20

88 8 1
                                    

Da sassafe Hafsa ta gama shirin ta, suka je suka karbo abincin su na safe wato dambu. Tana ta lura da Murja, ta ga tun jiya jikin ta a sanyaye. İta dai bata ce komai ba bayan sun gama cin abincin nasu, wanda shima sama sama suka ɗan taba, nan Hafsa ta ɗan kishingida akan katifar ta da zata yi ban kwana dashi ita kuma Murja ta zabga tagumi.

Sallamar shugabar su ta bayi suka ji a cikin dakin nasu, nan take jikin su shafa'atu ya sake yin sanyi. Kallon ki biyo ni shugabar bayin nasu ta ma Hafsa, nan da nan kuwa ta miqe tsaye ta dauki damin kayanta tabi bayan ta, su Murja, shafa'atu da Lantana har ma da wadansu daga cikin bayin na biye da Ita.
Sunzo gurin fita daga babbar gate din masarautar aka dakatar da su Murja, anan pa aka fara draman, kamar ansan zasu yi taurin kan kin tafiya sai ga dogarai da bulalu, duka suke kaiwa bilhaqqi, Hafsa nan take ta saka kuka, ba wanda zai baka tausayi a gun kamar murja, wlh yanda take kuka kamar za'a raba ta da ranta ne, nan bayin da suka rako Hafsa suka janye Murja suka koma da ita, tana ganin su shafa'atu sai kuka suke yi, Murja sai ihu take tana waigo ta har suka shige kofa na biyu, bayan tafiyarsu ne dogaren dake wurin suka ce Hafsa ta fita daga cikin masarautar ɗayan hadda daka mata tsawa wai tana sa su jinkiri wajen aikin su.

Hafsa na saka kafar ta a wajen masarautar ta shaqi iskan ƴanci, yau dai gata ƴantatta, Allah Sarki Murja, In Sha Allahu zata nema mata mafita da izinin Allah, in yaso sai ta dawo gidan su da zama tunda dai ga yanayin gidan su su.
Fita tayi ta fara tafiya, yau watan ta ɗai ɗai har guda biyu da sati biyu bata saka en gidan su a idon ta ba, ji tayi gaba-daya kanta ya juye ma, kamar wanda ta shekara bata je gida ba, toh ita tun da take bata taɓa zuwa wani gida wai dan ta kwana dayawa haka ba, hana rantsuwa sunje gidan su halime ita da su Azima sun yi kwana biyu da ta haihu. toh yanzu ita bata san ina zata fara dosa ba ma, wasu matasa ta gani a gaban ta har guda hudu, ce mata kawai suka yi an aiko su dan suyi mata jagorana ne, bata ce musu komai ba har suka kaita gida.

Sadiqu ne ya fito zashi yawo kamar dai yadda ya saba, ya sawo wata rigan sa ruwan bula, wanda taci duniya har ta gaji, sannan rigar har tayi fari fari ta dafe tsabar jimawar da take ba'a wanke ba, idan aka tashi wanke ta kuwa se taji Omo ta gaji, wandon kuwa har gwiwar ta babbarge tsabar karambani da wasan banza, cin karo yayi da Hafsa sai kuwa yaja da baya yana mai matukar zare idanu, sakin kuwwa yayi tare da fadawa cikin gida yana ihun yaga fatalwa, su Mama Lantana zanin ta har faduwa yake garin gudu, sai zauren gidan nasu yake nunawa da hannu yana cewa "fatalwa, fatalwa" Lawan da gidan shi yake gefen na su Hafsa ne ya leqo a hanzarce ƙafarsa ko takalmi babu, daman an fasa masa kofa ta cikin gidan nasu, sannan gidan da yake dayan gefen nasu shi kuma wadanda suke ciki sun bar unguwan to yanzu an daga gini ana wani hadadden gida na siminti. to tanan ya shigo, da yaga sadiqu yana nuna zaure sai ya tasamma gurin.
Yana ƙarasawa sai yaga Hafsa da wasu samari guda hudu, kayan jikin su kamar na ma'aikatan gona.
Iso ya musu, tare da kama hannun Hafsa ya shigo da ita cikin gidan, a lokacin ko wane mai rai na gidan sai da ya fito har da matan Lawan kuwa, Mama da bata jima da warkewa ba seda ta fito bayan ta kuwa Jamila ce a tsaye tun sanda sadiqu yayi ihu daman dukkanin su suka fito, su Mama Kulu ana gaban murhu ana dafa kunu, Azima tana wanki dije tana tankade, ko wannen su da yaga sadiqu ya taho ya tsaya cirko cirko.

