15

92 8 0
                                    

"Hafsa"
Ya kira sunan ta
"Kinyi mamakin ganina koh"?
Ita dai Hafsa ido ta zuba masa, tana jiran taji dalilin kiran da ya mata
"Dagaske nake Hafsa da nace miki kina da kyau, sede ba wannan bane ba, gobe idan da ran mu zamu kama hanyar Gobir, idan munje mahaifina ya natsu zan fada masa batun ki, se yazo ya neman min auren ki, İna matukar kaunar ki, kisa wannan a ranki, Ni Isma'il ina dauke da matsanancinciyar soyayyar ki, kece a cikin zuciya ta sannan........"
Be karasa ba se ga Yarima a gaban su, fuskar nan kamar hadari, be ko kula kowa a cikin su ba ya saka hannu ya janyo hannun Hafsa suka fara tafiya, fusge hannun ta ta fara yi amma mutumin ki yayi haikam yaqi bata dama, yana zuwa sashen sarauniya babba ya kutsa kai a ciki ba tare da neman izini ba sannan kuma be saki hannun Hafsa ba.

Suna shiga suka samu Suleiman, Hayatu da kuma Shamsu a ciki a zaune suna tadi
Hafsa faduwa tayi bisa gwiwowin ta, ta ma rasa ya zata yi, gaisuwa zata kwasa ne ko kuma kallan mamakin da dukan su en cikin dakin shakatawar suke jifan su da shi zata kalla, jikin ta ne ya kama kyarma.
"Yarima riqe da hannun baiwa? Unbelievable" fadin ko wannen su kenan a cikin ransu tare da sakin baki, sallaman Ismail suka ji, da ya shigo ya zube kasa ya kwasa gaisuwa a gun Sarauniya Babbar da bakin ta itama a sake yake.

Bayani Isma'il ya fara koro mata, akan ta shiga tsakanin shi da Yarima, dan yaga yarinya yana so ya tare mishi hanya, kuma ba kowan shi bace face baiwar sa wanda yake wulakantawa. Hakan da ya fada ya ɓata ran Hafsa, wato itace baiwar kenan.
Hajiya Babba kuma ta kasa taɓuka komai dan bakin ta mutuwa yayi
Hayatu ne ya miqe ransa a bace yace "haba Yarima gaskiya Ni duk baku min adalci ba, kaipa yanzu yanzu naga muka fito daga fada aka ce za'a tura ma Sarkin Adamawa saƙo akan a nema maka yarsa, kuma naga ai baka musa ba, sannan ita yarinyar nan da kai kake maganan ta, nine nake son ta" ya fada yana kallon Ismail, zuciyar Hafsa seda ta saki Bomb, wa yaga tashin hankali, ai nan take ta sume ltsabar kidima.

Ni na dade ina matuƙar san sarautan nan amma da shike kaine babba yasa ban ma taba nuna maka ba, sannan yarinyar nan tunda na dora idona akan ta naji ina mutuwar sonta, gaskiya abu daya zan iya fada tunda dai kai ba son yarinyar nan kake ba, kawai ka sallame ta, in yaso ni se inje in aure ta, sarauta kuma na bar maka har abada, tunda kaine babba. "Kai kuma" ya juya yana kallon Ismail "Ka ma cire ranka akan yarinyar nan, taya gida bai ƙoshi ba, na waje ze saka baki"?

Jin haka yasa jikin su suka yi sanyi, barin ma Suleiman da shima yake ciki, amma lura da take taken Yarima ya sa shi ja da baya, sannan kuma ga abinda ya faru a fada, na bashi auren Bilkisun da aka yi, shi ya gode Allah ma da be taba nuna mata komai ba ko da wasa.
Isma'il kuwa kallon rabi saura kwata yake jifan Hayatu dashi.
Shi kuma gogan shiru yayi, shi dai ba sonta yake ba, hasali ma be ga komai a tattare da ita ba inba rashin kunya ba, shidai kawai baze iya barma ko wannen su ba, haka zasu gani su kyale sbd baiwa dai tasa ce ba wanda ya isa ya ja dashi akan hakan. Ah toh.

