23

64 4 0
                                    

Shirin miqewa Hafsa tayi, taji ya riqe mata kafada
Zata yi magana taji yace mata "Duk sanda kika zo gonan nan, ki dinga zuwa kina duba Ni, idan bana nan, ki rubuta wasika ki bada a bani haka aka san bawan kwarai da yi ma uban gidan sa."
"Çapdi jam, meyasa zan sake dawowa gonan nan ma, sannan meyasa zan ajje maka wasika, a garin ajje wasika inje a hallaka ni ko en uwana? Sannan ma nipa duk duniya ba wanda naqi jinin sa kamar kai, tun sanda kasa aka kaini masarautar ku na riqe ka a zuciya, yanzu so nake insan mai zan maka ma da zan huce haushin ka da nake ji"
Ita kanta tsintar muryar ta tayi ta furta haka, Wayyo Allahnta, idan ma raga mata yake yau kam zeci ubanta ne, wayyoooo ta shigan gaɗa yau kam, ai nan da nan ta zube a kasa wai tana neman afuwa.
Shi kuma wlh mamakin kansa ma yayi, da ya tsaya wai yake hira da baiwarsa, baiwar sa fa fisabilillah, shiyasa ma ta samu daman raina shin. Sannan ma ya kasa mata komai
Tsintar kansa yayi da ɗago ta, tare da mata rada a kunne kamar haka "Nima zan dinga rubuta Miki wasikan, idan yaso duk sanda kika karba, sai ki mayar da amsar ki, kuma kin manta kince duk sanda muka hadu zaki cijeni ne?".
Kasa cewa komai tayi, ta kwace hannun ta, ta murkuda masa baki tayi tafiyar ta, samun kansa yayi da yin murmushi can ƙasan ranshi, kapın shima yayi cikin gonan.
Yana ƙarasawa kuwa ya hadu da Sulaiman, suka yi ta hiran su, masu aiki na ta musu hidima.

_____________
Jamila kuwa da Habiba, bangaren dabbobi suka sauka, da isan su kuwa talo talo suka biyo su, ba shiri suka kwasa da gudu suka rasa hanyar fita, ashe akwai wani kofa ta bayan lambun, da suka ga a rupe shine suka hau katanga suka dira dan bashi da tsayi, bayan sun dira suka zauna suna ta kwasar dariyan tseren da suka yi tare da maida numfashi, sai a lokacin suka tuno da sun bar Hafsa a cikin lambu, dole suka zagaya ta ainahin mashigar gidan gonan, inda suka tsaya suna jayayyar wanda zai shiga, can kuwa suka hango Hafsa ta taho a guje ga wani leda ta rungumo shi a cikin hijabin ta, tana isowa gunsu suka saka da gudu, sune basu tsaya ba se a gurin nan da aka ɗauki Hafsa aka tafi da ita masarauta.
Ai kuwa Yarima ya sha tsinuwa, Hafsa da Habiba haduwa suka yi suka dinga zagin sa Jamila na dariya, daga karshe da Hafsa taga zagin yayi yawa gashi Habiba sai surfo wasu take, sai ta ɗan ji haushi kuma, ta sa hannu ta rufe ma Habiban baki.
__
Ashe ita Hafsa da ta fito kin tahowa tayi, da ta juya kuwa taga wani dan leda hakanan, nan ta fara kwasan ya'yan itatuwa yanda kasan abinda aka aiko ta da tayi kenan tana sakawa a ciki, idan ka duba ledar babu fruit din da bata ciro ba sai gwanda kuma dan shima tsayin ta bazai kai bane shiyasa, tana cikin tsinka kuwa sai ga daya daga cikin masu tsare gidan gonan, ji tayi yace "waye anan" ita kuma sai ta ranta a na kare. Shi kuma hango ta da yayi da leda ne yasa ya ringa fadin ku kama ta gashi tuliqi ba daman yayi gudu, Hansatu kuwa ina gudu take bilhaqqi, da ta taho fitowa kuwa taga su Habibah sunyi shirin gudun, shine fa suka gudu.