Lawan suka gani ya shigo riqe da Hafsa a hannun sa, ai da gudu Jamila, dije da Azima suka je suka rungume ta, har sai da suka zube a kasa, sadiqu ma daya ga haka yaje ya runguma ta sai ihun murna suke tayi
Kamar hadin baki suka ji sallamar Malam Sule Mai Rini, kuma dawowar sa kenan daga tafiyar da yayi, can bayan an gama su murna, masu koke koke sunyi sun gama, da aka natsa Malam Sule Mai Rini ya sallame waɗanda suka rako Hafsa, Seda suka ajiye manyan jakunkunan da suka zo dashi kapın suka tafi.

Su Mama Lantana tun da suka kyallara ido suka ga jakunkunan hankalin su ya koma wurin, Mama Kulu tsabar kwadayin har dena marmarin dawowar mijin nasu tayi, ta karkata hankalin ta kan jakunkunan.
Sai can zuwa azahar aka miqe akaje akayi salla, har yanzu hankalin su Mama Lantana yana gun jaka, Sadiqu da ya ga haka ya zauna yaqi ya tashi ko sallan ma yayi.
Da shigan Hafsa dakin su Mama yazo ta riqe hanun ta ta bude wani sabon babin kukan, ita kada tasan yadda tayi kewar yarta, ta ringa nan nan da Hafsa, ita da kanta ta shimfida mata sallaya tayi salla ma, ita Hafsa abun har ya so ya bata dariya, dan seda ta murmusa, Jamila kuwa a jikin Hafsa tayi sallah, duk sai suke ganin kamar Hafsan ta canza musu, ta zama wata shiru shiru, Mama har ranta take roqon Allah ya sa Hafsan ta shirya
Bayan da suka yi sallah suka koma tsakar gidan nasu, lokacin har an aika su halime da Fati sun iso. Zama akayi a tsakar gidan aka ce Hafsa ta bada labarin abinda ya faru aka kaita sannan da dalilin dawowar ta, nan Hafsa ta bada labarin komai, amma ta cire inda Yarima yake dukan ta da dalilin da yasa aka kore ta, cewa tayi kwanakin da aka ɗebe mata ne suka kare. A hakan ma Yarima bai tsira ba seda su Dije su kayi ta zunduma masa ashar har hakan ya ɓata ma Hafsa rai.
Bayan an kira la'asar Malam Sule me Rini y miqe ya saka su Azima su saka kayan da aka aiko Hafsa dashi cikin dakin sa, shi kuma ya miqe yaje masallaci, daga nan zai wuce gidan yayansa Musa ya maida masa da batun in yaso ko gode suje su miqa gaisuwar godiya a fada.
Wannan kenan

__________

Da dare yayi su Hafsa suka fita gada, Seda suka yi kusan awa biyu suka dawo gida a gajiye
Can da ta nitsa mama tace ta basu labaran abinda ya faru a masarautar, nan ta dinga basu labarin irin damben da ta dinga yi, na dariya suyi dariya na kuka suyi kuka, a nan ne Hafsa take fada ma Mama kan ta hadu da wani wai Ibrahim dan masarautar Borno da kamannin da yace tana masa da wata, harma yace zai dawo, ita dai Mama bata ce komai ba, amma taji somewhat uneasiness a ranta.

Suna ta hirarrakin su har barawon yazo ya sace su
On the other hand kuma, mama Lantana da Mama Kulu da kyar suka yi bacci, dan har sai da suka yi maganan jakunkunan akan Malam tsabar bakin hali ya biye jakunkunan a dakin sa. Nan dai suka rabu rai babu dadi.

Su Azima kuwa sunji dadin dawowar Hafsa domin ita ce mai tare musu fada duka da tana xin zalinsu, suma din kuma ba baya bane wajen rashin kunya.

Washegari Baba yayi sammako suka je fada shida Baffa Musa suka je yin godiya, sai a lokacin aka fada musu sanadiyyar koran Hafsan, nan suka dawo jiki a sanyaye, da Malam Sule me Rini ya koma ya qira Hafsa yaji ta bakin ta itama ta fada masa kamar yadda ya faru
Sede tace masa ita Babu laifin ta a ciki.
Wannan kenan.

Mu haɗe a shafi na gaba da yardar Allah.
Ayi sharing, voting da commenting dan Allah

Taku ce har kullum
Fadrees 🖋️ 🖋️.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now