Yau bayan wata biyu kenan da auren su hafsat da Yasmin.khadija kuma busy dan sun kusan kammala makaranta duk da bata da lafiya amma dai taki taje asibiti.
Yau asabar Khadija tana zaune a parlour tana kallon tv,ta fara jin kamar abu yana ƙone wa ta zaro ido ta tashi dan ta ɗaura abinci a kitchen,tana shiga da sauri ta kashe gas ɗin ta buɗe tukunyar tana ta duba ya ƙone kawai taji zuciyar ta na tashi ta fara jin jiri kawai ta faɗi ta suma.
Nasir bayan ya tashi daga aiki direct gida ya dawo yayi parking sannan ya shiga parlour baiga Khadija ba kawai ya wuce ɗakin shi yayi wanka sannan yaje ɗakin ta ya duba har toilet bai ganta ba,sauka yayi parlour ya shiga cikin kawai ya kalle ta a kwance da sauri yaje wurin ta yaja ta jikin shi yaga ta suma da sauri ya ɗauko key na mota ya ɗauke ta suka wuce asibiti.
Yana isa suka wuce ciki da sauri nurses suka taimaka mishi aka shiga da ita binsu ya fara yi wata nurse ta tsayar dashi tukunnan ya zauna Kamar yayi hauka shi kaɗai yace"i wanted to tell you how I feel".ya saukar da kanshi dake ciwo sosai.bayan kusan minti talatin likita ya fito da murmushi a fuskar shi Nasir da sauri ya tashi yana cewa"ya jikin nata likita?".likita da fara'a yace"congratulations matar ka tana da cikin wata biyu da sati biyu".Nasir sujjada yayi yana cewa"Allah na gode maka Allah na gode maka".likita yace"kawai zazzaɓi ne da stress ne yasa ta suma amma in tasha magani za tayi sauki".Nasir ya tashi yana murmushi sosai yace"thank you doctor thank you so much".likita murmushi yayi yace"zaka iya shiga, ta tashi". gwaɗa kai yayi da sauri ya shiga ɗakin yaga Khadija na kwance tana kallon sama,da sauri yaje yayi hugging nata yana cewa"thank you so much Khadijah thank you for everything". Khadijah tace"thank you for what yaya Nasir".sake ta yayi yaja ta jikin shi yana cewa"albishirin ki". kallon tambaya tayi mishi sannan tace"goro fari sal".yace"kina da cikin wata biyu".zaro ido tayi tace"dagaske?". gwaɗa kai yayi ta sake ihun jin daɗi tace"zan zama mama".kara gwaɗa kai yayi yana murmushi,farin ciki take sosai da mamaki.doctor ya shigo ya rubuta musu magani sannan aka sallame su.
Direct pharmacy suka wuce Nasir ya saya magani kafin suka wuce gida,suna isa suka je ɗakin shi ya kwantar da ita akan gado yana cewa"daman bakya jin daɗi shine baki faɗa min ba". tura baki tayi tace"ai ban ɗauka har ze sumar dani ba". gwaɗa kai yayi yace"we will be parent". murmushi tayi tace"Abun mamaki wai nine zan zama mama".dariya yayi yace"gaskiya kam dan bakya jin magana". hararar wasa tayi mishi tace"ina jin magana nikam". gwaɗa kai yayi yace"me zaki ci?".a shagwabe tace"Ni ice cream zan sha".tashi yayi yace"an gama bari yanzu na sayo Miki". karkaɗa kai tayi tace"kai nake so ka haɗa min da kanka". murmushi yayi yace"ban iya ice cream ba ai se de in sayo Miki".tura baki tayi tace"Ni dai naka nake so".zama yayi yace"Khadija ban iya ice cream ba da gaske fa".kukan shagwaba ta fara yi Nasir ya jata jikin shi yace"shikenan ba ice cream nawa kike so,angama ki ɗaina kuka". gwaɗa kai tayi ya tashi ya fita ya wuce waje yaba me gadi ya sayo ice cream shi kuma ya zauna yana jiran shi a wajen,me gaɗin ya dawo ya mika mishi sannan ya shiga kitchen yasa ice cream ɗin a bowl ya kai mata.khadija ta kalle shi tace"harka gama?". gwaɗa kai yayi yace"sha kiji".sawa tayi a bakin ta tasha sannan ta kalle shi tace"yaya Nasir Ni zaka yi wa wayo, wannan ai ice cream na cravins ne".da mamaki ya kalle ta yace"har kinsan ice cream na ina ne wannan?". murmushi tayi tace"ina son ice cream sosai ai shesa".bashi bowl ɗin tayi tace"na ƙoshi gashi ka sha".yace"kiyi hakuri kisha kinji"."dagaske bazan sha ba bacci nake ji".karɓa yayi ya sauka dashi ya kai wa me gadi da ya dawo ya samu har tayi bacci.murmushi yayi ya wuce parlour.
_______________+________________
Yau Bayan wata uku da sanin cikin Khadija kenan.cikin ta yayi wata biyar kenan yanzu.ba karamin azabtar da Nasir take ba dan ko bacci me kyau baya yi,ko abu yana kusa da ita se ta kira shi tace ya ɗauko mata,aiki ma ba kullum yake zuwa ba dan tana laulayi ga zaɓe.
