1

653 23 9
                                    

A shekara ta 1950 a watan Shawwal.

WANI GIDA ne mai karamin ƙofa, irin kofar katako dinnan kuma ginin ƙasa (Bricks) ne, gidan ba wani babban gida bane domin daga gani kaga gidan mai ɗan rufi asiri ne.
Da zarar ka bude kofar gidan kuwa zaka ci karo da zaure me dauke da dakuna biyu masu kallon juna (opposite), daki ɗaya na maigidan ne dayan kuma na samarin gidan. kana shigowa asalin cikin gidan kuwa da kwanuka da butoci da ledoji zaka fara cin karo.

Ɗaga kai na kuwa ke da wuya dakuna na hango a jere guda uku da yar rumfar (veranda) su a kowacce gaban dakin, gashi kuma ko wanne daki labulensa daban hakan ne ya tabbatar min gidan da kishiyoyi.

Ban tabbatar da hakan ba kuwa sai da naga wasu mata magidanta ɗaya na suyan ƙosai ɗayar kuma tana dafa wani abu kamar kunu daga ganin yawan shi za kasan na siyarwa ne, ata gurin da suke sana'ar tasu akayi musu ƙatuwar rumfa a matsayin madafa (kitchen), suna yi suna harare-hararen juna ga wani uban tarkace a gaban su.

Wani yaro wanda ba ze wuce shekara sha ukku ba na hango ya fito daga ɗaki na tsakiyan cikin ɗakunan, jikinsa ajike alamar yayi fitsarin kwance, da misalin karfe shida na safiya, ko kallon iyayensa da suke aiki beyi ba ballantana suyi tsammanin gaisuwa daga gare shi, yana hamma tare da rufe bakin sa da hannu ya nufa banɗaki ya shiga, se kuma ya fito bayan ya duba yaga babu ruwa a cikin butan banɗakin, fitowa yayi yana ɓata rai, se wani murza ido yake kamar sabon barawon da aka kama, ɗaga kansa keda wuya ya ga buta babba ata gefen da yake tsaye ɗaukan butan yayi, jin a cike da ruwa yayi murmushin jin dadi, daman beyi Asuba ba sannan ga ruwa Allah ya kawo a cikin buta, bari kawai yayi wanka sai yayi alola da sauran, se ya sa hannu ya dauka, ya juya kenan da niyyar sake shiga bandakin ya ji an kwala masa kira me cike da gargaɗi

"Sadiqu", karka sake ka taɓa mun ruwa wallahi ko kuma inci ubanka" juyar da kaina nayi ba zata na hango wata kyakkyawar budurwa da baza ta wuce shekara sha bakwai ba tana wani uban sauri tana zuwa ta buga masa dundu ta kwace butan daga hannun shi tayi shigewarta banɗakin ba tare da ta gaida masu girkin ba, itama daga ganin yanayin ta da kyar in tayi sallar asuban.

Mahaifiyarsa dake kan sana'ar ta ne ta miqe rai a ɓace ta kama masifa, sai caa take
"Bantan Ubancan, 'Ke Hafsa dan Uban ki meya miki kika masa wannan uban dundun, tsabar mugunta da rashin da'a? Ke ko kunya bakiji ba a gabana Ni mahaifiyar shi kike dukan sa?, mikewa ma tayi gaba-daya tabar suyan kosan ta kama zage zage, sai habaici take tayi takai minti goma tana girgiza kamar wanda aka sata rawar dole ita a dole an daki danta daidai lokacin da Hafsan ta fito daga banɗakin kenan tana murkuda baki cike da rashin kunya, tare da faɗin, "haa'a da waya aike shi ya taɓa min ruwana tsabar asara fitsarin kwance fa yayi, gardin yaro kamar wannan ace yana fitsa.." Rankwashin da tajine yasa ta yin shirun dole tare da juyawa

Ko ba'a fada ba tasan waye ne, 'haba mama me nayi da za'a rankwashe ni' Uwaki kikayi bana hana ki maida musu magana ba? Suma fa iyayen kine. Tukunna ma kin gaida su? "Çapdi jamm" ta sake fadi cike da faɗa aiko Maman ta sake buge mata bakin, aikuwa ta bata rai tana yatsina ta nufi hanyar ɗakin su ko gaida sun bata yin ba.

Tana shiga dakin nasu na karshe daga jerin ɗakunan ta hango kanwarta Jamila a kwance tayi ɗaɗɗaya da kafafu tana sharar bacci aiko ta hau bubbuga bayan ta.
"Ke Jamila ki mike ki je kiyi wanka kapin inyi Sallah kar muyi lattin makaranta kinji?"
Nan ko Jamilar ta mike ta fice a dakin da saurinta

Dayake butan da Sadiqun yayi niyyar dauka babba ne dashi take wanka wataran, to yanzun ma hakan ne ta kasance ta kwarfo ruwan ta daga rijiya ta ajiye a bakin banɗakin kafin taje ta dawo shine ta tarar da shi yana shirin dauka mata

