ya fada masa me da me ake bukata, nan yabar Yarima Idriss a tsaye a gun yana karewa tsuntsaye kallo tare da lulawa duniyar tunani.

__________

Hajiya Hafsa na hango an fito daga gidan su Habibah, biye da ita Habiban ne da Jamila, suna tafiya suna ɗan tadi ita Hafsa tana bata labarin gidan sarki, ita kuma Habiba tana bata labarin an saka mata rana, Hafsa hadda ihun murnan ta, suna tsakiyan yadda zasu tsara abunsu ne, suka hango Zaliha a tafe, lokacin har sun yi nisa da tafiya, tsokanan Hafsa Zaliha ta fara, wai ta tafi yawon ta zubar da sunan wai masarauta, hakan da tace kuwa sai ya bata ran Hafsa suka kama dambe, suna tsakiyan dambe suka hango kura a tafe tana gudu, ga takunkumin da aka mata tana ta kokarin ɓalla wa, ƙafa mai Naci ban baki ba, nan suka ranci na kare har Zalihan, suka fada cikin wani babban gidan gona da suka gani a hanyan. Daga ta cikin gonan suka ga wani yabi kuran akan doki, shine suka samu daman kutsawa can ciki, a ranan tunda suke a rayuwar su basu taba ganin tashin hankali irin yau ba, kura fa? Yanzu kila da zancen wasu ake yi ba nasu ba. Saida suka gama maida numfashi kusan mintina har goma yasa suka dawo hankalin su, Ganin yanzu Zaliha ita kadai ce yasa suka mata taron dangi suka mata dukan tsiya banda Jamila da take basu hakuri akan su kyale ta kar su ji mata ciwo, su daga kai suka hango wani dogari na zuwa hannun sa dauke da dorina mai baki goma, nan da nan kowa yayi hanyarsa a cikin gonan suka bar Zaliha da dogari.

_____
Hafsa da ta ɗeba da gudu bata tsaya a ko ina ba sai cikin lambun ya'yan itatuwa, bata ankare ba taji ta fada akan abu har sun kusa zubewa kasa ma Allah ya takaita. Ta daga ido sama, sai taga Yarima ne, nan da nan jikin ta ya kama karkarwa sannan bata cika shi ba, hannun ta yaja suka kutsa cikin itatuwan gun da ɗan duhu gudun kar wani bafaden sa ya gansa ata nan ajin sa ya zube, gun kuwa harda kujeru a ajiye, zama yayi tare da zaunar da Hafsa itama.
Zaman nasu keda wuya hafsa ta harare shi tare da cewa "Barka dai, sannun mu"
Shikam mamaki ne ma ya cika shi ganin tsagwaron rashin kunyan Hafsa, wato sannun mu ma zata ce, tafi ƙarfin ta gaida shi kenan, lalle ma, kawai sai ya zuba mata ido.
Tsintar Muryar ta yayi tana cewa;
"Nasan tunanin da kake yi a ranka Allah ya baka nasara, sede nan ba masarauta bace, duk da nasan zaka iya sakawa a zaneni a nan dinma, sede wlh kapın a zaneni sai na cije ka, na dade ina so in cije ka Wallahi, idan na tashi cizon ka sai na raba fatar ka da jikin ka, kaji irin muguntan da kamin Nima" ta karashe tare da murkuda masu baki, hade da hararar sa.
Kallon toh ki ciza din ya mata
Ai kuwa ta kama damtsen hannun sa, ta sa hakori, ta gallaza masa wani uban cizo, inaga da shi ba namiji bane da sai ya suma dan kururuwa da zafi, sai da taga dama ta cika, shi kuwa ko gezau hakan da yayi ya matukar bata mamaki gashi gurin yayi bala'in ja dan har fatar shi saida ya ɗan fara ɗayewa.
"Kin huce"? Ya tsinci bakin shi da furta wa
"Ai wlh ban gama hucewa ba, duk sanda na hadu dakai sai na cije ka wlh, se dai kasa a daureni". Ta karashe tana murkuda masa baki, kuma akan idanun sa.

Let's meet in the next Chappy
Vote, read and comment
Love ya🤍

Fadrees 🖋️ 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now