khadeejah 💙 9

22 2 0
                                    

Tashi tayi ta wuce toilet tayi wanka ta shirya da hijabi dogo baki ta fesa turare ta ɗau pen ta fita ta shiga ɗakin mama da sallama,mama ta amsa se Khadija tace"mama ina kwana".mama  tace"lafiya lau Khadija,exams zaki?".gwaɗa kai tayi se aunty Samira ta shiga ɗakin, murmushi tayi tace"amarya makaranta za'a je?".tura baki tayi tace"mama kinga aunty ko".dariya sukayi se Khadija tace"Ni na tafi".suka yi a dawo lafiya se ta wuce ta shiga napep ya kaita makaranta.tana isa ta wuce suka zana jarabawar se ta fito dasu anam suka wuce gidan su anam dan yau zasu fara raba ankon auren anam ɗin.suna isa ɗakin anam suka shiga suka zauna,me aiki ta kawo musu abinci suka gama ci se suka je wurin yayan anam ɗin,da sallama suka shiga se ya amsa,anam ta shiga se tace"yaya ka ara mana motar ka zamu kai anko". kallon ta yayi yace"kin iya tuki ne?".anam ta tura baki tace"toh ai bani zan tuka ba Khadija ce zata tuka".gwaɗa kai yayi se ya bata makullin.fita sukayi Khadija ta shiga ta kunna motar suka wuce.

Khadijah ta iya mota amma ba wanda ya sani a gidan su se ƙawayen ta.haka sukai ta raba ankon gida gida har magriba tayi se suka tsaya a gidan gyaran jiki dan ayi ma Khadija,da wuri kuwa suka gama se suka koma gidan su anam ta ajiye motar sukayi sallama akan gobe zasu karasa rabawa.bayan sunyi sallama ta fita da Maryam da wata kawar anam ɗin suka shiga napep kowa yayi gidan su.tana isa ta shiga parlour da sallama ta same kowa suna zaune, gaishe su tayi ta wuce ɗakin ta se taji aunty Ummu tana cewa wai gobe za'a kawo kayan ta.tana shiga ɗakin wanka tayi ta kwanta bacci.

Da safe ta tashi tayi wanka kamar kullum tasa hijabi blue ta fesa turare ta fita wurin mama,da sauri tace"mama na tafi makaranta".bata tsaya taji me zata ce ba tayi fice warta.tana isa ta wuce suka zana jarabawa kaman jiya haka suka wuce gidan su anam suka karɓe motar yayan nata suka wuce.haka sukai ta raba ankon,sunzo wuce wa a ta wani wuri se  anam tace"Khadija wannan ba mijinki ba?". Khadija taɗan juya se ta kalle Nasir yana fita daga mota,se tace"Toh se na faɗi na karya wiya".Maryam tace"da wata suke fa". Khadija wani tsayar da motar tayi wanda sanda suka je gaba tukun suka dawo baya.ta juya ta kalle baya.maryam dariya take har ta kwanta akan seat na motar.anam tace"wannan irin parking haka,tun kafin ki shiga gidan kin fara kishi". Khadija tsaki taja tace"wallahi ke dai Maryam yar iska ce".Maryam kasa magana tayi dan dariya,anam kuwa fita tayi taje wurin Nasir,tana zuwa wurin shi tace"ina wuni".juya wa yayi se yayi murmushi yace"lafiya lau,kawar Khadija Koh?".gwaɗa kai tayi se tace"Khadija tana cikin motar ai".kara murmushi yayi yace"toh ki gaishe ta". murmushi tayi ta gwada kai se sukayi sallama ta koma motar ta shiga, Khadija harararta take tace"munafuka toh me kika faɗa mishi".anam murmushi tayi tace"wai yace in zaishe ki".shiru tayi taja motar suka wuce,haka dai har suka gama raba ankon zaba ɗaya suma suka ɗauka nasu ta mayar da motar se kowa yayi hanyar shi.

Tana isa gida taga mutane sunzo dayawa kawai ta shiga ɗakin se taga cousins nata daga Yola sunzo.maimuna da ummati ne suke zaune a ɗakin da gudu taje ta rungume su suma se farin ciki,zama sukayi suna hira se ummati tace"amarya kenan kinga yadda kika kyau kuwa".maimuna tace"ke dai ƙya faɗa". Khadija tace"oho dai kuyi ku gama".dariya sukayi se Habiba ta shiga tana cewa"amarya wai kizo kiga kaya". Khadija tace"a'a ba sena gani ba".Habiba zama tayi tace"akwati set shida aka kawo se set biyu na iyaye". Khadija gwaɗa kai tayi ta tashi ta shiga bayi tayi wanka ta fita ta kwanta,su kuwa hirar su suka ciga ba dayi.haka dai kowa ya gaji ya kwanta.

----------------++++------------------
Yau saura kwana biyu Khadija ta tare a gidan nasir.se shirye shirye ake yi,an gama komai dangi kowa ya hallara a maiduguri.haka dangin Nasir ma kowa ya zo.amarya kuwa se shirya ta akeyi ba wasa,ba kalan maganin da ba'a bata se kara kyau take gashi kullum se taje gyaran jiki,dangi kowa farin ciki yake daga dangin miji har na matar.ta gama exams nata.

