28

51 5 0
                                    

Mikewa Malam Sule Mai Rini yayi, yace da injiniya da Ibrahim din su shigo zauren su su zauna su tattauna, bayan sun shigo sun gama gaishe gaishe ne shi injiniya ya fada bukatar sa, na neman izinin ya bashi daman turo iyayen sa dan ayi aure, shi kuma Ibrahim sai yace yazo ne da Yan garin su, suna so su gana da Hafsa, sannan shima yana neman izinin auren Hafsan. Abu goma da ashirin suka hade wa Malam Sule Mai Rini, nan take kuwa ya sanar dasu anyi ma Hafsa aure yau yau a Masarauta, ta auri Yarima İdriss, injiniya saida yaji hajijiya ta kama shi, Allah Sarki, dazu a gaban sa akayi auren bai dauka da Hafsan shi bace nan ya tashi sukuku zai miqe sai ya kasa, da yaga haka sai ya ɗan zauna, Malam Sule Mai Rini ne ya bashi hakuri tare da cewa ya bashi daman ya zabi daya daga cikin yaran nashi da suka rage, dan shi kanshi yasan Azima da Dije basu da tsayayyun samari, Jamila ma ta kai a mata auren, injiniya ce masa yayi zai yi shawara sai ya tafi, hawaye na zuba daga idanunsa.

Sai ya rage daga malam sule mai rini sai Ibrahim, shi kansa Ibrahim saida yaji hajijiya na neman kayar dashi. Daurewa yayi ya sanar dashi dalilin zuwan sa, akan tunda ya fara ganin Hafsa yaga tana masa kama da wata, yanzu da yaje garin nasu ne ya kara tabbatar da hakan, har ma ya taho da mutanen su biyu daga garin nasu.
Ce masa Malam Sule Mai Rini yayi da ya qira su, shima bari ya ma Hafsan da maman ta magana su fito, shiga malam sule yayi cikin gida yace wa Mama Zainabu su fito ita da Hafsa, sai tace masa zazzaɓi ya rufe Hafsan, nan ta saka Jamila a gaba suka yi zauren, Jamilan na riqe da hannun maman.
Suna shiga zauren, suka hango wasu matasa uku a zaune suna tattaunawa da Baba, suna ganin Mama suka miqe a tare cike da tsantar kaduwa, da basu bar dayar a can ba, da zasu ce itace ta nan, zama mama tayi tana kare musu kallo daga kasa har bisa, ji tayi zuciyan ta ya buga.
Baba ne yace zasu iya bayyana kawunan su, Ibrahim ne ya fara fadan alaqar sa da masarautar Borno sannan da dalilin da ya sa suka zo nan, sai ya kara da fadin "kamar yadda na fada, wadannan su biyun daga Borno muke dayan yaran mijin mama Maryamu ne, wadda take tsananin kama dake, itama tana da ƴa sa'ar Hafsa ce, saidai wancan din matar Galadiman Borno ce, wanda hakan ya nuna wannan shine ɗan Galadiman, wannan kuma dan Hakimin Bornon ne.
Mama ne take ta musu kallon al'ajabi, ita sam bata gane inda suka dosa ba, kallon dan Galadiman tayi me suna, Abubakar tace ya mata bayani
"Mama Ibrahim yana so yace Miki ne, akwai mahaifiya ta, a can Borno wacce kuke tsananin kama da ita, wanda bana kyautata zaton ƴar biyun ki ce ita, domin yadda kika gankin nan, haka take itama sakk, babu abinda ya bambanta ku, hatta yar kin, nan tana kama da kanwata". Abubakar ya karashe.
Mama al'ajabi ne ya kama ta, kamar tace karya suke bakin ta ya mata nauyi, inaga shiyasa da ta gansu zuciyarta ta buga.

Abubakar ne ya juyar da kansa kan malam sule mai rini yace
"Baba dan Allah ina neman alfarma, ka bani daman na tafi da mama da yar kanwata garinmu, ina so in yi wa mamata bazata ne dan Allah" ya karashe muryar sa da alamar roqo kamar ze fashe da kuka
Baba ne yayi shiru sai can yace "yaushe zaku koma garin naku"?
Ibrahim ne wannan karan yayi magana yace "gobe ko jibi da yardar Allah,
Baba ne yace toh Allah ya kaimu, in yaso sai a samu wadanda zasu biku ku tafi taren. Murmushi dukkanin su suka saka, Mama dai tayi shiru abin ya bata mamaki, abu biyu sun hade mata na farin ciki da na bakin ciki, dan tunda taji an ce matan Yarima suna mutuwa hankalin ta bai sake kwanciya ba amma tayi murnar zuwan samarin nan sosai da sosai.  ita kuma Jamila sai farin ciki take, Finally suma sun samu ƴan uwan mamansu.

