Bayan wata ɗaya, wato watan haihuwan Hafsa ya kama kenan, daman tun da ta samu lapiya sarauniya babba ta kora su daga sashen ta, Sede ganin yanzu tana watan aihuwa yasa sarauniya babbar cema Yarima akan Hafsa ta dawo sashen ta shi kuwa gogan yayi kunnen uwar shegu da ita.
Zaune Hafsa take, tana me rubuta wasika, yawancin kwanakin nan zakaga tana yawan rubuta wasiqu musamman ma idan Yarima baya nan ya tafi fada, buɗe wani wasiqa tayi taga daga Jamila ne, karantawa tayi tana murmushin jindadi kamin ta maida mata amsa.
Gama rubutawan ta kenan ta afka duniyar tunanin yariman ta, daga cewa zeje ya dawo ta ji shi shiru, zasu haɗu ne ai, ta ɗan rufe idon ta kenan se taji kaman wani abu ya soke ta a ƙahon zucin ta, ji tayi ya fara mata zafi, salati ta fara saki, nan da na ta fadi sumammiya dan zafin ya zarce wa lissafin ta.
Can bayan kamar awa biyar Yarima ya shigo sashen da sallama bisa bakin sa, a kwance yaga Hafsa kamar ma bata numfashi, karasowa yayi gunta, ilai kuwa kwance take jini yana zuba daga hancin ta, besan sanda ya sumgume ta yayi waje ba sai dakin jinyar Masarautar.
Zuwai ce ta fara duba ta da gaggawa, bayan tace ya tsaya daga waje, dakyar ta samu jinin ya ɗan tsaya, fitowa tayi tazo gun da yake, tace masa
"Allah ya baka nasara, nidai a binciken da nayi na kasa gano komai, dan ba nakuda take ba, ina roqon alfarmar da a sake zuwa a kawo wannan me maganin in ba haka ba, ina mai tsoron rayuwar ta yana cikin matsala, dan idan nakuda ya kama ta baza ta iya aihuwa ba, karshen ta zata iya rasa ɗan cikin ta ne".
Da jin haka Yarima ya fice zuwa sashen Sulaiman, tun kafin ma ya isa labarin rashin lafiyar Hafsa ya karade ko ina, koda ya isa sashen Sulaiman sai be same sa ba, dogaran da suke gadin sashen ne suka ce masa yana sashen sarauniya babba, can kuwa ya wuce da sassarfa, yana isa ya hango su suna tahowa da sauri hadda sarauniya babba, daga alamu inda ya fito zasuje, suna ganin sa suka karaso inda yake, tambayan Sulaiman yayi bawan sa Hamisu, ba'a jima ba Sega Hamisu, yana zuwa aka saka su shirin sake zuwa ƙasar Yobe, kwana ɗaya da rabi ya kaisu Yobe garin Nangere inda suka je basu samu Malam na bakin rafi ba, wai yayi doguwar tafiya ze kai mako huɗu ko ma fiye da haka kapın ya dawo, da sakewar jiki suka kamo hanyan dawowa, suka sanar da su Yarima abinda ake ciki, daga nan fa hankula ya sake dunguma ya tashi, nan da nan kuwa masarautar Bauchi ta dinga aika wasiqu zuwa Masarautu daban daban neman masu magani amma a banza, dan ciwon Hafsa sake gaba gaba ma yake, gashi ana tsaka da haka ne ta kama naquda, fadin irin kalar azabar da take sha ma bata lokaci ne, sannan har a lokacin hannun ta na damqe Kyallen canBayan mako uku, zan iya cewa Hafsa ta gama galabaita, idan har kai musulmin kwarai ne dole ka tausaya mata, hatta da makiyin ta nasan in yaga kalar azabar da take sha dole ya tausaya mata, an sake aikawa kasar Yobe har yanzu Malam na bakin rafi bai dawo ba, sannan har lokacin kyallen na hannun ta, dakyar yau da siɗin goshi zafin naquda yasa ta saki kyallen shi kuma Yarima sai ya ɗauka a hannunsa yana jujjuyawa, fita yayi ya samu Sulaiman ya nuna masa, se yace masa ai wannan kyallen ya kalla irin sa a cikin kayan wannan bawan da suka saka ya binciki Fulani, shima har yariman yace ya tuna.
Ai kuwa Sulaiman na fita ya aika a dubo kayan bawan, anje aka ga kaya a ƙone, dan ko toka ba'a samo ba, sannan babu kyalle babu dalilin ɓatarsa, ganin haka Yarima ya ajiye na gunsa dan yayi bincike akai.Bayan mako ɗaya, lokacin Hafsa ta fige ta matuqar ramewa da galabaita, lokacin haihuwar ta har ya wuce amma shiru ba labari, sake aikawa akayi Garin Malam na bakin rafi lokacin duk masu bada maganin gargajiyan kasashe daban daban sunzo sun gwada amma Sede abu ya lafa, bayan kwana biyu kuma ciwo ya sake tashi.
