24

69 4 1
                                    

İnnalillahi wa inna ilaihirraji'un
Duka falon ya dauka.
Dayan wasiƙan waziri ya bude sede shida Maimartaba ne kadai suka san meke kunshe a ciki. Kilishi har ranta ta so tasan meke cikin dayan, amma tasa a ranta ta zata tambaye Shugaba boka Kapoor, nan da nan kowa ya watse.
Yarima ya koma sashen sa, ya zauna yayi tagumi akan wani teburin shi dake dauke da su takardu, su allo da su tawada, da kuma pepopi. Tagumi yayi yana mai sake sake a ransa, shi har ga Allah daman ba son auren yar gidan Sarkin yake ba, sannan mutuwar ta, ta girgiza sa, saboda bai bata mutuwa ba, kuma yasan da bata mutu ba, da da ita zeyi rayuwar aure, sannan mutuwan matasa yana matukar girgiza mutane, ya jima yana jimami, kapın kuma ya tuno hajjaju makkatu shehiya Hansatu da abinda ta fada masa, lalle sai ya koya mata hankali, tsaya! Bari ma ya rubuta wasika ya bawa Sulaiman ya kai gidan gona, dan shi gobe baze iya fita ba, tunda ga abinda ya faru
Takadda ya dauka ya fara rubuta kamar wani abun arziki, sai kuma ya nannade takaddan ya dora tawada akai.
Yayi shigewar sa, uwar dakan sa ya kwanta, yana tunanin abinda ya wanzu dazu da rana a cikin gidan gona.

_____________
Kilishi ce durqushe a gaban shugaba, da shigowar ta aljanun cikin kogin nasa suka fara mata ihun nasaran da tayo musu bakiɗaya sai cewa suke "Eho Eho Eho Eho" a cikin wani irin sauti mai ban tsoro da firgitarwa.
Gama ihun su kenan Boka ya saki wata bahaguwar mummunan dariya.
Da muryar sa mai sauti uku uku, daya na mutum daya na zaki daya na aljanu ya kama magana
"Kinyo mana babban nasara da wannan sadaukarwar da kika kawo mana a cikin wannan matsafa tamu, daga yanzu har illa Masha Allah zamu dinga kashe matan da Yarima zai aura mu shanye jininsu, domin ko a cikin launukan jini, jinin sarakai daban yake. İdan aka ga yana ta kashe matan da zai aure zeyi bakin jini, domin farin jinin sa har yanzu gabagaba yake, sannan in ba ta hakan ba wahala ce kadai zai bamu, tunda ga hanya mafi sauki da inganci toh kinga sai mu bi ai, ita kuma baiwar sa har yanzu ana bincike a kanta da zaran an gama, za kiga aiki da cikawa.
Dayan wasiƙan da waziri bai karanta ba kuma, wayar tarho ce, Sarkin Adamawa ya basa shawarar da su siya tare, zaki iya tafiya".

Bude ido tayi, ta ganta a kan gadon ta, sai yanzu ta gane puzzle din boka, idan aka ga yarima yana kashe matan sa, kowa zeji tsoron ya basa auren yarsa, karshen ta ma a hana sa sarautar a baiwa daya daga cikin en tagwayen ta
Wannan kenan.
___
Mama Kulu ne ta kira yaron da yace ana sallama da Hafsa, tace "zonan Sa'idu ko dai baka ji da kyau bane, ka tabbata Hafsa aka ce maka kuwa"
Yaron da aka kira da Sa'idu kuwa yace, "Cewa yayi na san wata yarinya fara a gidan nan, sai ya siffanta min Hafsa shine nace masa Hafsa ce, shine yaban Kobo, sannan yace in aika ana sallama da ita" ya karashe da murmushi tuna sisin Kobon da aka basa
Mama Kulu bata daddara ba, tace toh ai Azima da Dije ma da hasken su, kawai Hafsan ta fisu haske ne"
Sa'idu ya sake cewa, "nidai Hafsa ya siffanta min"
Mama Lantana ce ta karbi zancen wannan karan, tace "waye ne shi da yace a masa sallama da Hafsan?"
Budan bakin Sa'idu sai yace "Wannan injin miyan ne, wanda ya saka yaransa suka gina gidan simintin nan" ya karashe tare da pointing din gidan simintin da ɗan yatsan sa
Da jin haka Mama Lantana tace "kaje kace tana zuwa"
Yana fita tace "ke Azima zo kije kila ke yake nema, injin miya kam ai Saide ke din kece kalar sa".
Mama Zainabu dai bata ce komai ba, suna a haka Azima ta fito an shafa hoda an ja gira, ga balbala kumatu, jambakin nan radau, tana taunar cingam tayi waje, can suka ga ta dawo ranta a mugun haɗe
Mamanta, Mama Lantana ce ta tambaye ta ko lpy ta ganta a haka, sai tace wai ko kallo ma bata ishe shi ba, shi cewa yayi Hafsa yake nema, nan da nan Dije tace "ba wata Hafsan da yake nema, Ni yake nema, kema ai kinsan mun fiki kyau kika fita, kuma bayan haka ai kinsan cewa kina da Saminun ki, wlh in baki yi a hankali ba se na fada wa Saminun abinda ya faru, sannan dama na jima ina son injiniyan nima amma shi ko kallo ban ishe sa ba, Yaya Lawan da shigowar sa kenan caa yayi, "ke Hafsa bawan Allah yazo gun ki ashe tun dazu yake jira shine baki fita ba, baki san cewa ba'a ma ya'yan babban gida haka ba?
Zaran mayafinta Hafsa tayi tayi waje. A cikin gida kuwa Mama Kulu ce take tambayan Lawan din "Kai Lawan kace injin miya ɗan babban gida ne? Toh waye babansa a garin nan?" Ta karashe tana dan hararansa, Lawan ne ya buɗi baki yace "Wallahi ɗan Hakimin garin nan ne, gashi yaron yana da hankali da sanin Yakamata Seda ya biyo ta waje na ma nace masa ze iya zuwa hira gun Hafsan, ya karashe tare da shigewa sashen sa, ya bar ko wacce tana saƙa da kullawa.

