Yau sati biyu bayan sa ranan Khadija da Nasir.khadija kuwa rayuwar ta take harma ta manta da tayi aure.umar kuwa se nace mata yake amma taki ta bashi fuska duk da dai tana shiga motar shi ya kaita har gida ko makaranta.nasir kuwa har ya dawo Maiduguri ya cigaba aikin shi.nasir ya kara sayan sabon gida dan Abba yace mishi ya kara sayan wani se yakai Khadija ta gani.a yanzu ya saya gidan gobe ze je gidan su Khadija gaishe da maman ta se jibi ya kaita gidan ta gani in komai ya mata.
Yana zaune a office nashi yana aiki se aka buɗe kofar office nashi,ɗaga kai yayi se yaga abokin shi Umar ne.umar murmushi yayi yazo ya zauna yana cewa"Nasir kenan waton har ka dawo amma baza ka zo wurina ba".Nasir yace"Umar ai se kayi knocking Koh,kuma da kake ciwa banzo wurin kaba ai kai ya kamata kazo wurina kamin jaje".Umar dariya yayi yace"malam maida wukan nasan nayi laifi toh ayi hakuri". murmushi kawai Nasir yayi mishi.umar yace"Ni yaushe ne auren".Nasir yace"wata ɗaya da sati biyu".Umar yace"kace ka kusa angon cewa mu kuwa gamunan".Nasir ne yayi dariya yana cewa"toh dai gonda ka cere mata kafin a maka irin nawa".Umar ma dariya yayi yace"gaskiya kam ai ina da wanda nake so amma taki ta yarda ta soni amma dai zan cigaba da gwada wa".Nasir ruwa ya sha ya ajiye cup ɗin kafin yace"hmm toh tunda bata sonka dole ne".Umar murmushi yayi yace"man yarinyar ta haɗu nesa ba kusa ba,gata na jan aji ga rigiba ga hankali".Nasir shi dariya ma abun ya bashi.umar ne ya tambaya"ka taɓa kallon matar kan ne",Nasir yace"a'a amma gobe zan je gidansu gaishe da mamanta".Umar yace"kace gobe zaka kalle amarya".shuru ya mishi Umar yayi dariya haka dai suka cigaba da hira har Umar ya tafi gida,shima Nasir yana gama aiki ya wuce gidan shi tsoho, toilet ya shiga yayi wanka ya fita parlour ya zauna,wayar shi ta fara ringing dauka yayi Arwa ta cikin wayar tace"yaya Nasir ina wuni". murmushi yayi yace"lafiya lau Arwa,ya gida"."lafiya lau,yaya Nasir kace wurin Khadija ne".Nasir yace"a'a se gobe".daɗi taji tace"yaya in kaje ka karɓa min number nata".yace"ton shikenan,yasu mommy".tace"kowa lafiya suka ce a zaishe ka"."toh ina ansawa".katse wayar yayi dan an kira sallah,tashi yayi alwala ya wuce masallaci,bayan an idar da sallah ya dawo ya dafa abinci yaci se ya ɗan danna waya har yayi bacci.
Nasir ne ya dawo daga masallaci yayi wanka yasa men black material da hula ya fesa turare yayi kyau sosai,haka ya ɗau makullin motar shi ya wuce office,haka dai yayi ta aikin shi.