Zama yayi abin shi akayi tayi amma yaqi cewa komai, Sarauniya Babba se magana take masa ya share ta, karshe dai miqewa yayi da niyan ya tafi, se ya ga Hafsa a sume, da kanshi ya tashi yaje ya ɗibi ruwa ya watsa mata, ta farfaɗo se dukkan su suka dawo da hankalin su kansu, ɗaga ta yayi da kanshi ya kama kafadar ta suka fara tafiya, yana fita ya hadu da shafa'atu da ta gama jin komai, kallon gargadi ya mata, na karta sake kowa yaji batun, kapın ya mata alama da tazo ta kama Hafsa su tafi
Kama ta tayi suka tafi, se sannu take mata, suna shiga ta kwantar da ita akan katifar ta, ciwon kai ne ya saukan ma Hafsa, gashi Murja bata nan
Tunani ta fara yi, na abinda ze biyo baya.

___________________

Yarima kuwa Barga ya nupa, jikinsa har karkarwa yake tsabar ɓacin rai, yana isowa gun dokunan sa, ya doshi gurin favorite nasa, ya shiga shafa shi, tare da sakin ajiyar zuciya.
A falon Sarauniya Babba kuwa fada ne ya kaure tsakanin Hayatu da İsmail, kamar zasu bugi juna, Shamsu kuwa se shigar ma wa dan uwansa yake Sulaiman ne yake ta kokarin raba su.
Da Sarauniya Babba taga haka, nan ta shiga tsakanin su, shine pa suka samu suka lapa

________________

A bangaren Kilishi kuwa ba ƙaramin bakin ciki tayi ba da taji zancen za'a nema wa Yarima yar sarkin Adamawa, domin a danta Hayatu tayi ma tanadi, sannan in har aka hada su aure, kamar ƙiman ta ta ƙaru ne. Amma zatayi wa tufkar hanci. Baza ta taba bari Fulani ta fita ba, sannan ta tsani waziri har ranta.

____________

Samira ce a kwance riris kamar wadda babu nunfashi a jikin ta, tayi kukan tayi kukan har ta gaji hawayen sun ma dena zuba, hakikanin gaskiya bata taɓa tunanin zata aure wani da ba Yarima ba, sannan an shammace ta sbd ita bata jin zata iya rayuwa da wanin da ba Yarima ba.
Can dai zuwa dare tayi shiri ta tafi gun Bilkisu dan su jajanta ma juna, ita da take san yayanta se ba'a bata shi ba, instead ita Bilkisun aka bata nata yayan.
Da isar ta sashen Fulani ta iske Yarima a cikin dakin shakatawar yana kishingide ga tarin abinci a gaban sa amma ba ta shi yake ba, abun duniya ya taru ya masa yawa, tunanin wani abu daban ma yake.

İdo Samira ta zuba masa bata ko kyaftawa, nan duniya babu wanda take so da matukar kauna da san gani kamar shi, gashi ana so a musu katanga, ba ma wannan ba, tasan mijin da zata aura baze taba kamo ko da yatsar Yarima bane a kyau ko kuma kasaita.
Kusan minti biyar kenan bata motsa ba seda taji taku a bayan ta kapın nan, Fulani ta hango tana shigowa cikin palon, nan da nan ta durqusa ta kwashi gaisuwa tana fatan Allah ya sa bata ganta tana kallon danta ba, amsa mata Fulani tayi cikin sakin fuska, kapın nan tace mata ta shiga dakin Bilkisun tana ciki
Da shigan ta ta samu Bilkisu tana kwance akan gadon ta, hadimai na mata labarai da tausa.

Sallamar su tayi ta miqe ta kamo hannun Samiran ta zaunar da ita kan gadon
Da zaman ta ta fara kuka, ta fara koro mata jawabi. Nan take jikin ta yayi sanyi domin ita a nata bangaren tayi na'am da zabin da aka mata, duk da bata taba tsammanin soyayya ze iya shiga tsakanin ta da Suleiman ba, yanzu gashi auren su ma za'a saka. Sannan ga kanwar sa da ta dade da fahimtar tana san yayanta amma bata taba nuna mata ba, se gashi itace aka mata wani zaɓin.

Rarrashin ta Bilkisu ta dinga yi har ta samu tayi shiru, nan take Samira taji salama tare da jin sabon tsana ga Kilishi, domin ita ce ta ɗora ta akan hakan tare da mata alqawarin samun sa, yanzu gashi ta kaita ta baro.

Read and Share
Vote and Comment.

Yours lovely
Fadrees 🖋️ 🖋️ 🖋️.

See you later.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now