26

52 3 0
                                    

Yau Hafsa da zazzabi ta tashi sam ta rasa meke mata dadi, ko dan auren da taji ance za'a yi ma Yarima ne oho, toh ita meye nata ma a ciki ita da take da injiniya Kabir guda? Cikin en kwanakin nan da suka shige sau biyu ta hadu da Yarima a gidan gona, duk sauran a wasika suke magana, sannan duk sanda ta shiga gidan gonan, sai ta kawo ya'yan itatuwa, Mama har ta gaji da mata magana, daga karshe sa Jamila tayi ta bi bayan Hafsan inda ita kuma Jamilan tazo ta fada ma Mama, aiko mama har da mata dundu daga nan ta hana ta fita, ta sha satan hanya ta fita amma sai mama ta kama ta, daga karshe sai ta dangana, sai kuma in hira zata yi da injiniya, yau watan baba biyu da satika har biyu kenan bai dawo ba, amma yana aiko musu da aike da wasiku shiyasa basu daga hankalin su ba.

________

A Masarauta kuwa Fada ne a cike da mutane ana fadanci, wani dogari ne ya fado cikin fadan a firgice ko sallama baiyi ba ya zube a kasa yace, "Allah ya baka nasara, yanzu yanzu aka aiko Ni da inzo in sanar Allah ya yi ma yar gidan ciroma wanda Yarima İdriss zai aura rasuwa.
Nan take fada ta dau salati dan babu wanda bai kadu ba a gurin, daga masu sakin baki sai masu mutuwan zaune, ba'a gama jimami ba aka ji wayan tarho dake cikin fadan yayi kara, nan da nan magatakarda ya miqe tsaye yaje ya dauki wayan, "layin masarautar Gombe" ya furta kapın ya amsa kiran ya saka a hansfree,
"Barka da warhaka magatakarda, magatakardan masarautar Gombe ke magana, Mai Martaba Sarkin Gombe yace a sanar da Mai Martaba Sarkin Bauchi kan Allah yayi wa yarsa wadda Yarima Mai jiran gado na Bauchi zai aura rasuwa, yanzu yanzu. Jana'iza da yamma".
Gaba daya sai fada ta kaure da hayaniya, salati kam har bata ƙirguwa.

________
Kusan karfe sha biyu Hafsa ta fito cikin gida ta zauna Kamar daga sama suka ga Dije ta fado gida, daga ganin bakin ta zaka san gulma ta kunso, ilai kuwa tana shigowa tsakiyar gidan nasu tace, "yanzu naji wani labari daga fada, ance matan da Yarima zai aura dukkan sun mutu yau", nan da nan pah gida ya kaure, kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa, daga Mama Lantana tace gwanda ma tun yaushe yakamata a masa aure anki, seda lokacin sa ya wuce, sai Mama Kulu tace shi yake kashe su kawai.
Ashe ba'a gidan nasu bane kaɗai ake ta jimamin ashe duka garin ne ya dauka, wasu cewa ma suke shanye jinin su yake yayi tsafi dashi, da abubuwa dai kala kala marasa dadin ji.
Ai nan da nan Hafsa taji zazzaɓin nata ya ware, da gudu tayi hanyan waje sai gidan gona, tana zuwa ta tarar bai kawo mata wasika ba, daman ita ta bada last, nan ta dawo gida gwiwan ta a sake, tana kwanciya kuwa zazzaɓin ya sake lullubeta, tunanin Yarima ta fara yi, tasan yanzu haka yana cikin tashin hankali, ga yanzu maganan da mutane suke tayi akansa, har sun manta alherin da ya musu, dakyar baccin wahala ya kwashe ta. Ba ita ta tashi ba sai yamma, haka tayi wunin ranar sukuku, da injiniya yazo ma bata samu daman fita ba.

_______
Bayan jana'izar yar ciroma, aka wuce Gombe akaje akayi na yar sakin kana aka dawo, rana na bakwai, babban malamin garin Bauchi yace ya bada auren yarsa ma Yarima İdriss. Idan ya'yan wayancan basa addu'a toh shi tashi tana yi, sannan shima zai dinga mata, aka saka rana daidai da na su Sulaiman, ya kama wata daya kenan, duk da haka mutane sai maganganu ake akan matan da Yarima zai aura.

Fulani mahaifiyar sa tafi kowa shiga tashin hankali, kusan wuni take tana kuka da tausayin danta, da cewa take natural death ne amma yanzu ta fara tantama, yanzu ta tabbata wani ne yake san ganin bayan Yarima shi yasa yake masa haka, sarauniya babba da kanta taje sashen nata tana ta rarrashin ta har ta samu kanta.