Yau su Anam da Maryam sun kawo wa Khadija jiya ra.anam ma tana da cikin wata shida.suna zaune suna hira a parlour Khadija ta baje akan kujera tana shan chocolate dake cike a bowl na hannun ta.anam tace"ke kam se son ciye ciye baki san zaki zama katuwa ba". Khadija ta harare ta tace"se me,ki barni naci haka ɗan cikina yace na ci sosai". dariya sukayi Maryam tace"Anam barta kinsan bai kamata a hana me ciki abinda take so ba".Anam tace"gaskiya kuma amma ai Ni bana ciye ciyen da take yi". Khadija tace"ke daman Ni daman,dakyar fa nake bacci dan wahala".Anam tace"kai ciki akwai wahala ina faɗa Miki,Maryam kema soon kin kusan ɗanɗana wa tunda dai auren ki saura wata biyar".Maryam tace"ki min hakuri Ni Ko nayi aure bazan haihu da wuri ba wallahi akan me zan sha wahala".Anam da Khadija suka fashe da dariya Khadija tace"kema dai kinsan faɗa kawai kike yi sede in ba na miji zaki aura ba". anam tace"ki faɗa mata dai,nima farko haka naso amma mijina yace shi yana son yara da wuri".Maryam tace"oho dai ai mijin ku da nawa daman ne".dariya tayi dariyar munafurci ta cigaba da shan chocolate nata.wayar Khadija ta fara ringing dauka tayi daga cikin wayar Nasir yace"Khadija ya jiki, ba abinda yake damun ki ko,me zan saya mika". tura baki tayi tace"ba abinda ke damina,ka sayo min eee--mm ko ma mene amma me daɗi".Nasir yace"kin tabbatar?". gwaɗa kai tayi kamar yana kallon ta se tace"ehh na tabbatar"."ok se na dawo". gwaɗa kai tayi ta katse wayar a daidai lokacin wayar Anam ta fara ringing dauka tayi bayan tayi magana ta katse wayar tana tashi wa tace"bari zan wuce mijina yazo".tsaki Khadija taja tace"shine baze ce ze shigo ba,can ta matse muku".Anam dariya tayi tace"se shegen masifa kamar wata tsohuwa". harararta tayi tace"oho dai kuma saura kice ina gaishe shi dan kin iya".Anam dariya tayi ta fita Maryam kuwa kara baje wa tayi sukai ta hiran su da Khadija akan shirin aurenta.bayan kusan minti talatin Maryam tace zata wuce sukayi sallama da Khadija ta wuce.
Nasir ya dawo daga aiki ya shiga parlour da sallama Khadija ta amsa, murmushi yayi ya zauna a kusa da ita yace"ya kike?".tace"lafiya na kalau,me ka sayo min".ta faɗa tana kallon ledan hannun shi,mika mata yayi ta buɗe,tana buɗe wa da sauri ta tashi ta wuce kitchen ta fara amai,Nasir ma Binta yayi yana shafa bayan ta harta gama ya bata ruwa tasha sannan suka fito parlour suka zauna yace"sannu ko".hararar shi tayi tace"ba ɗik kaika jawo ba kawai zaka je ka kawo min roasted fish". taɓe baki yayi ya gyara zama ya kalle ta dan ba karamin wahalar dashi take ba ai kuma ma ita tace kome ya sayo mata amma yanzu tana complain.ta kara cewa"Ni da ma ice cream ka saya min da ka burge Ni".Nasir ya sauke ajiyar zuciya yace"ai na tambaye ki kika ce min ko ma mene na sayo Miki".se tace"haka ma zaka ce ko to shikenan".ta faɗa tana kokarin fara kukan munafurci da sauri yace"ah ah kiyi hakuri bari naje na sayo Miki ice cream ɗin". gwaɗa kai tayi se ya fita ita kuma zama tayi a fili tace"ai wallahi se na rama duk abinda kayi min".
Se bayan sallar magriba ya dawo ya same ta a zaune akan sallaya tana addu'a,zama yayi kusa da ita yace"gashi na kawo Miki ice cream ɗin".kallon ledan tayi tace"na fasa bana son ice cream ɗin". kallon ta yayi irin na da haushin Nan yace"shine kika sa na sayo Miki".tace"yanzu bana so ai ɗazu ne nace maka ina so". gwaɗa kai yayi ya ajiye ledar kusa da ita ya tashi ze wuce sama tace"ina son awara yaya Nasir".da haushi ya juya ya kalle ta a zuciyar shi yana cewa daman haka ne maza suke shan wahala.khadija ta kara cewa"ko baza ka saya min ba?". murmushin dole yayi yace"na isa,bari nayi wanka tun dana dawo daga aiki ban shiga ɗaki ba fa".tura baki tayi kamar zatayi kuka tace"Ni yanzu nake so".sauke nunfashi da karfi yayi sannan ya gwaɗa kai ya wuce waje.bashi ya dawo ba se bayan sallar Isha a same place ya same ta yazo ya bata ta karɓa tace"thank you yanzu ne ka burge Ni".guntun smile ya mata sannan ya wuce ɗakin shi ita kuwa zama tayi ta ci kayan ta.bayan ta gama ta shirya bacci ta wuce ɗakin shi ta same shi har yayi bacci,kuka ta fashe dashi da sauri ya buɗe ido ya kalle yana cewa"me ya faru?".a kukan tace"ba kai bane baka jira Ni ba ka fara bacci". rolling na idonshi yayi ya sake jikin shi ya kwanta yana cewa"kiyi hakuri manta wa nayi". gwaɗa kai tayi ta kwanta a jikin shi tana cewa"Ni yau a jikin ka nake so na kwanta". gwaɗa kai yayi ta kwanta har bacci ya fara ɗaukan shi ta fara kuka ahankali da gajiya a Muryar shi yace"me ne ya faru?".a kukan tace"ba kai bane ka fara bacci".dan haushi ma kasa magana yayi ai kuwa ta kara volume na kukan se yace"to kiyi bacci bazan yi ba". gwaɗa kai tayi dakyar tayi bacci sanda ya tabbatar da tayi bacci sannan shima ya samu yayi bacci.
❤️