Khadijah ce take ta ce gashin ta a gaban madubi,se Nana taja tsaki tace"Madam ke fa muke jira kin tsaya kina bata mana lokaci.kallon ta tayi tana cewa"ke kimin a hankali mana se kace kwana zanyi".tana faɗan haka ta ɗauka ribbon nata ta kama kai tasa hijabi suka fita.kiran Yasmin tayi a waya se ta amsa, Khadija tace"kina gida ne".Yasmin tace"munje karɓo kaya daga wurin tela ne". Khadija tace"toh shikenan dama kaimu salon zakiyi".sallama sukayi suka je bakin titi suka tare napep ya kaisu salon,suna isa Khadija aka fara wanke wa kai,haka dai aka mata komai na amare aka gama aka fara yiwa Hafsat se wayar Khadija ta fara ringing, dauka tayi,ta cikin wayar Nasir yace"kina ina".tace"ina salon".yace"tura min address ɗin bari na zo".kafin tace toh ya katse wayar,tsaki tayi me sauti se ta tura mishi address ɗin,bayan an gama musu dukka se suka zauna suna jiran shi,bayan minti kaɗan se yazo da motar shi wani baƙin Mercedes,sauke glass ɗin yayi se suka kalle shi,Hafsat tace"wayyo Allah kai ya haɗu wallahi".bata kula taba suka shiga motar,su hafsat da Nana da taslima suka gaishe shi ya amsa se ya kalle Khadija wanda take kallon waje yace"Khadija ina wuni".juya wa tayi ta kalle shi tace"ina wuni".bai kula taba ya kunna motar shi ya fara tafiya,ita kuwa haushi ne ya kamata.se tace"ba gida zamu je ba wurin lalle zamu je".yace"toh ki nuna min hanya".gwaɗa kai tayi ta dinga nuna mishi har suka isa,da suka isa ya cire kuɗi ya mika mata,kallon shi tayi se tafara kokarin buɗe kofar motar se ya rufe,juyawa tayi ta mishi wani kallo se ya mika mata kuɗin yace"gashi ki karɓa".shiru tayi se Hafsat tace"Khadija ki karɓa mana baki san zamuyi dare ba".ta kusan minti ɗaya bata karɓa ba kawai kuma se ta karɓa ya buɗe kofar suka fita.tana fita taja tsaki suka shiga gidan,basu suka gama lalle ba se bayan sallar Isha,Tahir suka kira a waya yazo ya ɗauke su dan dare yayi,haka suka jira shi har yazo suka shiga motar suka gaisa dukka,Tahir yace"amarya kinga yadda lalle yayi kyau kuwa".dariya tayi tace"yaya Tahir ba daga lallen bane daga me sanye da lallen ne".shima dariya yayi haka har suka isa gidan su Khadija ya sauke su ya wuce dan su Hafsat sun dawo da kwana a gidan su Khadija.shiga sukayi kowa busy haka suka shiga ɗakin ta suka samu su maimuna sun haɗa majalisa a ɗakin ta,suna kallon su ummati tace"kai Masha Allah kinga yadda lalle tayi kau kuwa".tace"thank you".shiga bayi tayi wanka tayi alwala ta fito tayi sallah se taslima ta kawo abinci suka ci suna hira,wayar Khadija ta fara ringing se ta dauka,amra ta cikin wayar tace"albishirin ki". Khadija tace"goro".amra tace"ina kofar gidan ku". Khadija da mamaki tace"wasa kike yi Koh".amra tayi dariya tace"ki fito idonki ya gane Miki".ai kuwa Khadija tashi tayi ta wanke hannun ta da wuri taɗau wani karamin gelen dake kusa da ita ta fita,tana fita kuwa ta hango Arwa da nasrin a jingine a motar Nasir,da gudu taje ta rungume su tana cewa"wayyo Allah wallahi naɗau wasa kike min".Arwa da farin ciki tace"ai kuwa kin ganNi ai da gaske".dariya tayi tace"ya kuke ya gida, Nasrin ya kike?".nasrin murmushi tayi tace"lafiya na lau,kinfi kyau ma a zahiri". Khadija dariya tayi tace"ke ma haka ai enmata,yasu mommy".Arwa tace"lafiyar su kalau suka ce a zaishe ki". murmushi tayi tace"ina amsa wa".Muryar Nasir taji yana cewa"wannan wani irin gele ne haka".kallon shi tayi yana kan zagaya wa wurin su se tace"ina wuni".yace"lafiya lau,tambayan ki nake".ita mamaki take yau ya amsa gaisu wanta.arwa ce ta buga ta tana cewa a hankali yadda su kadai zasuji"kiyi sauri ki koma gida se ranan aure zamu zo mu yini Miki kinji".gwaɗa kai tayi da sauri ta shiga cikin gidan tana tunanin toh ma mesa ta shiga gidan da ta tsaya ta nuna mishi ita ma tana da taurin kai ai.haka dai ta shiga gidan mama ta kira ta kicin,shiga tayi ta same su ta gaishe su gaba ɗaya se suka amsa,mama tace"kin sha abinda na baki ɗazu".gwaɗa kai tayi se mama tace"je ki na ajiye Miki wani a cikin drawer a ɗakin ki".gwaɗa kai tayi ta fice daga kicin ta shiga ɗakin ta ta buɗe drawer ta cire se tasha,tana gama wa tace wa en ɗakin"dan Allah ku kwanta kuyi bacci Koh ku rage murya".Nana tace"karki damu zaki neme mu ki rasa ai jibi". Khadija tsaki taja ta kwanta har bacci ta sace ta.


❤️

Khadeejah💙Where stories live. Discover now