Bayan sun gama maida numfashi da hutawa sai Hafsa ta basu labarin cire ya'yan itatuwan da tayi suka dinga dariya, Jamila harda cewa wai a nemo leda a raba kowa ya kama gaban sa
Basu samu ledan ba kuwa, sai a hannu suka bawa Habiba ta tafi gida, dan lokacin har anyi kiran sallan la'asar. Hafsa baiwa Jamila ledan tayi wai ta dauka idan ba haka ba in sunje gida baza ta raba da ita ba.
Ilai kuwa Jamilan ce ta dauka har suka karasa gida, sai admiring din gidan simintin da aka gida a jikin gidan su suke, da suka zo shiga suka ga Lawan a zaune a kofar gida, gaida shi suka yi ya amsa suka shige, karewa Hafsa kallo yayi, shi gaskiya al'ajabi yake, yarinya mara jin nan ce za'a ce Yarima ya bata gida? Ai sai dai ya bata kashi ba dai gida ba kam, jiya jiya fa matar shi ta gama barbada masa tijara wai kannensa sun raina ta, musamman ma Hafsa, kuma shi kanshi yasan zata aikata, a hakan ma ai ta mata da sauki tunda a rashin kunya kaɗai ta tsaya.
Kamar daga sama ya ji sallama a kanshi, ya daga kansa kuwa sai idan sa ya fada akan injiniya Kabir, musabaha suka yi bayan sun gaisa injiniya ya barbado bukatun sa, na ya kalla Hafsa kuwa yaji ta kwanta masa a rai, idan babu hali yana neman iznin bashi daman yin hira da ita, dan shi da aure yake san ta, ba'a yi wata wata ba Lawan ya amince, abu biyu ne yasa ya amince, na farko in Hafsa tayi aure kila ta shiryu sannan zasu huta da fitinun ta, na biyu kuwa injiniya a wancan zamanin masu kuɗi ne sosai, injiniya gida yace yana san kanwar sa? Ai sun warke, ƙila idan ya tashi gina mata nata gidan ai sai yayi wanda yakai gidan simintin da aka ce a bata, ko ma fiye da hakan, dan a dan binciken da yayi da kuma yanayin injiniyan ya fahimci lalle dan babban gida ne
Shi kuma injiniya amincewar Lawan da wuri ya basa mamaki kuma ya burge sa, ko ba komai shi dama da niyyan auren ta yazo, sannan be san itace Hafsan da Yariman ya bata kyautar gida ba. Nan ya koma gidansu cikin matsanancin farin ciki har mahaifiyar sa na tambayan ta, ya fada mata, itama bata yi wata wata ba, ta taya dan ta farin ciki. İn Sha Allahu yau da dare ma zaije hira gurin ta.
Wannan kenan.
Hafsa kuwa da ta shiga gida aka ce mata yau ita ce da yin tuwo, dije miya, Azima wanke wanke, dan Malam Sule me Rini yaja kunnen su da kyau yace da ya dawo kowa ta fidda miji a mata aure wannan kenan.
Yau dai bata yi gardama ba tayi tuwo me kyau, su kuma su Mama Kulu gudun kar ta musu tuwo irin na ranan yasa basu yi mita ba har ta gama, da gamawarta tayi alola tayi salla. Suka ci tuwon daren su suka yi shirin fita gaɗa, nan da nan aka aiko wai ana sallama da Hafsa.
___________

Yarima kuwa sai yamma lis, suka koma masarauta inda suna zuwa suka je suka gaida Mai Martaba da Waziri. Daga nan suka je suka gaida Sarauniya Babba sai kowa kuma yayi sashen mahaifiyar sa.
A hanyan sa na zuwa sashen Fulani yaga Murja kawar Hafsa, da ta gaida shi ga mata murmushi wanda tasan albarkacin Hafsa taci, daman sashen su na bayi zata tafi, nan ta koma tana hawayen farin ciki, can zuwa dare suka tafi makarantar su na bayi, tana tafe tana hawayen rashin Hafsa, kusan kullum sai tayi kuka, yau ma kamar kullum ta amso takadda ta rubuta wa Hafsa wasika, tasha alwashin se ta kai ma Yarima ya taimaka ya baiwa Hafsa, ko da zata ci duka ne ta amince. Nan da nan ta share hawayen ta ta fara rubutu...

_______
Shi kuwa Yarima da zaman sa a sashen mahaifiyar sa bayan miqa gaisuwa suka ɗan taɓa hira, Fulani har mamakin Yarima take, nan ta fahimci yana cikin farin ciki ne.
A nan yayi sallan sa na mangariba da yaci abinci ma yayi isha, nan aka aiko musu kiran gaggawa daga sashen Mai Martaba, suna isa suka kwashi gaisuwa suka ga kowa ya hallara a gun.
Abinda waziri ya fada ne ya matukar girgiza su, takadda ya dauka kamar wasika, ilai kuwa wasikan ne, da tambarin masarautar Adamawa a jiki.
Karantawa waziri ya fara yi kamar haka.

"Sallama bisa tsarin addinin musulunci,
Assalamualaikum Warahmatullah
Bayan sallama da so da yarda, muna mai fada muku Gimbiya Haulatu da ake shirin yi mata baiko ita da Yarima, Allah ya karbi ranta, jiya Juma'a aka mata jana'iza aka kaita gidan ta na gaskiya
Wassalam
Sarkin Adamawa
Daga Masarautar Adamawa".

Mu haɗe a na gaba.
Fadrees ce. 🖋️🖋️

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now