khadeejah 💙 27

23 4 0
                                    

Tunda safe da sukayi sallar asuba Khadija ta wuce ɗakin su Arwa duk da Nasir yana nan.

Tana zaune tana shan tea nasrin tace"karfe nawa ne Flight nakun?". Khadija tace"karfe biyu".Arwa tace"shine kika shirya da wuri se kace zamu cinye ki in kin Kara wani yini a garin mu". Khadija ta kalle ta tace"oho dai nima ai nayi missing na garin mu". nasrin tace"kwana nawa kika yi har zaki ce kin gaji da garin mu"Khadija tace"na gaji nima zanje na kalle mama na".Nasir da sallama ya shigo ɗakin suka gaisa se ya kalle Khadija yace"zo muje ki raka Ni".da sauri ta tashi ta wuce tana cewa"muje".dariya sukayi sannan Nasir ya bita a baya suka wuce side nashi kallon shi tayi tace"nan ne zan raka ka?". gwaɗa kai yayi yana jata ɗaki yana cewa"wani abu zaki bani".tura baki tayi tace"indai maganin kane wallahi Ni na gaji duk kasa jikina yana ciwo". murmushi yayi ya jata kusa dashi yace"ba yanzu ba se munje Maiduguri yanzu wani abu zaki bani". gwaɗa kai tayi se tace"me ne zan baka ?".sake ta yayi yace"bani cup a toilet".wani kallo ta mishi se tace"dan in ɗauko maka cup ka kira Ni". gwaɗa kai yayi yace"kekam ki je mana".tura baki tayi se ta wuce toilet ɗin,tana shiga taga wani box me kyau Black da 🌹 rose me kyau sosai,zama tayi ta buɗe taga wani box a ciki, murmushi tayi ta buɗe box ɗin ta kara ganin wani box,juya wa tayi ta kalle Nasir yayi murmushi se ta juya ta cigaba da ɓude wa se ta buɗe taga wani sarka me kyau sosai da bracelet da ring nashi tashi tayi se taji Nasir a bayan ta  ya karɓa yabuɗe sarkan yakai hannun shi ta gaba ya sa a wuyanta se ya kalle ta ta mirror suka haɗa ido se tayi murmushi shima yayi se yayi perking na wuyan ta yace"yayi Miki kyau sosai". murmushi tayi tace"thank you yayi kyau sosai".juyar da ita yayi yace"i have another surprise". murmushi tayi se ya cire wani box daga aljuhun shi ya mika mata se ta karɓa yace"naga kina son speechless sosai shine na saya Miki Black favorite colour naki".zaro ido tayi ta buɗe box ɗin taga key na mota ne bata san lokacin da tayi hugging nashi ba dan farin ciki tace"na gode sosai thank you thank you thank yo--".kawai taji ya haɗa bakinsa da nata ahankali yake motsi da bakinshi it is so good that bata san sanda ta fara kissing back ba.haka suka cigaba da yi har sanda sukaji nunfashin su na yanke wa tukunnan yayi pulling bakin shi a hankali, Khadija ta rufe fuskar ta da hannun ta, murmushi yayi yace"se kace da gaske".dariya tayi ta fita daga toilet ɗin se yace"se munje motar yana Maiduguri". gwaɗa kai tayi.

