21

72 8 6
                                    

Yini sun lulluɓa zuwa kwanaki, kwanaki kuwa sukayi ta rikiɗa zuwa makwanni, makwanni kuma suma suka juye zuwa watanni , sede a cikin watannin akwai wata daya.
Yarima na hango ya fito daga sashen sa, shigar jikin sa kuwa riga ce da kuma wando mai zaiba, ruwan goro, yayi kyau abinsa, ya dora alkyabba ruwan kasa akai, takalmin nan nasa sai daukar ido yake. Gashi yasha rawani abinsa, sashen mahaifiyar sa ya nupa, bayan ya miqa mata gaisuwa ya wuce sashen Sarauniya Babba itama ya miqa mata gaisuwa budar bakin ta kuwa sai tace
"Ina zuwa Yarima"?
"Zan zagaya gari ne kamar yadda na saba" ya bata amsa Kamar baya san yin magana
Murmushin gefen baki sarauniya babba tayi, kapın tace "a dawo lapiya".
Mikewa Yarima yayi nan da nan ya kama hanyar fita daga cikin masarautar tare da hawa kan keken dokin sa, mai kalar ruwan sararin samaniya.
_____________________

Gidan Malam Sule me Rini a cikin kwanakin nan ya koma kamar dai yadda yake a baya, Hafsa ta zama shiru shiru ta rage fitina amma rashin kunya da dambace dambacen ta na nan musamman in an tsokane ta, dan sunsha yin cacan baki ita da matar yaya Lawan, dasu Dije sai mama ta sa baki take kyale wa, makwabta yan uwa da abokan arziki, ba wanda bai zo ya gaida ta ba, ta samu alheri sosai, musamman daga gidan mai unguwan su, dan su shiryuwar Hafsa gaba ta kai su, dan an dena dukan musu ƴaƴansu, hatta su garzali sai da suka zo suka taya yar uwarsu murna na dawowa tare da kawo mata tsaraba kala kala, fadin kalar tsaraban da Hafsa ta samu ma bata lokaci ne Malam Sule me Rini Seda yayi sati Uku kapın ya koma bakin aikin sa, ba tare da ya bude wannan jakunkunan da su Mama Lantana da Kulu suka kwallafawa rai ba, hakikanin gaskiya ransu sai da ya ɓaci da ya tafi, gashi makullin dakin nasa yana hannun Mama Zainabu. Shi kuma dalilin da ya sa yaqi bude jakan gani yake jakunkunan sunfi karfin su, sannan yana kyautata zaton za'a iya cewa su maida, to shi baya so ya taba a samu matsala.

Yau bayan an gama karin kumallo su Mama Kulu an gama sana'ar safe, su Azima kuwa an fice yawo, Mama ne ta kira Hafsa tace taje gidan mai unguwa ta musu godiya daga bisani sai ta wuce gidan su kawarta Habiba, tunda tun sanda ta dawo take ziryar zuwa gidan nasu.
_____________________

Fitar Yarima kuwa keda wuya sai na hango wadannan samarin da suka raka Hafsa har gida dinnan, sun taho garesa sun zube sun kwashi gaisuwa.
Kallon babban cikin su Yarima yayi yana jiran ƙarin bayani daga gare sa
"Allah ya ja da ran Yarima, mun miqa saqo kamar yadda aka umurta da muyi, saidai alamu sun nuna ba'a bude saqon ba tukunna, idan da an bude da wani maganan ake yi ba wannan ba".
Matashin ya karashe maganar yana mai sunkuyar da kansa kasa
Sallamar su Yarima yayi, ya kama hanyan zuwa unguwan su Hafsa

Sallama aka masa a kofar gidan mai unguwa yana zaune a cikin keken dokin bai ko fito ba dogarawan da suka masa rakiya sai filfita suke masa, Mai unguwa ko dajin wa ke sallama ya saba babbar rigar sa bai ko jima ba sai gashi ya fito a rikice, yana zuwa ya zube ya kwashi gaisuwa a gaban sa
Nan da nan yasa aka ma Yarima iso cikin dakin shakatawan sa, cike da ƙasaita da tsantar sarauta yarima yake taka kasan, Seda ya shiga dakin shakatawar mai unguwa ya zauna, sa'anan mai unguwa yasa aka kawo abubuwan taba baki, da ya natsa, sai ya fara koro bayani kamar haka
"Ina so ka nemi Malam Sule me Rini ka aika masa da kiran gaggawa yanzu "
Ko gama maganan sa beyi ba mai unguwa ya zari takalmin sa yaje kofar gidan su Hafsan da kansa, kasancewar layin su daya dama, sannan gida bakwai ne ma a tsakanin su.

