Cikin Khadija yayi wata tara,dakyar take tashi dan cikin yayi ƙato sosai gashi kowa yana cewa twins zata haifa amma taki taje tayi scan.sunyi graduation nasu kuma alhamdullilah ta gama komai nata Duk da dai tace bazatayi bautan ƙasa ba.
Tana zaune akan carpet ta baje da babban ciki tana kallon tv.wayar ta ne ya fara ringing ta ɗauka tana cewa"badai kin haihu ba?".Anam ta cikin wayar tayi dariya tace"ai na ma daɗe,to dai da asuba na haihu na samu baby girl". Khadijah ihu tayi tana farin ciki take"alhamdullilah Allah ya raya mana baby".Anam tayi murmushi tace"Ameen kema Allah ya sauke ki lafiya"."Ameen".ta faɗa tana kokarin tashi.anam tace"kuma wallahi na yafe Miki zuwa". Khadija tace"na isa daman,yanzu ma fa dakyar nake tafiya".Anam tace"anya lokaci baiyiba kuwa"."hmm ki rufa min asiri saura kwana kaɗan dai".ta faɗa tana hawa steps dakyar.anam tace"Allah ya raba lafiya"."Ameen,ki shafa min kan baby".anam tayi dariya tace"an gama".sukayi sallama sannan ta katse wayar ta shiga ɗakin ta ta kwanta tana jin yau fa ciwon daban ne amma ta mantar tayi bacci.
Nasir bayan ya dawo ya same ta tana bacci se kawai ya wuce ɗakin shi yayi shirin bacci shima yazo ya kwanta yana tausaya wa Khadija dan tana shan wahala sosai.
Tun safe Khadija take jin cikin nata kamar yana kara sauka ƙasa amma haka ta daure tayi wanka Nasir ya shigo ɗakin ta yazo kusa da ita yana cewa"anya lafiyan ki kuwa?". murmushi tayi tace"me ka gani?".zama yayi ya shafa cikin ta yana cewa"ko baby ne yake damun ki?". karkaɗa kai tayi tace"ah ah kawai dai na gaji ne shesa". gwaɗa kai yayi suka zauna suna ta hira dan yau ba aiki.
Sanda aka kira sallar azahar sannan Nasir ya fita Masallaci, Khadija kuwa ji tayi labour yazo mata tayi dauriya amma ina abun yafi karfin ta ta fashe da kuka ta tsuguna tana ihu tana cewa"wayyo yaya Nasir kazo ka kaini asibiti zan mutu!!!".tana ta ihu ta kasa tashi.sanda aka idar da sallah Nasir ya dawo gidan yana shiga yaji ihun ta da sauri ya wuce ɗakin ya same ta a kwance tana ihu.da sauri yazo yana cewa"sannu bari mu tafi asibiti".kuka take tace"kayi sauri zan mutu!!".ɗaukan wayar ta yayi ya kira Yasmin ta amsa sannan yace"yanzu zamu tafi asibiti da Khadija ki faɗa wa mama".bai tsaya yaji me zata faɗa ba ya katse wayar ahankali ya taya ta tashi ta kara fashe wa da kuka haka dai dakyar ya kaita mota sannan ya ɗauko abunda za'a bukata suka wuce asibiti.
Suna isa ya kira nurses suka shigar da ita labour room direct,Nasir ya zauna a kofar,chan bayan minti kaɗan su mama suka iso dasu mommy da Yasmin da nana.mama tace"ya ya haryanzu bata haihu ba". gwaɗa kai yayi sannan yace"eh haryanzu".kara sauke kanshi.can sukaji tana ihu tana cewa"Ni ku kira min mijina!!!".anyi anyi ta hakura amma ina wai sam Akira mata mijin ta.wata nurse ta fito tana cewa"waye mijin ta?".Nasir tashi yayi yace"ganinan". nurse ɗin tace"matar ka tana so ta kalle ka". gwaɗa kai yayi suka shiga tana kwance tana ta kuka tana kallon shi ta kira shi da hannun ta se yazo ya rike hannun ta kamar yayi kuka se tace"yaya Nasir zan mutu dan Allah ka yafe min".Nasir ya karkaɗa kai yace"ba inda zaki je tare zamu zauna".likita tace mata tayi nishi dakyar tayi nishi alhamdullilah yaro ya fito zata sauke nunfashi taji wani nishin kuka ta fara yi tana cewa"yaya Nasir ko na mutu ke sani Ni Khadija wallahi ina sonka,i love you so much,thank you for coming into my life,you changed me you make me the happiest woman on earth,I love you so much!!!".Nasir farin ciki ne ko bakin cike ne bai san me yake ji ba ya kara damke hannun ta.alhamdullilah Khadija ta haife twins na miji da mace,Nasir a labour room ɗin yayi wa yaran huɗuba,na mijin ya samu sunan baban Khadija waton Ahmad za'a kirashi da ahan na macen sunan mommy wato Maryam za'a kira ta da ahana .aka fitar da yara kowa yace Masha Allah wai suna kama da Nasir .aka gama kintsa Khadija tsab sannan aka kaita wani ɗaki akan ta huta kafin a sallame su anjima.