Sallama suka ji an doka, Ibrahim ne ya miqe ya leqa, wani bafade ya gani a tsaye, tambayar sa yayi shin Malam Sule Mai Rini yana nan? Yace masa eh, sai bafaden ya basa wata wasika yace ya bawa Malam Sule Mai Rinin. Karba yayi ya koma zauren ya baiwa malam sule mai rinin.
Karantawa yayi, rubutu ne na ajami, sannan da tambarin masarautar Bauchi a jiki.
Abinda ke kunshe a ciki kuwa shine, "Gobe za'a aiko keken doki azo a dauki Hafsa a tafi da ita Masarauta.
Kayayyaki suka ga ana ta shigowa dasu, Lawan da fitowar sa kenan ya tsaya a jikin kayayyakin. Har baba suka gama tattaunawar su, su Ibrahim suka tafi masaukin su, su Mama kuma suka shige cikin gida, malam sule mai rini kuwa yayi alola dan lokacin har an kira sallan mangariba.

Lawan ne yasa aka kwashi kayan aka shigar dashi sabon gida, aka ajiye a dakin da nake kyautata zaton na mama Zainabu ne.

__________

Azima kuwa koda ta shiga gida sai ta rabza ihu, har da burburwa, ana ta tambayan ta meya paru sai can yace musu "Ba dazu kunji labari ya zagaye gari Yarima matar sa ta mutu an sa sake bashi wata har an daura aure ba? Nan kuwa suka gyada kansu, toh ba kowa bace amaryar face Hafsa, Hafsan gidan nan ma kuwa. Nan da na suka sake salati hassada ƙarara a fuskokin su, sai daga baya suka kwantar da hankulan su tunda ance matan nasa ma mutuwa suke yi, sai a lokacin zancen sabon gidan yazo kansu Kulu, su dai ko ajikin su, ko da wani abu ya samu Hafsa ai dai sun tsira da sabon gidan su.
Duk abubuwan da ake a kunnen Hafsa da take dakin su, wanda Jamila ce ta taimaka mata ta kaita dakin, ita kanta Jamila tayi mamakin wannan abu, sai bata ce komai ba, ta wuce take ta ɗan riqe mama suka je zaure wai baba yana neman su ita Hafsa ba wannan bane damuwan ta auren da aka mata shine babban damuwan ta, bata taɓa tunanin zata yi aure nan kusa ba, duk da Baba yace daman ze musu aure, amma a rasa waye mijin nata sai Yarima?
Inaaa gaskiya baza ta iya dauka ba, Yarima yafi karfin ta nesa ba kusa ba, da haka baccin wahala ya kwashe ta, Se bayan isha ta farka tayi Sallolin ta, a lokacin Jamila take bata labarin samun en uwan Mama, ji tayi ranta ya ɗan yi sanyi. Baccin wahala ne ya sake kwashe ta cike da saƙe saƙen halin da injiniya yake ciki, dan ta tabbata duk inda yake yanzu kam yaji labari.

_______
Da safiya tayi suka dunguma suka koma gidan siminti. Gida ne babban gaske mai matukar kyau, ko wacce mata saida ta samu daki da dakin shakatawa daidai gwargwado, se dakin sadiqu, sai ta waje sashen Malam Sule Mai Rini, Lawan ne dai yake tsohon gida. Zuwa sha biyu Mama ta aiki Jamila gidan su Habibah taje ta fadawa maman yadda ake ciki, sannan su taho da Habiban
Ba'a jima ba kuwa gida ya fara cika dan labari ya karade ko ina, wasu daman da biyu suka zo, dan suga sabon gida sannan dan suga ko dagaske ne zancen auren, ganin yanda ake shige da fice ne ya gaskata hasashen su
Wanka Habiba ta taimaka ma Hafsa tayi, suka bude jakunkunan da aka kawo jiya suka ga kayayyaki na alfarma da murjanai, nan aka shirya Hafsa aka sa mata alkyabba, da yamma ma yayi aka sake mata wanka ta saka wasu kayayyakin.
Shi kuma baba daman wannan jakan da aka taba kawo Hafsa dasu ya bude, yaga wasika akan cewar ga gida nan na Hafsa sannan ga sulalla, karafuna, kwabbai da sisina suyi amfani dashi, kamar yasan kuwa kudaden zasu musu amfani, dan dashi baba yayi ta hidima har yamma tayi aka zo aka ɗauki Hafsa aka saka a mota, aka tafi da ita

Fadrees 🖋️

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now