18

99 6 2
                                    

Kilishi ce ranta yayi mugun ɓaci, ita sam ba haka ta so ba, ta so a kwace matsayin sa na Yarima Mai jiran gado a bawa daya daga cikin ya'yan ta, amma hakarta be cimma ruwa ba, dole se ta koma wajen Shugaba, babu yanda za'a yi tabar ahalin nan a haka, dukda tana jin haushin cewa yaran nata suma jinin Mai Martaba ne, amma dai ai ance da babu gwara ba dadi kuma ko ba komai itama ai jinin ta ne, kuma sai yadda ta so tayi da su.

Can dai ranta a hade tace tana da magana
Waziri yace an bata dama
Se tace "İna mai neman alfarmar da ayi ma Yarima sassauci ba dan halinsa ba, sannan ba wai na fada hakan bane dan a tozarta shi, na fada hakan ne dan ayi masa gyara, domin Yarima tamkar ɗa yake a guri na, soyayyar da nake nuna masa ko mahaifiyar sa saidai hakan, na gode Mai Martaba".

Ran Hayatu da Shamsu sai da ya ɓaci jin irin abinda mahaifiyar su ta jawo, abinda tayi wa dan uwansu sam basu ji dadi ba, sannan shi Hayatu shima ai abin ya shafe shi tunda shima ai yace yana san ta, amma da aka tashi aka rufe nasa sai na Yariman da aka fadi

Hayatu ne yace yana da magana, Kilishi wani irin mugun kallo take aika masa, daman tana kule dashi kan labarin da taji akan wai yana san baiwar Yarima, yanzu gashi zai sake kwapsa mata, ita ba abin ta hana shi magana ba, kar ma a zarge ta, shi ko Hayatu yaqi hada ido da ita kar ma kwarin gwiwar sa ta karye.
Waziri ne ya basa daman magana.

Duk abunnan da ake Fulani Hauwaó hawaye take zubar wa ita da Bilkisu, Samira kuwa cewa take in ta hadu da baiwar se na duniya yapı ta jin dadi wlh

Sulaiman kuwa da sarauniya babba idanu kawai suka zuba, Mai Martaba kuwa ba'a gane expression nasa shi kuma waziri idanun sa tausayin Yarima ne fill a kwance. Shi kuwa uban gayyar ko ajikin sa, hasali ma shi ya gaji da zaman da ake, ya matsu ya koma yaga halin da Hafsa take ciki, sannan in ya tuna ance zata bar masarautar se yaji hankalin sa na matukar tashi, gaskiya yana san baiwar shi ta cigaba da masa bauta, shi bai damu da rashin jin nata ba ma.

Muryar Hayatu akaji yana cewa
"Allah ya baka nasara, idan akwai wani mai laifi toh ba kowa bane, face ni, domin nine na fara tada harzomar nan, dan nine nace ina son ta, shi Yarima ba sonta yake ba ma kawai yana hakan ne saboda aƙidar sa na baya san wani ya mallaki abun sa kuma ko tambayar sa ayi gashi nan zai maimaita abinda nace ne, sannan ko a yanzu ina mai neman iznin Mai Martaba da ya bani dama in nemi auren ta, domin....." Kasa ƙarasawa yayi sbd kallon gargadin da Kilishi take jifan shi da shi idon ta kaman ya fado kasa saboda harara gashi nan yayi jazur dashi sosai, ita ji tayi ba'a taɓa tozarta ta irin na yau ba, da Yarima ne ya fadi haka sai tafi kowa jin dadi, amma jin hakan a bakin gudan jinin ta seda ta girgiza, duk da taji labari a wajen wata amintacciyar baiwar ta bata yadda ba, dan saida ta sa aka hukunta baiwar, yau gashi nan ya gama ci mata mutunci a gaban makiyan ta, babu wanda yapi bata haushi kamar waziri, murmushi ta gani kwance akan fuskar shi wanda ta tabbata ita ba alheri bane a gurin ta, wlh ta tsani wazirin nan, ita wallahi bata ƙi ya dena numfashi ba shida Yariman, ta tsane su wlh tsana mafi muni
Takai sunayen su gun shugaban ta Boka Kapoor, amma komai yaqi aiki a kansu, shiyasa jiya da taje gun shugaban ya bata shawaran tayi da tunanin ta, amma dole zata koma yau, dan ta bada sunan baiwar.