Da ya rabza sallama sai yaga Hafsa da Jamila sun fito, daga gani sunyi shirin fita ne zuwa wani guri, da ganin sa har kasa suka tsugunna suka gaida shi, shi kuwa ganin Hafsa yace "ja'ira" a ransa.
Sadiqu suka gani ya fito shima, nan da nan shima ya gaida mai unguwa sai a lokacin su Hafsa sukayi ficewar su daman Mama gidan mai unguwan ta aike su wai Hafsa taje ta musu godiyan sakonnin da suka aiko mata da ta dawo, Sadiqu kuma mai unguwa ne ya aike shi yaje ya ƙira masa Malam Sule me Rini, sai sadiqun yace masa ai Malam Sule ya koma bakin kasuwancin shi, sai ya tambaye sa ko Lawan yana ciki, shine yace bari yaje ya dubo, ko da zuwan sa, sai ya iske baya nan, wai yaje kasan layin su, shi kuma mai unguwa baya so ya koma Yarima yaga kamar ya kasa ne sai ya aiki Sadiqun da yaje ya kira masa Lawan din da hanzari, shine yaje ya samu Lawan ya kira sa, da ya zo ya miqa gaisuwar sa ga mai unguwa sannan mai unguwa ya fada masa abinda ke tafe dashi, shine shi kuma yace bari yaje ya canza kaya suje gun Yariman, a ƙalla an dauki mintina talatin kan mai unguwa da Lawan suka koma gidan mai unguwa, suka iski Yarima bisa kafofin sa yayi mutuwan tsaye.

_________________

Hafsa ce suka zo shiga cikin gidan mai unguwa dogarai suka hana su, gida dai gashi nan babban gida ne mai dauke da zauruka har uku sun wuce zauruka biyu a na ukun da zai sada ka da cikin gidan taga su barau din a tsatsaye tayi tayi ta wuce suka ce ta koma, ai mutane dayawa sun zo ance su koma, Hafsa kuwa ranta ya ɓaci tace baza ta koma ba, Jamila sai jan hannun ta take tana fusgewa, daga hannu tayi ta shararawa barau mari, daman bata manta shi ba, shine dogarin da Yarima ya taba sawa ya zane ta da tana gidan sarki, sauran sai suka tsaya suna mamaki, a garin kallon mamakin da suka tsaya ne ita kuma ta janyo hannun Jamila suka fada a zaure na ukun, ganin haka sauran dogaren suka biyo su, Hafsa kuwa ta damqi hannun Jamila suka fada a cikin dakin shakatawan mai unguwa inda suka iske Yarima a zaune wani bafaden na masa filfita.
Zuciyoyin su ne suka buga a tare, Allah Sarki Yarima tun sanda Hafsa ta dawo gida da tunanin sa take kwana take tashi, idan lokacin cin abinsa yayi sai tace, ƙila Yarima yanzu haka yana cin abinci, ko tace ƙila ya gama, tafi yin tunanin sa idan dare yayi musamman taga su Mama sun yi bacci ita da Jamila, toh zata dauki matashin kanta ta rungume shi har sai bacci ya dauke ta, yanzu kuwa da take kallon sa nan take shima idon sa ya fada a cikin nata, aka fara kallon kallo. Shima gaskiya yayi missing nishadin da yake sha, idan ya sa ta aiki tana gunguni da mita, karan zubewar Jamila kasa ne ya dawo da hankalin su kowa ya janye idanunsa daga cikin na dan uwan sa.
Kwasar gaisuwa Jamila tayi, sai ya kasa ce mata komai kawai ya tsaya yana kallon ta, hakika tana matukar kama da Hafsa, gata itama kyakkyawa ce sosai, Hafsa kuma ta kasa motsawa, suna a haka ta jiyo alamun za'a shigo, shine ta damqi hannun Jamila suka yi waje suka fada a cikin gidan mai unguwan.

Su kuma dogarawan da suka biyo Hafsa ganin ta shige cikin dakin shakatawan ne yasa suka koma, domin sunsan dogarin dake ciki zai hukunta ta daidai gwargwado.
Su Hafsa kuwa suna fita suka je suka yi abinda ya kawo su, matan mai unguwa sai sa musu albarka suke, su kansu sunji dadin ganin ta haka, yaran su sun dena dawo musu gida da kuka da majina, dan Hafsa ba ruwan ta da yaran mai unguwa jibgansu take yi ba tausayi
Da suka fito, sai suka nupi hanyan gidan su Habibah.
Hafsa hadda ma dogarawa gwaliyo tare da zagin su


Mu game a shafi na gaba
A tabbata an bar min, comment.

Fadrees 🖋️ 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now