khadeejah 💙 2

43 2 0
                                    

"Ke kiyi sauri kinsan mutumin nan in ya shiga baya bari a ƙara shiga class ko"Khadija take cewa tana jan hannun kawarta anam dan su tafi class da wuri.suna shiga kuwa da minti kaɗan se gashin ya shigo.

Haka suka gama class suka zauna suna hira,Maryam tace"hmm yau lecturer Nan bai zo da mugunta ba wallahi,dan da baze bar kowa ya shiga in yayi letti ba". Khadija taja tsaki tace"wallahi chan ta matse misi".anam dariya tayi tace"chan ta matse Miki dai,dan wallahi in yace baza ki shiga ba toh wallahi kinsan ba inda zaki".haka dai suka tashi ana hira har suka isa kofar makarantar, sallama sukayi kowa ya kama hanyar sa.

Khadijah tana sauka a napep ta buɗe gate na gidan su ta shiga parlour da sallama,ba wanda ta gani kawai se ta wuce ɗakin ta,tana shiga toilet ta wuce tayi wanka tayi alwala se ta fito,tasa wani riga dogo baki,ta shimfida sallaya tasa hijabi tayi sallah.tana idar wa ta wuce ɗakin mama,tana shiga ta same ta akan gado tana zaune,zuwa tayi kusa da ita ta zauna tana cewa"mama ina wuni",mama murmushi tayi kafin tace"lafiya lau,kin dawo kenan,ya makaranta".itama murmushi tayi tace"makaranta lafiya lau yau ai lecturer bai hana Ni shiga class ba".mama dariya tayi tace"yau kinyi sauri kenan,toh je kici abinci Koh".gwaɗa kai tayi se ta tashi ta wuce kicin ta ɗebe abinci ta zauna a island na kicin ɗin taci abincin ta,Yasmin ne ta shigo kicin ɗin ta kalle Khadija tace"yaushe kika dawo".kallon ta tayi tace"bai daɗe ba,wani abu ne". Yasmin ne tazo kusa da ita tace"ki shirya muje gidan aunty A'isha".tura baki tayi tace"yanzu fa na dawo kije ke kaɗai Ba ga Habiba ba".

Habiba cousin nasu Khadijah ne kuma tana karatu a Maiduguri shine take zama a gidan su dan ita er Yola ce.yasmin tayi dariya tace"amma ai da ice cream nace zan saya ai zaki tashi da wuri ai". Khadija tayi murmushi tace"toh ki faɗa ki gani".dariya tayi ta fice daga kicin ɗin.khadija ma sauka tayi ta ajiye kwanon wurin me wanke wanke ta wuce ɗakin ta,tafara danne dannen waya har dai lokaci ya tafi aka kira sallar magriba,tashi tayi ta wuce yin sallah tana idarwa se wayar ta tafara ringing,dauka tayi tana cewa"baby ka manta dani Koh,ai Ni nayi fushi da kai".

"Haba dai taya zan manta Dake wallahi wasu aiki ne nake yi shesa".

"Toh ya aiki,ya gida".tafaɗa tana ɓata rai dan har ga Allah bata son shi kawai dai ta yarda ne dan kar tayi breaking heart nashi.

"Lafiya lau ke ma ya gida,yasu mama"."lafiyan su kalau,kaga mama tana kira ne se gobe".kafin yace komai ta katse wayar tana jan tsaki,a fili tace"kai duk abinda nake maka amma kaki gane wa".haka dai ta shirya takaddun ta na gobe tayi sallah ta kwanta.

Nasir 💙
  Nasir dai ɗan abuja ne kuma baban shi yana da kuɗi shima kuma yana da kudi,Nasir duk inda kaga na miji toh shima ya kai.fari ne yana da saje daya kwanta a fuskan shi, kyakkyawa ne sosai dan ko ina yaje se an kara mishi wani kallon,mata kuwa se Binshi sukayi shi kuwa ba wanda yake kulawa dan mata basa gaban shi.

Su huɗu ne iyayen su suka haifa,shine na farko se Ahmad se Arwa se nasrin.nasir ba mutum bane me magana kuma kowa ya sani.a Maiduguri yake da zama ɗan a wurin yake aiki amma iyayen shi suna abuja.a gidan shi yake zama shi kaɗai.bayi da hayaniya sam gashi a biyar yake baya kula ko wace yarinya.

Nasir ne a zaune akan kujerar parlour yana danna laptop nashi,wayar shi ce ta fara ringing,dauka yayi da sallama yace"Abba ina wuni".ta wayar ya amsa da"lafiya lau Nasir,ina neman kane gobe ko jibi kazo Abuja".Nasir ne ya sauke ajiyan zuciya yace"toh Abba inshallah gobe zanzo". haka suka yi sallama, Nasir tashi yayi ya wuce ɗakin shi ya shirya kayan shi a akwati se yayi zamar shi a zuciyan shi yana cewa" me kuma ya faru".haka dai har ya kwanta bacci.

