25

122 8 0
                                    

Suna gama shiri suka kama hanya sai unguwar da yaya fati take
A hanya su Dije Seda suka yi fada ita da Azima, dakyar Hafsa ta raba su, da suka je gidan yaya fati kuma suka dawo normal, Hafsa ne ta saci jiki dan taje gidan su Murja dan unguwa daya suke da yaya fati, da ta fita da tambaya ta gane gidan, ilai kuwa kowa sai zagin babar Murja yake wai azzaluma ce ta shanye mijin ta, sallama tayi taje ta zauna akan kujera, taji shiru ba'a amsa ba, hango wani rafkekiyar takunya tayi a cike da kunu akan wuta, juyawarta keda wuya kuma taga ƙullin ƙosai dayawa ga gishiri dayawa a ajiye a gefen, a take ta miqe ta dauki gishirin ta juye duka akan tukunyan kan wutan, ta debi mai da ta gani a gefe a cikin wani katon Samira ta juye shi shima a cikin kunun, daukan wani ludayi tayi, ta gauraya, shi kuma sukar din da Yakamata a zuba a kunun ta dauka ta juye a cikin ƙullin ƙosan, ta dibi ƙasa a ƙasa ta hada ta gauraya, gamawarta yayi daidai da fitowar wata makirar mata daga banɗaki, ganin abinda tayi yasa matan zambada ihu domin yau ta mutu, sana'ar ta da take dogaro dashi yau babu shi, fitowa wanda suke cikin dakin suka yi suna ashariya ganin abinda ya auku, ita kuma Hafsa ta sa gudu da iyakar karfin ta, tare da fadin "Na rama wa Murja" har tabar layin bata dena jin kururuwar matar ba, ita ko Hafsa ko a jikin ta, komawa gidan yaya fati tayi, kamar bata yi komai ba, suka ci gaba da hiran su ba sune suka bar gidan yaya fati ba, Seda aka kusa shiga mangariba, suna yin Sallah kuwa suka ci abinci, gamawar su keda wuya akayi isha, nan da nan kuwa suka yi ta, sai jin sallaman Sadiqu suka yi wai ana sallama da Hafsa, nan da nan kuwa Hafsa tayi waje su Mama Lantana suka bita da harara
Suna tsakiyan hiran su su Azima suka zo suka wuce gaɗa, bayan sun gama hira ya gama fada mata abinda yake so da wanda baya so, itama ta faffada masa, nan suka yi bankwana ya tafi, tare da ce mata gobe baze samu daman zuwa ba dan zeyi tafiya saboda haka ta saka shi a addu'a.
Nan da nan kuwa ya wuce, sai Hafsa bata shiga gida ba ta wuce wurin gaɗan itama, bayan sun gama wasannin su suna shirin tafiya, Saminu yasha gaban su, ya tsare Azima da ido wai sai ta fada masa uban me ya mata take shasshare sa, ita kuma tayi banza dashi, tunda taga injiniya taji ta tsane shi, ilai kuwa a gun suka yi baram baram, kowa ya watse, da suka dawo gida Dije ta bada labarin abinda ya faru, da mamakin su Mama Lantana bata tanka ba.

Hafsa ne tayi shirin kwanciya ta haye gadon mama, jira take su yi bacci ta dakko wasikun ta ta karanta, amma Mama taqi kwanciya, daga karshe ma ce mata tayi ta bata labarin injiniya, jin haka da Hafsa tayi seda tayi mamaki, yau Mama ne ke tambayan ta wani?
Nan kuwa ta saki baki ta fara zuba, "Mama injiniya yana da kyau, sede bekai Yarima ba" nan ta gane ashe subutar baki tayi, aikuwa ta doke bakin nata da kanta, ganin Mama bata ce komai ba yasa taci gaba, "Mama injiniya naga yana da hankali, da sanin Yakamata, sannan daga alama mamar sa zata so Ni, Ni dai Mama ko Baba ya dawo ki gaya masa Ni dai shi nake san aura" ta karashe, tana me kulle fuskan ta wai alamun kunya, da taga Mama bata tanka ba, sai ta leqa fuskan ta, se taga idon maman a rupe, ita dai sharewa tayi amma bata yadda mama tayi bacci ba.
Can da taji ba motsin komai sai ta tashi ta dakko fitila ta haska kasan kayan ta ta ciro wasiku
Tana budewa taga 'MURJANATU' a jiki da rubutun ajami, a take ta rungume wasiƙan hawaye na zubo mata, bude wasiƙan tayi ta fara karantawa kamar haka;