Duk sanda Hafsa ta dawo hayyacin ta zaka ganta tana kuka, Yarima kuma ya dinga rarrashin ta kenan dan baya barin gefen ta, duk laifin kan sa yake gani, da be tafi ya barta ba, da ai ƙila yanzu tana lafiya.
Bayan wadanda aka aika Yobe sun dawo, se suka sanar da basu same sa ba still sede ance musu malam na bakin rafi kwana hudu ze kara ya dawo, Sulaiman ne yace su koma in yaso su dawo tare da malam din.4days later.
Hafsa ne aka samu ta ɗan yi bacci, yau kwanan ta biyu kenan bata farka ba, da farko da aka ga ta samu hutawa kowa dadi ya dinga ji, har Maman ta da Jamila sun dawo masarautar dan su suke jinyar nata, koda aka ga kwana biyu kenan bata farka ba hankula ya tashi, Maman tane akan ta Yarima ya shigo ya zauna can da yaga dai baccin take sai yayi miqewar sa yaje dakin sa ya dauko kyallen nan ya bude da kyau, shi be gane meye a jiki ba, koda ya fito ze koma dakin hafsan se yaga Sulaiman da Bilkisu a ciki, ido ya ma Sulaiman akan suyi waje, dakin shakatawa suka zo suka tsaya Bilkisu kuma ta shige cikin ɗakin, Yarima ne yake ce masa ya kalla kamar akwai rubutu a jikin kyallen, matsowa Sulaiman yayi suka kama karantawa tare, nan da nan suka gansu a cikin kogon boka Kapoor, abinda basu sani ba Malam na bakin rafi har ya kusa isowa cikin masarautar domin dasu Hamisu suka je sun same sa ya dawo sai suka taho tare kawai, shima beyi wani ja'in ja ba ya biyo su.Koda ganin su a kogo me matsanancin duhu sai abun ya basu mamaki, daga karanta abu kawai sai su gansu anan?, kutsawa ciki suka fara yi, Kogo ne me girman gaske, tafiyar dawakai suka fara ji, sai kuma suka yo gamo da wani rapkeken zaki sai gurnani yake, fadin Irin tashin hankalin da suka shiga ma ɓata lokaci ne, kansu yayo su kuma suka tsaya, take kuma suka ga ya ɓace, da suka yi gaba suka dinga cin karo dasu damisa ne, kura ce da su Dila, duk dai aljanune suke shigen su da niyar su tsorata su, Sede abu daya ne, duk da sun tsorata a zuciyar su, se basu nuna hakan ba a fili, da kuwa sun nuna da sun rasa rayukansu domin aljanun tsoro suke so su gani a idon mutum dan su cimma mutumin.
Tafiya suka cigaba dayi suka hango haske suka apka gun hasken, ganin saniya suka yi da kan agwagwa, alade da kan mutum, Mami water a siffar maza, duk sharewa suka yi suka kutsa kai suka ci gaba da tafiya, suma shigowa gun hasken suka ga wata halitta a zukunne a gaban wani wargajejen halitta bisa wata kujera da akayi wa ado da kan zaki da kuma kan damisa na gaske, masu rai kuma, ƙafar Sulaiman ne ta kama rawa, zuciyar Yarima kuwa bugawa take fat fat, shidai in har zai sama ma Hafsa magani ya yadda ya rasa ransa.
Magana suka jiyo halittar dake durqushe nayi
"Ya kai shugaba, meyasa yarinyar nan bata mutu bane gashi yau watan cikin ta har goma, kodai an fasa daukar fansar ne? Kodai maganin da aljani Gopal ya kawo ba ingantacce bane, na rantse har da girman tsafin duk sanda na koma ina ganin ta da rai zuciyata baki take yi, sannan maganin da akace daga an dasa mata shi zata fadi ta mutu yau wata daya ake nema da dasa mata shi"Dariya ya saki da murya uku uku yace
"Da badan addu'ar wani wawan malami wai shi Malam na bakin rafi ba da ta dade da ziyartan lahira, amma ina so ki sani na rantse da tsafin kakanni na baza ta tashi da rai ba, saboda wannan baƙin mutumin ne ai da ba haka ba, sannan shima bazan barshi da rai ba, Ku kuma kun kawo kanku halaka da kafafun ku, daman dan ku ake yin komai"
Ya karashe da razananniyar dariya yana me kallon su Yarima, juyawa halittar tayi wa zasu gani in ba Kilishi ba, sai a lokacin ƙafafun Yarima suka fara rawa.Ɗaga allon sihirin sa yayi, da niyyar ya kashe su Yarima sai yaga abun baya motsi, wai ya ɗaga kanshi dan yaga wanene ya masa wannan katoɓarar se yaga Malam na bakin rafi a tsaye a gaban sa cikin ɓacin rai.
FADREES 🖋️ 🖋️ 🖋️ Ƴar Mutan Yobe.
YOU ARE READING
YARİMAN HAFSA
Historical FictionA 1950's Love Story Labarin Rayuwar Yarima Idriss, ɗan Sarkin Bauchi, tare da wata fitsararriyar yarinya me suna Hafsa. Ku biyo domin ku ji yadda zata ƙaya Share please. Fadrees_20