Yarima kam ba'a magana, shi baima san
Me yakamata yayi ba, Sulaiman ne ya raka shi sashen sa ya dinga tausar sa har Allah ya sa ya kwantar da hankalinsa dan wannan babban al'amari ne. Samira hadda kukan ta ita da Bilkisu.
Yanzu dai sun bar wa Allah komai suna jiran suga kuma ko yar Malam zata mutu ne eh ko a'a.
Wannan kenan.
___________

Kilishi ce durqushe cikin kogon boka Kapoor ta rabga masa kwanciya, da sunan girmamawa, bayan ta gama zayyano masa godiya, tana so ta masa tambaya amma ta rasa ta yadda zata fara, shi kuma da yake yasan tambayan me zata masa sai ya bata amsa kawai
"Muna ta kashe masa mata, kenan daman ƙaddaran sa ce ba zai yi aure ba?, ya maimaita mata tambayar ta a fili. Ɗaga kai tayi ta kalli sashen da yake, dan bata isa ta haɗa ido da shi ba, gudun kar ta rasa ranta
"Duk matan da zai aura sai sun mutu, sannan ƙaddarar sa ta tabbata din kenan, Indai har nine boka Kapoor toh ba shi ba aure har duniya ta naɗe". Ya karashe yana dariyar mugunta, itama kanta dariyar muguntan Kilishi ta sake, nan da nan ta masa godiya ta bace.

Kishingida tayi tana ta murnar abinda yake faruwa da Fulani, ko ba komai tasan dai yanzu an kusa shafe matsayin sa na Yarima Mai jiran gado, a bawa danta,  gaskiya taji dadi. Sannan tasan idan yar malamin nan ta mutu ba wanda zai sake basa aure, idan taga dama ma, haɗa husuma zata yi da masarautar nan da kuma masarautun da aka kashe musu yara.

____
Da Hafsa taji ance za'a masa aure da yar liman kuma yanzu har saura sati daya ba abinda ya faru, sai ta kwantar da hankalinta, a lokacin ne taje gidan gona ta amso wasikar sa, da ta dawo ta karanta, ta sake rubuta masa wani ta kai.

Yau saura kwana biyar ayi auren yarima da Sulaiman, tun ana saura kwana 15 aka fara su raye raye, kade kade da kuma bushe bushe. An gayyaci masarautu da dama kuma duk sun amsa gayyatar, hakika an sha wasanni daban daban. Kuma tun a lokacin aka saka amare a lalle

____
Yau ne ta kama ranar juma'a, ranar daurin auren yarima da Sayyada, yar gidan Malam, sai kuma Sulaiman da amaryar sa Gimbiya Bilkisu.
Bayan an hallara a cikin masallacin fadan ana shirin fara daura aure wani dogari ya shigo ya zube a ƙasa yana haki cikin tsananin tsoron abinda zai fada,
"An aiko Ni ranka ya dade daga gidan Liman akan in zo in sanar Allah yayi wa yarsa Sayyada rasuwa yanzun nan, nan da nan masallaci ya harzike, sai a lokacin aka lura ashe Liman baya cikin masallacin.
Yarima ne yayi mutuwar zaune, gaba-daya ya kasa motsi seda Sulaiman ya jijjiga ga, zuciyar Sarki Sulaiman saida ta buga tsabar firgici, waziri ma Seda ya tsorata, salati aka dinga sawa a fadan ana ta sallallami.
Sarkin fada ne ya tsawatar akan kowa yayi tsit, nan da nan kuwa fada tayi tsit, shi waziri tunanin da yake da yana da ƴa a yanzu zai bawa Yarima ita a daura musu aure, sede yarsa daya ce, kuma an mata baiko, nan da nan sarki da manyan fada suka shige daga ciki aka bar jama'a a cikin masallaci an yi tsit, kamar wanda mutuwa tazo ta gifta.

Galadima ne yayi magana kamar haka, "Hakika wannan al'amari ya daure min kai, menene dalilin da ya sa matan da Yarima zai aura suke mutuwa"
Waziri ne ya karbi zancen da fadin "Hakikanin gaskiya nima abun yana daure min kai, amma yanzu ba wannan bane a gaban mu, mafita Yakamata mu nema masa"
Ciroma ne yace "Wannan gaskiya ne Waziri, mafita yakamata mu nema, dole mu sake sa ma ma Yarima mata ya aura a yanzu yanzun nan, sai mugu idan an daura mai zai faru, Ni yanzu misali da ina da wata yar na rantse yanzu yanzu za'a daura mata aure da Yarima" ya karashe Muryar sa cikin yanayin damuwa
Mai Martaba kasa cewa komai yayi, idanun sa seda suka cika da hawaye, ashe daman mabiyansa suna san shi haka?.
Tsintar Muryar Waziri yayi yace "toh kawai muje a daura masa da yar uwarsa Samira tunda dai yanzu wa zai sake bada yarsa"?
Galadima ne yace "akwai alƙawarin aure tsakanin yarka da masarautar Borno, sbd haka wanin mu ne zai bada yarsa".
Nan da nan ido ya rena fata, falaƙi da wambai da garkuwa kowa yana da ya'ya mata amma yana tsoron badawa.

Afuwa ranka ya dade, mai unguwar wunti yana neman iso, da kamar su waziri zasu ce ya koma suna muhimmiyar tattaunawa sai kawai suka ce ya shigo, shigowa mai unguwa yayi tare da Malam Sule Mai Rini, suna shiga suka zube suka kwashi gaisuwa, malam sule mai rini ne yayi maganar da ta girgiza su dukkan su.

"Ni Malam Sule Mai Rini na bada ƴata ma Yarima İdriss, halak malak, idan an yadda da hakan, na amince yanzu yanzu aje a daura musu aure.

Fadrees 🖋️ 🖋️ 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now