khadeejah 💙 11

23 3 0
                                    

Knocking kofar da taji ne ya sata ta tashi daga bacci,bayyi magana ya wuce masallaci,alwala ta shiga tayi se tayi sallah ta sauka kucin,dafa abinci tayi se ta ajiye akan dining,Nasir da sallama ya shiga parlour se ya wuce ɗakin shi,bayan Khadija ta gama cin abinci ya sauko parlour.yasa wani brown gezna da hula se wani kyau ya kara,zama yazo yayi a dining, Khadija ta lalle shi se tace"ina wuni".kallon ta yayi yace"yanzu yini ne?".shiru tayi ta shiga da cin abincin ta a zuciyar ta tana cewa"danma ka samu na gaishe ka".haka shima yaci abinci,bayan sun gama ta kwashe komai ta wuce kicin ta fara wanke wa,Nasir ya shiga kicin ɗin yana ce mata"Ni zan fita".bata juya ta kalle shi ba tace"toh".wuce wa yayi ya fita,ita kuwa tana gama wa ta je ɗakin ta tayi wanka tasa wani atampa dogon riga me kyau tayi ɗauri ta shafa lip gloss ta fesa turare se ta sauka parlour, knocking na kofar parlour taji anyi,tashi tayi taje ta buɗe,su hafsat ta gani ta rungume su tace"se yanzu zaki zo".taslima tace"dan ma kin samu munzo".zama sukayi se Khadija tace"nikam hafsat na manta wani agogo na a cikin drawer na kin gani?".hafsat tace"ban Gani ba amma bari na kira Yasmin in zaau zo se sukawo Miki".gwaɗa kai tayi hafsat ta kira Yasmin tana cewa"yawwa adda in zaki zo Khadija ta manta agogon ta a drawer kizo mata da shi". Yasmin tace"toh bari zan duba".katse wayar tayi suka cigaba da hira haka dai yan uwa da kawaye sukai ta zuwa Khadija se farin ciki,bayan sallar la'asar aka kawo abincin yini aka zuba wa kowa se aka rage a flask aka aje wa Khadija na dare.

Su zainab Suna zaune akan gadon Khadija se Maryam tace"nikam ya naga kina tafiya lafiya lau ne?".dariya sukayi dukkan su, Khadija tsaki taja tace"toh daman kina so na tafi a lankwashe ne".anam tace"kai Maryam Allah ya shirye ki".zainab tace"ai ton gaskiyar ta,mufa muna son yaro fa toh". Khadija tace"se kuzo ku samu yaron ai da kanku".kamila tace"yi hakuri maida wukan kinji".haka dai ta hakura har magriba tayi aka fara watse wa,su hafsat ne suka tattara gidan aka share akayi mopping gida yayi kyau tukunnan da kyar Khadija ta barsu suka tafi.

Zaune take a parlour tana kallon tv tashi mota ya shiga gidan,buɗe kofar parlour Nasir yayi da sallama ya shiga,ko kallon shi bata yiba ta amsa sallamar se ya yau sama,bayan minti kaɗan se ya dawo da wani shirt se da wando ya zauna a kusa da ita,ba wanda yace wa wani sannu,bayan kusan minti biyar Khadija ta tashi ta shiga kicin ta ɗebe abinci ta zo ta zauna ta fara ci,Nasir ne ya kwace palate ɗin a hannun ta,tura baki tayi tace "ka bani abinci na".Nasir ya tashi ya ɗaga hannun daya riƙe palate ɗin sama yana cewa"ki karɓa da kanki mana".tashi tayi ta dinga salle dan ta karɓa amma ina Nasir ya fita tsayi sosai,da taga baza ta iyaba tace"Ni ka bani abinci na zan kawo maka wani".se yace"Ni wannan nake so".tace"nima nawa nake so".gwaɗa kai yayi se ya bata ta karɓa ta zauna se ta kalle shi tace"bari na deba maka". girgiza kai yayi alamar a'a.gwaɗa kai tayi ta cigaba da cin nata har ta gama taje ta ajiye kwanon ta fita suka cigaba da kallo har bacci ya ɗauke ta,Nasir juya wa yayi ya kalla tayi bacci se yayi murmushi ya kashe komai se ya ɗauke ta chaɗak har kan gadon ta se ya rufe ta ya kashe wuta ya wuce ɗakin shi,yana shiga shima ya kwanta.

Khadijah a firgice ta tashi kuma se ta kalle duhu ko ina,da sauri ta tashi tafa ihu tana neman kofa,dakyar ta samu kofar se ta fita,taga parlour ma da duhu kawai ta tsuguna tayi ihu sosai wanda sanda ya tayar da Nasir daga bacci,da sauri ya fita se ya kunna wutar parlour ya je wurin ta yana cewa"me ya same ki?".se tace"ina tsoron duhu kuma juya ma dakyar nayi bacci".yace"zo muje ɗaki na".fara tafiya ɗakin yake ita kuwa kallon shi take a zuciyar ta tana cewa"ba inda zan shiga".Nasir ya isa kofar ɗakin shi se ya juya yaga tana tsaye kawai se ya zaro idonshi yana cewa"yawwa gashinan a bayan ki".ihu tayi da sauri ta riga shi shiga ɗakin ma,shi kuwa dariya yayi shima ya shiga,tana tsaye se ya wuce ya kwanta,kanshi tazo ta tsaya tana tura baki tace"toh Ni ina zan kwanta".se yace"ki kwanta ta gefen chan".kallon wurin tayi se ta juya ta kalle shi,shi kuwa har ya lumshe ido harararshi tayi daidai lokacin ya buɗe ido se suka haɗa ido,da sauri ta zagaya gadon ta kwanta ta gefen,se wani abu yazo kanta tana tunanin yadda taje ɗaki tunda dai ita a parlour tayi bacci,haka dai da tunanin har bacci ya kwashe ta.