Idar da Sallan ta yayi daidai da shigowan Jamilar dan se da tayi gewaye gewaye kapın tayi sallan, nan kuwa Jamilar ta hau shirya wa, da shike ita tun asubar tayi Sallan, Hafsan ne daman taki ta tashi tayi.
Nan da nan suka sanya kayan makarantar su sai gasu fes
Zama sukayi suna jiran Mama ta kawo musu kalacin su, suka jiyo Dije da Azima, wadanda suka kasance sa'annin Hafsan ne, ƴaƴan kishiyoyn Mama, suna cacar baki, akan kayan makarantar su.
_______
"Yanzu fi sabilillahi wannan yaron har yanzu yana fitsarin kwance? Caa nake ya dena ashe be dena ba
Aiko nine daidai kai dan ubanka
daga yau asuba tana yi zanzo in kwara maka ruwan sanyi, dan iskan yaro kawai" Yaya Lawan kenan (yayansu babba) da ya shigo cikin gidan, sai wani cika yake yana batsewa, kuma kullum idan ya zo sai ya maimaita abun da ya fada amma be taba aikatawa ba.

"Salamu alaikum"
Maigidan Malam Sule mai rini ne yayi sallama yana tuntube da kwanuka, daga ganin yanda yake sauri kamar ya fire sama zakasan mantuwa ce yayi aiko ana ganin shi akayi shiru shiko harkar gaban sa yayi, masu gaisuwa nayi masu yan noke noke nayi.
Yana gama abinda ya kawo sa ya fice a gidan.
Su Hafsa kuma Mama ne ta shigo musu da dumame, fitar da tayi dazu shine ta dumama musu. Zama sukayi sai sauri sauri suke suna ci duk dan kar suyi latti Malam Sidi ( Malamin horon su na makaranta) ya jibge su, sun fito kenan sukayi kiciɓus da su Dijen suna zage zage ahaka suka fito da misalin ƙarfe 9 suka kama tafiya hanyar makarantar tasu da take da ɗan nisa da gidan nasu

"Hafsa" Su Dukan su suka juya ganin mai kiran sunan Hafsan, aiko da gudu gudu ta ƙaraso
Kawar Hafsan ce Habibah, suna ɗan ɗasawa da itane saboda ita kadai take iya tolerating halayen Hafsan.

Habibah kece dayin latti yau? Kice yau Malam Sidi ya samu nama, Hafsa ta karashe tana dariyar mugunta, su dai su dije sai sana'ar suke wato ashar a haka su kaci gaba da tafiya

A gida kuma Baba ne ya sake shigowa yazo yace a kai masa abincin sa dakinsa, tare da yi musu nasiha akan tsafta domin da Mama tana sharewa duka tsakar gidan sukai ta bakar magana har da faɗan su akan cewa sai dai a raba kowa yana gyara sashensa, haka aka raba mama kullum tana kokarin ganin sun canza amma abu sai karuwa yake,
Sai ya zamto kawai Mama dakin ta da rumfar gaban dakin ta ne zaka ga tsaf tsaf, su Lantana kuwa tsabar ƙazanta idan suka wuce ta gefen ka harwani bashi bashi za ka ji suna yi
Wai su ahaka suke sana'ar ga shegen ƙazanta kamar me, Mama kam har mamakin masu siyan abunsu take ana suya ana fyace majina ko kaga ana tufar da yawu abun dai ba kyan gani.

_____________
Su Hafsa kuwa suna cikin tafiya suka ci karo da wani uban taro an hana kowa wucewa, gashi ba daman subi ta dayan hanyar zasu yi latti, Fadawa suka fara hangowa suna wucewa sai sukaga da mota a tsakiyar su, a hankali motar take tafiya, motar zamanin daa ce ana kiran ta da 'volkswagen' a turance, 'Hajiya ba ɗuwawu' a hausance.

Tsabar wulakanci dogarai har duka suke yi in suka ga an zo kusa da su, abun ka da mutanen da ba kowa bane yasan mota shiyasa aka taru ana ta kallo, su a zaton su Mai martaba ne ma yazo wucewa ashe Yarima ne
Su Hafsa kuma wani Uban latti sukayi har sunso su koma sai suka tuna da fitinar Malam Sidi, double case kenan aiko ba yanda suka iya haka suka jira tukunna suka tafi, Suna isa makarantar nasu kuwa suka tarar da me tsaron bakin kofa.

Yana ganin su ya kwashe da dariyar mugunta yace
"Lallai ma kuɗin nan zakuci Ubanku yau, yanzu wasu suka zo ba da jimawa ba kunga dukan da aka musu?

Hahaha Kuma albishirin ku Malam Sidi ya sayi sabon dorina mai baki shid.." ai bai kai ga gama magana ba sai ga wani jibgegen mutum sai hura hanci yake da ka ganshi ka ga basamude hannun sa rike da ƙatuwar dorina mai baki takwas
"Kuzo nan" shine abinda yace kafin Jamila ta saki fitsari

Aaaaaahh

Vote and

Comment and

Share

Fadrees cehh.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now