khadeejah 💙 19

27 3 0
                                    

Yau sati biyu kenan da tafiyar Nasir, Khadija tayi sati ɗaya a family house se ta koma gidansu tayi sati, kullum tana tafiya makaranta kuma tana zuwa islamiya ranar asabar,ita da Nasir kuwa kullum se sunyi waya amma da faɗa suke gamawa.
Gobe Nasir ze dawo shine Mama tace  Nana ta raka Khadija wurin kitso da lalle.

Khadijah da Nana ne na hango suna fita daga mota, Khadija tasa wani baƙin hijabi ya haska ta Nana tasa material brown da gele baƙi itama tayi kyau suka wuce cikin wani gida.lalle akayi wa Khadija ja da baki dukka lalle yayi kyau sosai bayan sun gama suka wuce gidan kitso akayi musu kitso sosai Khadija ta koma kamar amarya dan daman kullum skin nata glowing yake.bayan sun gama komai suka tsaya a wurin shan mai se taga motar Umar a gabansu,shima ya kalle motar ya sauka dan yaɗau Nasir ne,zuwa yayi wurin glass yayi knocking yana murmushi.khadija ta sauke glass ɗin tayi mishi murmushi tana cewa"ayya Umar ba me motar bane matar shine".Umar da mamaki ya kalle ta se yace"ayyah daman matar shine naɗau shine ai toh ki gaishe shi Koh".gwaɗa kai tayi se yayi waving da hannun shi wa Nana itama tayi mishi se ya wuce motar shi.nana data bishi da kallo tace"wai mesa duk abokan mijinki sun haɗu ne". Khadija tace" hmm ke dai ƙe faɗa".suka gama shan mai se ta wuce family house sukayi parking direct dakin su hafsat suka shiga,suna shiga taslima tana zaune tana kallon tv tace"nifa na ɗau wata amarya ce ta shigo". Khadija tayi wani juyi tace"toh ba amaryar nace?".Nana zama tayi tace"heyyyy Ni na shiga uku damawa yaya Nasir kikayi wa juyin nan ba muba". murmushi tayi tace"bari na je gida mama tana jira na,in hafsat ta dawo kice ina gaishe ta". taslima tace"toh zata ji ki gaishe da mama".gwaɗa kai tayi ta fita se ta haɗu da mommy,zuwa kusa da ita tayi tace"mommy ina wuni". mommy murmushi tayi tace"lafiya lau irin wannan kyau haka ko angon namu ze dawo ne?".ɗan rufe fuskar ta tayi alamun jin kunya se ta gwaɗa kai mommy tace"ka jita wai kunya na take ji". Khadija dariya tayi tace"haba dai mommy ke zanji kunya kawai dai maganar kine ya bani kunya". mommy tayi dariya se Khadija tayi waving na hannun ta ta wuce mota se gidan su.

Tana isa direct dakin mama ta shiga ta zauna akan gado kusa da mama tana cewa"mama gani na dawo".mama murmushi tayi tace"enmata kinga yadda kikayi kyau kuwa ko kitso ne yake haska ki"."daman da haske na nake mama".dariya mama tayi tace"ke dai yarinyar nan ko".se mama ta mika wani abu tace"gashi gobe kisha kafin ki kwanta ze kwantar Miki da hankali". Khadija kallon tuhuma tayi wa mama se mama tace"ya da wannan kallon fa". Khadija tace"mama ai hankali na a kwance"mama ta daura hannun ta a kafaɗar Khadija tace"kidai sha kinji nasan baza kimin karya ba zaki sha Koh".gwaɗa kai tayi se mama ta shafa mata kai tace"yawwa er albarka gobe se Habiba ta raka ki kuje ku jira mijin ki ya dawo".gwaɗa kai tayi se mama tace"kinsan Khadija zaman aure se hakuri nasan ki da hakuri kinji kiyi biyayya wa mijinki". Khadija tace"ba karamin hakuri nake ba ai yanzun ma".mama tace"ban tambaye kiba kawai shawara nake baki". murmushi tayi ta tashi tana cewa"thank you very much"tayi perking na cheeks na mamanta tana cewa"I'll miss you".mama tayi dariya tace"me too er auta na". Khadija fita tayi ta shiga ɗakin tana cewa a fili"gobe kuma za'a koma gidan jiya".zama tayi tana kallo a wayar ta har lokaci ya tafi sosai.habiba ce ta shiga ɗakin tana cewa"ke haryanzu halin ki na zaman ɗaki yana nan Koh?". Khadija kallon ta tayi tace"toh ya za'ayi abu ya zama hali".Habiba murmushi tayi tace"toh Allah ya shirya". Khadija tace"Ameen Habiba".haka dai sukayi ta hirar su har dai lokaci yayi ta kwanta tayi bacci da tunanin gobe Nasir ze zo.

Wayar tane ya fara ringing wanda ya tayar da ita daga bacci ta duba taga karfe biyar da rabi na safe,tsaki taja da taga Nasir ne ke kira amma se ta amsa,da haushi take magana tace"wai Malam wannan wani irin abune kana wani gari ma Amma bazaka barni na huta ba".Nasir da wani irin Muryar bacci yayi deep and husky yace"eemmm kewai kullum baki da aiki se masifa, na kira kine dan ki tashi kiyi sallah se kuma yau tuwo da vegetable soup nake so ki dafa min".tsaki taja tace"bazan yiba". murmushi yayi yace"karkiyi in Kinga dama nidai i already said what I want and I expect you to cook it before I come home"katse wayar yayi kafin tayi magana,tsaki taja ta tashi tayi alwala tayi sallah kawai se tayi wanka tasa wani atampa fitted me kyau ta shirya ta fita duk da yau bazata je makaranta ba amma ta shirya da wuri dan taje ta fara shara ko ta buɗe kofa me aiki tayi.

Khadeejah💙Where stories live. Discover now