Muryar waziri taji yana magana kamar haka "Za'a sake bincike game da abinda ka fada Yarima Hayatu, domin kazo da abun dubawa, idon babu mai magana kowa zai iya watsewa, hukuncin Yarima Mai jiran gado zai fara daga yanzu".
Nan da kowa ya miqe ya fara fita daya bayan daya.
Aka bar Mai Martaba da Waziri da Sarauniya Babba dan su tattauna.
________________

Kilishi tana shiga sashen ta ta kulle nan ta nan ta dakko turaren ta na tsafi ta turara sai gata a kogon boka Kapoor. Sujjada ta fara masa kapın ya saki wata dariya mai bala'in tsoratarwa can kuma da ya gama shan kamshin sa yace mata "kije bukatar ki tabbatacciya ce" kapın ma ta masa magana taga har ta dawo dakin ta. Ranan kwanan baƙin ciki tayi farin cikin ta daya shugaban ta ya mata alkawarin biyan buƙatar ta.

_____________

Samira kuwa da suka fito ta kama hannun Bilkisu suka ɗan ja gefe, nan suka maida abinda ya faru, Samira tasha alwashin kapın baiwar ta tafi gobe sai ta sa an canza mata kamannin ta, ita kuma Bilkisu cewa tayi "Kawai ki gyale ta Samira, meye amfanin duba bayan hari, gobe in tabar masarautar nan fa har abada baza ta sake dawowa ba".
Budan bakin Samira sai cewa tayi "wane irin baza ta sake dawowa ba? Yarinyar da kika ji Yarima Hayatu yana cewa zai aure ta? Toh wai ma, me take da shi ne da suka rikice haka ne? Ko dai kyau gare ta kamar aljana, kodai asiri ta musu ne bamu sani ba"?.
Bilkisu ne tace "sai Allah, kedai kawai kizo mu wuce ita ta sani". Nan taja hannun Samira suka tafi ba dan ta so hakan ba.

_________________

Shamsu da Hayatu kuwa bayan fitar su sashen su suka wuce, Shamsu se masifa yake wa Hayatu akan meyasa shi baya daukan shawara "kai Hayatu banda rashin hankali ina kai ina baiwa, baiwar ma ta Yarima? Last munyi magana dakai nace ka cire ta a ranka, amma ka ƙeƙashe ka ƙi, yanzu tsabar rashin hankali har da fadin kana san ta a gaban Maimartaba, kai a zaton ka hakan da kayi daidai ne? Sannan Umma baza ta taba yadda da hakan ba, wai shin ko dai asiri baiwar nan ta maka ne nikam"? Ya karashe maganar sa yana zama akan gado tare da yin tagumi.
Hayatu ne yazo kusa da shi ya dora kan sa akan kafadar Shamsu yayi shiru sai can yace
"Ka fahimce Ni mana Shamsu, idan kai baka bani goyon baya ba waye zai bani? Kap duniyar nan bani da wanda ya kai ka, sannan Kai kanka ka gani, Allah ne ya dora min son ta, ba yin kaina bane, idan akwai wanda bai damu da sha'anin mata ko wani abu ba, toh nine, nidai ka bani goyon baya, in mallake ta, sannan Umma tana san abinda muke so itama zan fahimtar da ita, kuma Ni ba wanda ya min asiri, soyayya ce kawai daga Allah" ya karashe yana mai ajiyar zuciya.

Shamsu ne ya nisa kapın yace "idan Yarima bai Amince ba fa"?
Sai Hayatu yace "ai shi ba sonta yake ba kawai dai aƙidar sa ce, sannan shima zan fahimtar da shi, kaima sai ka taya Ni fahimtar da shi din".
Shamsu sai ya sauke ajiyar zuciya yayi masa tambayar da ya girgiza shi "idan kuma Yarima son ta yake kuma yana da niyyar auren ta fa kawai dai bai fahimta bane?"
Hayatu shiru yayi ya qurawa Shamsu idanu baya ko kiftawa.

_________________

A bangaren Yarima kuwa, shida Suleiman da masu take musu baya suka wuce sashen Yariman. Suna shiga suka tarar da Hafsa har yanzu a kwance take a inda ya ajiye ta koh motsi bata yi.
Ruwa yaje ya dakko ya watsa mata ta tashi a firgice, zata yi ihu ya daka mata tsawa, har se da ta firgita, da Sulaiman yaga haka nan ya dafa kafadar sa alamun ya sassauta.

Mu haɗe a shafi na gaba

Share
Vote
Comment and
Read.

Fadrees 🖋️🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now