Khadijah ce na gani tana sanye da wani atampa me kyau tana sallama da mamanta"mama na tafi".mama tace"toh a dawo lafiya"."Allah yasa".fita tayi ta tare napep suka kama hanyar makaranta,tana isa ta biya kuɗi se ta shiga makarantar tana ɗaga waya ta kira anam,anam ta amsa wayar tana cewa"ba dai har kin iso ba". Khadija tace"na iso kina ina ne"."ina hanya, amma na kusan ƙara sowa". Khadija katse wayar tayi ta wuce class ta haɗu dasu Maryam,zama tayi tana cewa"sannu ku enmata". Maryam tace"wai harda sannu kenan,toh sannu kema".tsaki taja tace"in ba,ace muku sannu ba kuce bakin hali yanzu ance sannu kuna magana kuma".a daidai lokacin lecturer ya shiga class ɗin ya fara koyar wa,bayan minti kaɗan se ga anam ta shiga class ɗin,ahankali ta shige bai gantaba, Khadija kuwa tana ganin ta da karfi tace"uwar letti se yanzu".ai kuwa malamin ya juya ya kalle anam yace"why are you late".anam ta kalle shi tace"sorry sir".yace"fita kibar class ɗina".fita tayi ita kuwa Khadija Dariya take yi me sauti.malamin ya kalle ta ya kira da hannu,tashi tayi taje gaban shi ta tsaya, kallon ta yayi yace"mesa kike dariya". kalle kalle ta fara se tace"babu komai"."toh kema ki bita".zaro idonta manya manya tayi tace"banyi komai bafa"."nace ki fita min a class".wuce wa tayi ta ɗau jakarta ta fita dan ita bata iya bada hakuri ba.tana fita anam ta fara mata dariya se  taje wurin ta ta zauna tana harararta tace"muna fuka kawai".anam ce tace"daman ai da gangan kikayi magana dan ya Koreni, toh dai gashi kema ya Kore ki". Khadija manna mata tayi har dai aka gama class sauran suka fita se suka wuce wani class,haka dai har sukayi sallar la,asar tukunnan suka fita.

Anam ta kama hannun Khadija tace"kizo muje yau jalil zaizo ya ɗauke Ni se mu sauke ki".tace"toh ai shikenan daman na gaji da hawan napep.zama sukayi har wata 4o6 tazo tayi horn,anam taja hannun Khadija suka wuce wurin motar, Khadija ta shiga baya ita kuwa anam ta shiga gaba.jalil ne ya juya yace"Khadija kenan sannu ya kike". kallon shi tayi tace "lafiya lau".bata kara Kula su ba se maganar soyayya suke yi ita kuwa haushi ma suke bata,a zuciyar tana cewa, dama bata shiga motar ba.haka suka isa har kofar gidan su Khadija suka ajiye ta ta shiga gida,direct dakin ta taje tayi wanka sannan ta ci abinci,se ta wuce ɗakin mama,tana shiga ta same su dukka suna zauna suna hira,mama ta gaisar tukunnan ta zauna aka cigaba da hira har lokacin sallah tayi,koma wa ɗakin ta tayi,se tayi sallah habiba ce ta shiga ɗakin tana cewa"shirya muje shan ice cream,ai kuwa da sauri ta tashi tasa abaya ta sa gele sannan ta fesa turare suka wuce,motar Yasmin suka shiga,ita da Yasmin da hadiza ne a motar suna ta hira har suka isa wurin,sauka sukayi suka shiga, Khadija dauka favourite flavour nata waton chocolate,haka suka gama sha har suka wuce, suna dawowa sallah tayi se ta chanja riga ta kwanta.

Nasir kuwa yau ya kama hanyar Abuja da jirgi,yana isa Ahmad ya dauke shi,suka shiga cikin motar Ahmad yace"yau dai Allah ya kawo ka,kullum kai se Maiduguri".Nasir murmushi yayi yace"gashi ai dai nazo Koh".dariya yayi har suka isa ya sauka direct side nashi yaje yayi wanka yayi sallah aka kawo kishi abinci yaci,bayan ya gama ci se ya wuce side na Abba,da sallama ya shiga Abba da mommy suna zaune suna hira,suka amsa sallamar shi ya shiga ya zauna se yace"Ina wunin ku".suka ce lafiya.abba ne yace"Nasir na kira ne kazo Abuja dan magana me muhimmanci nake so muyi dakai".Nasir ne yace"toh Abba ina jin ka".Abba ya gwara murya yace"kasan dai likita yace ciwon se kayi aure ze warke kuma ya daɗe ina ce maka ka fitar da matar aure ƙaki ji". Shiru Nasir yayi,Abba ya cigaba da cewa"toh Ni a matsayin wanda ya damu da kai kuma mahaifinka na zaɓa maka wanda nake so ka aure,a gidan amini na wanda yake Maiduguri wanda ya rasu nake so ka zaɓa ɗaya daga cikin yaranshi ka aura,dan na yarda da tarbiyyar su sosai".Nasir saukar da kai yayi bai ce komai ba yace"toh abba".Abba ya cigaba da cewa"yaran shekarun su daman daman ne,kuma nayi magana da ƴaƴan baban su kuma ya amince,yanzu inaso ka zaɓa me shekara nawa kake so".Nasir shiru yayi se ya ɗaga kai ya kalle Abba yace"Abba duk wanda kuka zaɓa min ma yayi".Abba ne yace"kai zaka zaɓa da kanka".kawai Nasir yace"sha tara".Abba yace"toh Masha allah gobe zamu  haɗu da yawun nata wanda yake abuja dan da wuri nake so ayi auren,kaga rashin lafiyar ka karuwa yake yi".Nasir gwaɗa kai yayi ya tashi ya fita daga falon,jiri  jiri yake ji haka dai har ya ƙarasa ɗakin shi yayi wanka ya kwanta dan kanshi kamar zata fashe yake ji.


❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now