Kowa na zaune ana ta farin ciki duk dangi sunji labari me daɗi.khadija tana zaune tana shan tea ta kasa haɗa ido da Nasir dan ita kunyar shi ma take shi.bayan angama komai aka sallame ta suka wuce gida.suna isa aka ajiye Khadija a ɗakin ƙasa kafin ta warware.mommy ta shigo ɗakin da kwano a hannun ta tace"gashi kisha wannan kunun yanzu zaki warware"."to mommy". Khadijah ta faɗa tana kallon ahana wanda ke hannun ta,hafsat ta karɓe ta tana cewa"Madam ki sha kunun kafin ki cigaba da kallon yaran ki". murmushi tayi ta karɓa kunun tasha tana ɓata fuska.bayan ta gama sha ta ajiye kwanon ta karɓe ahan a hannun Yasmin tana ta murmushi tana kallon shi.se bayan magriba sannan su mommy suka tafi se Nana da Habibah aka bari.nana da Habibah suna parlour Nasir ya shigo ya wuce ɗakin da Khadija take,tana kallon shi ta rufe fuskar ta, Dariya yayi ya zauna a kusa da ita yana cewa"kinji wani abinda naji kuwa?".dariya tayi ta kara rufe fuskar ta se yace"wai wata ne take so na amma fa taki ta faɗa min sanda ta ɗauka zata mutu tukunnan".dariya ta kara yi tace"yaya Nasir bana son tsokana".dariya yayi yaja hannun ta se ta rufe idonta yace"ikon Allah yau kunya na kike ji kuma".ture shi tayi tace"bari in kira mama in ce mata ka shigo ɗaki na". murmushi yayi yace"ki faɗa mana".ya faɗa yana kokarin janta jikin shi da sauri ta ture shi ta tura baki tace"baka san jikina yana ciwo ba".sa hannun yayi ya rike kunnen shi alaman he is sorry.murmushi tayi ta gwaɗa kai sannan tazo kunnen shi tace"i love you Nasir".se ta kwanta a jikin shi murmushi yayi ya shafa kanta yana cewa"i love you too".nana ne ta shigo ko knocking babu da sauri tace"oh sorry na manta kana nan". murmushi yayi ya tashi yace"nazo duba me jiki ne". murmushi tayi se ya wuce ya duba ahan da ahana sannan ya fita.nana ta zauna a kusa da Khadija tace"kinsan ɗazu se ihu kike yi kowa yaji me kike faɗa"."and so,ke baki ji abinda naji bane shesa".dariya tayi tace"sannu Allah ya raya baby ahan da ahana". murmushi tayi tace"Ameen ya Allah".suka shirya bacci Habibah ma ta shigo sannan suka kwanta bacci.
Da safe suka tashi aka haɗa breakfast aka kawo wa Khadija dake zaune tana kallon yaranta,Habibah ta shigo ta zauna ta ajiye abinci tana cewa"ikon Allah yaran nan fa ba guduwa zasuyi ba,kin sa su a gaba se kallon su kike yi".ɗaga kai tayi ta kalle Habibah tace"inna kalle su kawai farin ciki nake ji,se kace a mafarki".Habibah dariya tayi tace"se ki tashi dan ba mafarki kike ba".dariya tayi daidai lokacin Nasir yayi knocking kofar suka ce ya shigo suka gaisa se Habiba ta fita Khadija ta buɗe hannun ta mishi yazo ya shiga jikin ta yayi murmushi yana cewa"ba abinda yake damun ki Koh?". gwaɗa kai tayi se ya sake ta suka fara wasa da yaran Nasir yana cewa"Allah ya tsare ku da rashin jin mamin ku". hararar wasa tayi mishi tace"Ni fa ina jin magana".dariya yayi yace"kin fara ji dai". murmushi tayi se yace"bari naje na ɗauko su Arwa a airport".zaro ido tayi tace"daman zasu zo shine basu faɗa min ba". murmushi yayi ya tashi yace"tace kar in faɗa Miki"."ai yanzu ka faɗa min".dariya yayi ya fita ita kuma tayi waya da ƙawayen ta ta faɗa musu ta sauka lafiya.kafin kace me gida ya cika da masu yin barka.sosai akaita farin ciki.
Bayan sallar azahar ne su Nasir suka dawo da sauri Arwa ta shiga suka gaisa da en parlour sannan ta wuce ɗaki,tana shiga wurin yaran taje tana cewa"ina baby's namu?".taje ta ɗauke ahan, nasrin ma ta shigo itama ta ɗauke ahana.khadija tace"ko irin sannu ma babu kawai se ki wuce wurin yara ko".Arwa tace"barni na fara gaisa wa dasu tukunnan ai naki na musamman ne". harararta tayi sanda suka gama sannan ta dawo ta rungume Khadija tana cewa"congratulations kin sauka lafiya"."se yanzu kika ganni?".Arwa tayi murmushi ta sake ta ta zauna tana cewa"Kinga sune basu Sanni ba amma ai ke munsaba ko?"."hmm,chan ta matse Miki Arwa, nasrin kema kin koya halin ta ko?".nasrin dake rike da ahana tace"haba dai na isa".suka sha hira sosai har dare yayi mutane suka watse se Arwa, nasrin,Nana da Habibah ne kaɗai a gidan gobe aunty Samira zata zo.
________+________
Alhamdullilah ansha bikin suna sosai daga en Abuja har en Maiduguri duk an hallaru anci an sha kuma aka watse lafiya kalau.Sunan yaro Ahmad sunan yarinya Maryam.
Nasir da Khadija kuwa soyayya sukeyi sosai.
❤️