Khadijah 💙
Kicin take tana girki,suna hira da Habiba wanda take zaune akan kicin island ɗin,Habiba tace"Khadija nikam yaushe zamu je gidan aunty A'isha ne".juyawa tayi ta kalle ta se tace"muje ko ran asabar".Habiba tace"kamar dagaske,kena kullum se makaranta". Khadija tace"toh ai ran asabar ba makaranta Koh".haka dai sukai tayi,suna gama girki ta wuce ɗakin ta tayi sallar azahar t kwanta bacci.Nasir💙
Yana gama aiki yayi fice War shi,ɗaya shiga motar shi ya ɗaga waya ya kira Abba suka gaisa se yace"Abba yau zanje gidansu Khadija ta ina ne hanyar".Abba kwatanta masa yayi se sukayi sallama ya katse wayar,haka dai har ya iso gidan me gadi ya buɗe masa kofar yayi parking suka gaisa se yayi knocking kofar parlour,bayan minti kaɗan se Yasmin ta buɗe mishi kofar tana cewa"ina wuni".yace"lafiya lau mama tana nan".tace"ka zauna bari na kira ta".zama yayi ita kuwa ta wuce,yana tunanin Koh itace khadija.haka dai har mama tayi sallama ta shiga parlour, durkusa wa yayi da girmamawa yace"mama ina wuni".mama zama tayi da murmushi tace"lafiya lau,amma ban zane waye ba".Nasir yace"Nasir ne".mama tace"ayyah Nasir ya gida ya aiki". murmushi yayi yace"lafiya lau".tashi ka zauna mana.zama yayi se mama ta fara kiran sunan Habiba,da Habiba ta amsa ce tace"Habiba ze kice wa Khadija ta kawo wa bako ruwa".Habiba shiga ɗakin Khadija tayi wanda take bacci ta buga ta tana cewa"Khadija tashi mama tace Ki kai wa bako ruwa a parlour".tashi tayi tace"Toh".ta ɗauka hijabi dogo tasa ta wuce kicin taɗau ruwa da drinks ta wuce parlour dashi,tana shiga da sallama ta shiga ta wuce wurin Nasir ta ajiye mishi ruwa a gaban shi tana cewa"ina wuni".shi kuwa tunda take shiga idonshi na kanta,kana ganin ta kasan daga bacci ta tashi.amsa wa yayi da"lafiya lau".taga se kallonta yake a zuciyan ta tace"wai wannan maye ne da se kallonta yake".fita daga parlour ta fara yi mama tace"Khadija zo ki taya mu hira mana". juyawa tayi ta tura baki tana cewa"mama Ni bacci nake ji".se ta wuce kayan ta.shi kuwa har ta wuce ita yake kallo, a zuciyan shi yana cewa"Masha Allah".haka dai yasha ruwan wanda se kamshin turaren ta goran take,haka yayi sallama da mommy yace gobe ze zo ya ɗauke Khadija dan ta kalle gida,mommy tace"toh shikenan bari Yasmin ta baka number na Khadija".kiran yasmin tayi ta bashi number na Khadija sukayi sallama yaja motar ya wuce.
Khadijah 💙
Mama ne tace a kira mata Khadija Habiba taje ta tayar da ita tana cewa"se kace wata me ciki kullum se bacci ne aikin ki,toh tashi mama na kiran ki".tashi tayi bata kula taba ta wuce parlour ta zauna kusa da mama tana cewa"mama gani nazo".mama tace"Nasir ne ɗazu yazo kuma wai gobe ze zo ya kaiki kiga gida". Khadija kuwa buɗe baki tayi tana mamaki wai ta haɗu da mijinta ɗazu amma bata sani ba.kallon mama tayi tace"mama Ni gobe makaranta zanje kawai yayi hakuri".mama karkaɗa kai tayi tace"ke dai Allah ya shirye ki,ai kuwa se kinje".tura baki tayi ta fice daga parlour mama kuwa Binta da kallon mamaki tayi harta wuce.Safe nayi Khadija ta shirya tasa wani abaya brown ta shafa powder da lip gloss taɗau jaka tasa wayar ta da littafi ɗaya ta wuce, ɗakin mama taje ta buɗe kofar tana cewa"mama Ni na tafi makaranta".mama da mamaki ta kalle ta tana cewa"bance Miki Nasir ze zoba".tura baki tayi tace"mama muna da class wallahi".se ta rufe kofar ta fita daga gida,ta hau napep ta isa makarantar,class ta wuce direct ana gama lectures su anam sukace zasu tafi, Khadija tace"wallahi ba inda zaku se anjima se mu fita dukkan mu". Maryam tace"kawai dan kina gudun mijinki se ki haɗa da mu".anam ma tace"mudai ki barmu mu tafi se ki jira se anjima kije gida".tafiya suka fara yi se ta