"Da sallama zan fara bisa addinin Musulunci
Yar uwa ta ya kike, ya gida, ya su Mama, ya Jamila, ya kowa da kowa, da fatan kowa yana cikin koshin lapiya
Hakika ina cikin matsanancin rashin ki, kullum sai nayi kuka idan na juya ban ganki ba, hakika kin zamto tamkar wani sashi ne a jiki na, ina tsananin kaunar ki Hafsa, na rasa ta yadda xanyi inyi magana dake shine na yanke shawaran in rubuta Miki wasika in roqi Yarima dan Darajar Allah ya sa akai miki, idan kinga sakon nan, ya sa an kawo Miki kenan, wanda ya nuna yana da kirki sosai, idan kin karanta ki rubuto min ki bada a kawo min kinji yar uwata?
Ubangiji Allah ya gama fuskokin mu, idan muna da daman gamuwar.
Taki ce har kullum
Masoyiyar ki kuma Aminiyarki
Murjanatu Sahabi.
Bissalam".

Nan da nan Hafsa ta fara kuka, sai da tayi me isarta kapın itama ta dakko takadda da tawada ta fara rubutu kamar haka itama cikin ajamin domin duk wasikun su cikin ajami suke yi.

"Assalamualaiki Murja yar uwata.
Bayan sallama da so da yarda
Hakika ban manta dake ba, kullum kina a cikin tunani na, in Sha Allah zan nema Miki hanyan kubuta daga cikin masarautar nan, ko kuma in roqi Yarima ya fito min dake sai ki dawo gidan mu da zama
Nayi matukar kewar ki, su Jamila suna gaida ki, sannan nayi saurayi wani injiniya yana sona sosai, na kusa aure kenan, amma sai kin fito zanyi auren Kinga sai amana tare ma, dazu naje gidan ku na rama miki muguntan da babar ki take Miki (nan ta zayyano mata komai sai ta kara da).
Ki cigaba da hakuri kinji masoyiya ta, in Allah ya yadda zan sama Miki mafita.
Masoyiyar ki mai matukar kaunar ki
Hafsatu Sule".
Wassalam.

Bayan ta naɗe wasikar Murja ta dakko na Yarima ta fara karantawa kamar haka;

"Sallama bisa tsarin addinin musulunci.

Ya rashin ji da rawar kai, da fatan kina lapiya
Ki gaida min mai kama dake ɗinnan, sannan ki gaida Mama

Ni ne Ubangidan ki
Yarima Idriss".

Dariya ne ya suɓuce ma Hafsa da ta gama karantawa, wai ya rashin ji da rawan kai, amma Yariman nan ya ma raina mata hankali, wai Ubangidan ta Allah ya sa Uban ta ne ma ba Ubangidan ta ba
Tawwada da alkalami ta dauka ta fara rubutu kamar haka

"Sallama a gare ka mummunan Yarima
Ya masarauta ya jiji da kai, da fatan kana lapiya, ka gaida su Fulani da Sarauniya Babba, rashin ji kuma sharri kamin, amma zan rama ne, yauwa, naji ance matar da zaka aura Allah ya mata rasuwa, toh Ubangiji Allah ya mata rahama, kayi hakuri, Allah zai baka wacce ta fita, yauwa mummunan Yarima ina neman alfarma, dan Allah akwai kawata Murja ka taimaka a sallame ta, daman kaine kayi silan zuwan ta garin naku, amma bata da laifi, in ta kama a maido da Ni ne ma na karba hakan.
Zan dakata daga haka, ka tabbata kana cin abinci kar rasuwan nan, ya hana ka sukuni,

Daga fara kyakkyawar budurwa mai hankali da sanin yakamata
Hafsatu Sule".
Bissalam.