Kamar a mafarki Nasir taji na cewa"lokacin sallah yayi".tashi tayi shi kuma ya wuce masallaci bayan ta isar da sallah ta sauka ta dafa abinci se ta koma tayi wanka se tasa wani less red colour ta fesa turare tayi kyau sosai,sauka tayi daidai lokacin shima Nasir yake fita daga ɗakin shi,zama sukayi a dining se tace"ina wuni yaya Nasir". kallon ta yayi yace"lafiya".zuba abinci tayi ta fara ci har suka gama,Nasir ya kalle ta yace"yau zaki je gida ki gaishe dasu mommy dan gobe zasu koma Abuja". shiru tayi mishi,bayan ta tattare kwanukan ta wanke se ta koma ɗaki ta kwanta,Nasir ne ya shiga ɗakin yana cewa"ki shirya mu tafi".gwaɗa kai tayi se ya fita ta ɗau gele fari ta fesa turare taɗau jaka da waya ta fita,a parlour ta sameshi yana kallon ta ya tashi suka fita,motar shi suka shiga ya kunna me gadi ya buɗe gate sukayi fece warsu.ba wanda ya kula wani a motar har suka isa gidan,horn yayi me gadi ya buɗe suka shiga, parking yayi se suka fita,haka suka shiga parlour da sallama,mutane ne a parlour suka amsa,zama tayi a ƙasa tana cewa"ina wunin ku".dukkan suka amsa da lafiya.arwa ce tazo wurin Khadija tana cewa"amarya kinga yadda kika yi kyau kuwa me sirrin ne".a kunnen Arwa Khadija tace"yaya Nasir ne sirrin".zura ido Arwa tayi se ta fashe da dariya tana ganin Nasir.arwa ce take nuna wa Khadija kowa ita kuma tana gaishe su,wurin mommy a karshe suka tsaya,Arwa tace"ga mommy na kuma". Khadija sauke kai tayi tace"mommy ina wuni". murmushi tayi tace"lafiya lau Khadija ya kike".tace"lafiya na lau".mommy tace"mun san bamu Miki daidai ba amma se hakuri,Allah ya Miki albarka".Ameen tace se Nasir dake shigo wa daga waje yace"kun gama ne dan dare na yi".aunty tace"yanzu rowar amaryar taka kake mana,yanzu ne fa karfe huɗu na yamma".dariya sukayi ye Arwa tace"aunty wallahi gaskiyar shi".mommy tace"gaskiya ku tafi dan dare nayi". Khadija ta tashi tana cewa"Allah ya kiyaye hanya".dukka suka ce"Ameen ya Allah".Arwa da nasrin har wurin mota suka rakasu tukunnan se nasrin tace"yanzu yaushe zamu kara haɗu wa". murmushi tayi tace"karki damu nan kusa zamu haɗu".Arwa ta rungume tace"in munyi hutu zamu zo ki shirya mana wuri".se kuma Arwa tazo kusa da kunnen ta tace"se kuma a ajiye mana ciki ko yaro". Khadija bugun waya ta mata tana cewa"ke dai Allah ya shirye ki".Nasir ne yayi horn se ta rungume su sukayi sallama ta shiga mota suka tafi,a hanya ya tsaya a chemist ya saya magani se ya dawo haka har suka isa gida kowa ya wuce ɗakin shi.

Se bayan sallar Isha ne dukkan su suka dawo parlour suka zauna,kallo sukeyi se Nasir yace"Khadija ɗauko min laptop nawa a ɗaki na".tashi tayi ta wuce ɗakin shi ta ɗauka laptop ɗin ta bashi se ta zauna,bayan minti kaɗan ya kara cewa"Khadija mika min ruwa a fridge".tashi tayi ta ɗauko mishi ruwa ta buɗe mishi se ta mika mishi,zama tayi tana kallon tv se ya kara cewa"Khadija ɗauko min waya ta a ɗaki".kallon shi tayi tace"Ni gaskiya bazan jeba,ba ɗazu na ɗauko maka laptop ba mesa baka ce na kawo maka harda wayar ba".kallon ta yayi yace"baza kije bane".tashi tayi tace"eh bazan jeba".gwaɗa kai yayi ya tashi ya fara zuwa kusa da ita se ta fara yin baya shi kuwa se gaba yake har suka isa bango shi kuwa ya matsa kusa da ita sosai har suna jin nunfashin juna se ya kara cewa"baza ki jeba".duk da zuciyar ta na buga wa dan tsoro amma bai hana ta cewa"eh bazan jeba".tana gama maganar ji tayi bakin shi akan nata,zura ido tayi ta kasa motsi,shi kuwa kawai haɗa bakin su yayi se yaja lip nata na ƙasa da bakin shi se ya sake,ita kuwa ta kasa motsi ma,Nasir ne yace"zaki je ko baza kiba".da sauri ta hau steps ɗin ta shiga ɗakin shi tana taɓa bakin ta tana mamaki,ɗauka wayar tayi ta sauko mishi da ita ta mika mishi se ya karɓa,komawa ɗakin ta tayi,tayi wanka tasa wando da rigan bacci ta kwanta wai yau a ɗakin ta zata kwana amma ta kasa kawai se ta ɗauke hulanta tasa ta shiga ɗakin shi da sallama,baya ciki ɗakin kawai se ta wuce ta side data kwanta jiya ta kwanta har bacci ya kamata baizo ba.naair yana gama abinda yake ya kashe komai ya wuce ɗakin shi,yana shiga yaga Khadija ta dunkulu tana jin sanyi,bargo yasa ya rufe ta se ya shiga toilet yayi wanka yazo shima ya kwanta.

❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now