kama hannun su tana cewa"wai me haka ne,amma ai dakune zan jira ku ai".wayar tane ya fara ringing se taga number ce se taki ɗaura,ya tsinke se aka kara kira,dauka tayi se taji ana cewa"ki fito ina kofar makarantar ku".sauke wayar tayi ta duba number se ta kara mayarwa tace"kai waye".bai bata lokaci ba yace"mijinki". zuciyar tace tayi dum.katse wayar yayi ita kuwa mamaki take.anam tace"lafiya Koh?". Khadija ta kalle ta tace"wai mijina ne ya kira Ni wai yana waje".Maryam murmushi tayi tace"toh alhamdullilah tunda yazo se kowa yayi hanyar shi". Khadija tsaki taja tace"waya ce miki zuwa zanyi".anam ne ta rike hannun ta tana jan ta suna tafiya tana cewa"wallahi se kin tafi". Khadija se kokarin kwace hannun ta take yi amma sun haɗu sun rike ta haka har suka fita wurin gate,suka ga wani mota korar ford baƙi,horn yayi musu wanda ya nuna shi ne a motar,sake mata hannu sukayi ta harare su tana cewa"wallahi Allah se nayi maganin ku".dariya sukayi suna cewa"ai dan mun kawo ki". Khadija tace"Toh ai bazan jeba".anam kara damko hannun ta tayi ta jata har wurin motar,Nasir ne ya sauke glass na motar yayi wani kyau na face cap da t shirt blue, murmushi yayi wa anam yana cewa"thank you".ai kuwa anam ta samu karfin buɗe kofar tasa Khadija a ciki tana cewa"ba komai, Khadija se gobe".tsaki me karfi taja mata se anam ta wuce wurin maryam.nasir ya ɗaga glass na motar ya fara tuki,sanda sukayi nisa se yace"Khadija ina wuni".kallon shi tayi se tayi"ina wuni".bai ce komai ba, ahankali tace"mutum yasan ba amsa gaisuwa ze yiba to mesa ya tambaya".ya jita sarai amma se ya cigaba da tafiya har suka isa wani gida me kyau sosai, parking a kofar dan ba kowa a gidan,fita yayi itama ta bishi a baya.
Buɗe kofar gate ɗin da makulli suka shiga,paint na gidan milk colour ne.kuma beni ne,haka ya kara muɗe kofar parlour suka shiga,gidan yayi kyau sosai dukka ba komai illa labule da carpet.a kasa akwai parlour se kicin da dining se ɗaki daya,a sama kuma akwai parlour ɗaya da ɗaki biyu,kuma ko ina akwai carpet da labule.haka ta gama zagaya gidan gaba ɗaya se ta kalle shi tace"mu tafi".gwaɗa kai yayi suka fita ya rufe kofofin gaba ɗaya suka shiga mota,ze kunna motar kenan wayar shi ta fara ringing,dauka yayi se yaji Arwa tace"Allah yasa kuna kusa da Khadija".mika mata wayar yayi kallon shi tayi kafin ta karɓe wayar tasa a kunne,Arwa tace"Khadija Ni sunana Arwa ƙanwar yaya Nasir".kallon shi tayi se tace"ayyah ya kike,ya su mommy"tace"lafiyar su kalau".haka dai sukai ta hira Nasir kuwa se tuki yake.arwa tace"ki turamin number naki kinji". Khadijah tace"toh shikenan"sukayi sallama,ta wayar Nasir ta tura number ta wa arwa.se ta ajiye mishi wayar.wani restaurant ya tsaya ya kalle ta yace"me zaki ci".itama kallon shi tayi tace"ice cream".ɗan murmushi yayi yace"ba ice cream anan ai".tace"toh chips da kwai".gwaɗa kai yayi ya fita daga motar,bayan minti kaɗan ya dawo da leda biyu a hannun shi ya ajiye a basa se ya kunna mota suka wuce, wurin ice cream suka tsaya se farin ciki take yace"sauko muje".da wuri ta sauka suka shiga se kallon su ake irin na awwn sunyi kyau sosai a tare.tace a bata chocolate flavor,aka bata se ta lalle shi tace"baka shan ice cream".biyan kudin yayi se yace"ba sosai ba".gwaɗa kai tayi suka fita daga wurin,a hanya ta shanye ice cream nata,suka isa gidan su se ya dauke leda ɗaya ya bata tace"thank you".gwaɗa kai yayi se ta sauka ta rufe kofar motar ta shiga gida,tana isa tagan su dukka a parlour,shiga tayi ta zauna a ƙasa ta buɗe leda hannun ta tana cewa"bismallah".duk suka ce taci kayanta.cinye wa tayi tas se ta tashi ta wuce ɗakin ta tayi sallah ta gama komai ta kwanta bacci.
❤️