Hafsa kuwa ko da taje taga waye ne, sai ta samu kanta da gaishe shi. Amsawa yayi cikin sakin fuska, nan ya ɗan fara janta da hira, idan kaga Hafsa wlh cewa zakayi baka taba ganin mai hankali irin taba, tayi shiru abunta sai sussunnad da kai take, ji tayi ta ma samu mijin aure wlh ko dan ta kuntatawa su Azima da mamannin su.
Tarihin shi ya bata, akan shi dan Hakimin garin ne, sannan a Chadi yaje yayo karatun sa na injiniya, yanzu shi yake zane zanen gidajen mafi akasari na garin.
Nan suka yi bankwana da Hafsa ya miqa mata ledan da ya kawo mata, ya tafi, ranan gaɗan da ba'a fita ba a gidan kenan. Ya kawo mata takalma da turaruka, da su madara da su alawa, dayawa, har saida ta tsamma su Sadiqu
Da tunanin shi Hafsa tayi bacci, an manta da Yarima dan anga abun duniya.
___
Kapın safiya ko wane lungu da sako Seda labarin mutuwar wacce Yarima İdriss zai aura ya karade, ciki kuwa harda cikin gari, ana rade raden mutuwan ne da safe Murja ta saci hanya taje sashen Yarima, Allah ya so ta yana dakin shakatawar sa, har ƙasa ta durqusa ta gaida shi, ta ciro wasiqan ta basa hannun ta yana mai karkarwa, da kaman baze karba sai kuma ya mata nuni da ta ajiye a kan teburin sa, nan da na ta ajje tayi godiya kan ta fice cikin tsananin farin ciki. Fitar ta kuwa keda wuya sai ga Sulaiman, shi kuma ya dauki wasikun ya basa yace yau bazai samu daman fita ba.

Zuwa da rana su Hafsa suka iski labarin mutuwar a bakin wata makwafciyar su wanda mijin ta yake aiki a barga a cikin Masarauta. Dajin haka Hafsa ta fice sai unguwar gonan su Yarima, tana zuwa tayi sallama da masu gadin, zasu fara mata rashin mutunci itama ta bude baki suka fara cacan baki, suna cikin haka sai ga Sulaiman nan suka zube suka kwashi gaisuwa, tambayan meya paru yayi kapın suyi magana Hafsa ta, cafe "wai pah Maigida Suleiman daga Nazo karban sako wadannan suka dinga zagin ubana, hadda cewa wai sai sun sa an wulakanta ni a garin nan, shi Sulaiman baya san hayaniya da rashin gaskiya, hakan da ta fada ya bata masa rai yace sai ya hukunta su, su kuma ganin irin karyar da ta gama shararawa ne yasa suka kasa magana bakin su ya mutu, cewa yayi ta biyo shi, tana zuwa ya dakko wasikun ya bata, ya sake ja mata kunne yace kar ta sake tsayawa tana rigima da maza, Hafsa kuwa kamar ta Allah sai gyada kanta take kamar wata ƙadangaruwa, tana karba tazo fita ta musu gwaliyo hada danƙwalin su, ta saka gudu sai gida, da ta shigo layinsu kuwa ta kama yanga abinta. Da ta shiga gida Mama take tambayan ta daga ina, sai tace kawai ta ɗan zagaye unguwan ne. Ajiye wasikun tayi a kasan kayanta, sai dare yayi zata karanta, duk da haka tayi mamaki da taga wasikun nan, ta dauka wlh wasa yake da ya fada mata zancen wasiƙan.

Fita tayi tsakar gidan su, suka zauna ana hira, yanke shawara suka yi akan zasu je gidan yaya fati da anyi la'asar
Daga haka ko waccen su ta miqe, suka yi sallah suka çaba kwalliya dukda suna jin haushin Hafsa na samun injiniya da tayi.

Mu haɗe a na gaba
Fadrees 🖋️

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now