Bayan sunyi sallar azahar suka shirya suka sallame su mommy su Arwa suka raka su har airport.arwa kamar tayi kuka tace"zanyi missing naki sosai wallahi". Khadija tayi sad smile tace"nima haka abokiyar faɗa".dariya tayi sukayi hugging juna sannan nasrin ma tazo tayi hugging nata se suka  wuce jirgi.karfe uku suka isa Maiduguri driver yaje ya ɗauke su suka wuce gida.suna isa Khadija taga speechless black a pake da sauri ta sauka ta kalle Nasir tana cewa"wannan ne?". murmushi yayi ya gwaɗa kai da sauri ta je ta dudduba se ya ja hannun ta yace"ki huta tukunnan se anjima mu fita". gwaɗa kai tayi suka wuce ciki wai sam se sunyi wanka tare ita kuma ta ƙi haka ya hakura ya barta ta wuce ɗakin ta tayi wanka tasa wani t-shirt daidai guiwa da wani jeans ta kama gashinta ta sauka ta faɗa musu abinci sannan ta zauna daidai lokacin ya fito ya zauna yana cewa"harkin dafa abinci Sarkin abinci". murmushi tayi tace"eh dan yunwa nake ji shesa".suka ci abinci bayan sun gama ya taya ta wanke wanke sannan suka shirya ta fita da motar ta se farin ciki take da murna suka zagaya gari.  kallan shi tayi tace"yaya Nasir muje in kalle mama na nayi missing nata". gwaɗa kai yayi tayi murmushi suka wuce gidan.

Suna isa aka buɗe musu gate tayi parking suka fita tayi knocking kofar Yasmin tazo ta buɗe da mamaki tace"ke da kike Abuja yaushe kika dawo". murmushi tayi tace"yau na dawo mama tana nan?". gwaɗa kai tayi se ta kalle Nasir yana fito wa daga mota tace"ina wuni"."lafiya lau Yasmin ya kike?"."lafiya lau".ta faɗa tana matsa musu daga kofar suka shiga ciki suka zauna, Khadija tace"nikam bari naje naga mama na". murmushi yayi ya gwaɗa kai se ta fita da sauri ta shiga ɗakin mama tayi hugging nata tace"Finally". dariya mama tayi tace"gaskiya fa Finally Khadija ce a gidan mu".ta sake ta tana cewa"mama yau muka dawo nace bari na zo na ganki".mama tace"gaskiya kam dan da baki dawo ba binki zanyi ai".dariya tayi Yasmin tace"yaushe rabon ki da zuwa gidan nan tunfa lokacin da mijin ki yayi tafiya ko?". gwaɗa kai tayi tace"school ne yake hana Ni zuwa ai". Yasmin tace"mama yaya Nasir dai yana parlour dan naga alama matar shi bata faɗa Miki ba".mama ta tashi tana cewa"shine baki faɗa min ba kika barshi shi kaɗai".mama ta wuce parlour suka gaisa da Nasir Khadija  ta fito tana cewa"mama bari mu tafi dan dare yana yi ko?".ta tambaya tana kallon Nasir, murmushi yayi yace"gaskiya dare yana yi bari mu tafi".mama tace"to Allah ya kika ye hanya".Ameen suka ce suka wuce wurin mota suna shiga me gadi ya buɗe gate suka wuce gida.

Suna isa Khadija ta shiga ɗakin ta tayi sallah sannan ta zauna tana danne danne a waya se bayan sallar Isha ne ta shirya bacci se ta fita kitchen taje ta haɗa tea tasha tana zaune a parlour Nasir ya shigo daga waje yazo ya zauna kusa da ita, kallon shi tayi tace"yaya Nasir daga ina kuma?". murmushi yayi yace"naje Duba wani abu ne a waje". gwaɗa kai tayi ta cigaba da kallon tv juya kanta yayi yace"baza ki kwanta ba,gobe fa kina da school". gwaɗa kai tayi suka wuce ɗakin shi,ya shirya bacci ita kuma tana danna wayar ta harya gama yazo ya kwanta yace"kiyi bacci kina da school". gwaɗa kai tayi ta ajiye wayar ta ta kwanta shi kuma laptop nashi ya ɗauka ya fara aiki,se bayan kusan awa ɗaya ya kashe laptop ɗin ya juya yaga Khadija wanda ke bacci hankalin ta kwance, murmushi yayi ya shafa fuskar ta yazo kusa da ita a fili yace"I don't know what you did to me but I think I'm in love with you". kissing na goshinta yayi ya kwanta yaja ta kusa dashi har bacci ya ɗauke shi.

❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now