Da gama rubutawa ta haɗa wanda ta rubuta yanzu ta ɗora a saman kayan ta cikin gwangwaron ta, shi kuma wadanda suka aiko mata ta ajiye a can kasan kayan nata, kamar da farko.
Nan da nan ta kwanta cike da tunanin Yarima, an manta da injiniya
Da asuba tayi Hafsa ƙin tashi tayi, Seda Mama ta watsa mata ruwa.
Tana gunguni ta tashi tayi sallahn, can zuwa rana tsaka ta miqe ta tafi gidan gonan nan, da taje bata samu Sulaiman ba, se ta bama shugaban masu gidan gonan, wani tsoho, ta bashi tace ya baiwa Yarima idan bai zo ba ya baiwa Sulaiman.

Se da aka kwana hudu kapın Sulaiman yazo gidan gonan, a cikin kwana hudun nan kuwa kullum sai Hafsa tazo ta tambaye mutumin yace mata basu zo ba.
Ranan da wasiƙan ya shiga hannun Yarima, bai karanta ba ya ajje akan sai yazo kwanciya, ya wuce fada ana masa neman gaggawa, yana zuwa yaji ashe sake bashi mata akayi har biyu ma wannan karan, yar ciroman Bauchi da yar sarkin Gombe, saboda ɓacin rai da wuri ya kwanta ranan, bacci kuwa yaqi ɗaukan sa, can ya tuno da wasiƙan Hafsa nan, ya fara karantawa, da ya gama saiga Yarima yana murmushi, lalle yarinyar nan bata ji, wato shine ma mummunan, duk sanda suka hadu sai tayi bayani ne, gaskiya tasan hanyan da zata bi ta sa mutum nishadi, beyi wata wata ba ya maida mata da amsa, a karshe hadda sa mata, "sannu fara kyakkyawar budurwa mai hankali da sanin Yakamata". Yakai minti goma yana jin nishadi.
Wanda ta rubuta wa Murja ya gani, sai yayi kaman ya karanta, ya fasa, can har yaje ya kwanta, ya sake tasowa ya dauko ya fara karantawa, ji yayi ransa ya matukar ɓaci, an gudu ba'a tsira ba kenan? Wanene wannan injiniyan? Badai wanda ya saka gini kwanaki ba, bari zai sake bincike a kansa.
Sai da ya kwana biyu sannan ya hadu da Murja ya mata alaman tazo ta karba, daman ta dade tana zuwa sashen nasa ko Allah ze sa ya bata wasika sai ranan Allah yayi

Da taje ta karanta ta dinga murmushi
Nan da nan ta tafi dashi makarantar su na bayi, ta maida mata da amsa, da washegari ta kai sashen Yarima shi kuma ya baiwa Sulaiman ya bata.
Haka Yarima suka ci gaba da exchanging wasiƙu shi da Hafsa, wataran hadda na murja ma. in ya karanta wasiƙan ta ya dinga dariya kenan, har aka zo aka saka ranan auren sa da yammata guda biyun. Tare da na Sulaiman da Gimbiya Bilkisu na Samira ne aka dan samu canjin lokaci.
Wannan kenan

Let's meet in the next chapter
Ghost readers, daku nake, kuyi following account din sannan dan Allah ku dinga voting da commenting, zaku iya sharing ma mutane pls.

Yours lovely,
Fadrees 🖋️ 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now