Yau tunda Khadija ta tashi ta fara shiri dan yau su mama zasu zo,bayan tayi wanka tasa atampa wani brown da milk colour ta ɗaura ɗangwali sannan ta sauka ita da Arwa suka dafa abinci kala kala suka sa turaren wuta ko ina sannan suka zauna a parlour Arwa tace"karfe nawa zasu zo ne?". Khadija tace"ban sani ba amma baza su wani jima ba zasu zo".gwaɗa kai tayi se wayar Arwa ya fara ringing bata ɗauka ba kawai ta wuce upstairs Khadija kuwa danne danne take a wayar ta.bayan kusan minti biyar Arwa ta sauko ta zauna tana cewa"Khadija wai inji yaya Nasir kiyi hakuri ki bashi maganin da kika ce yana cikin ki". harararta tayi tace"ke ma dai kince yana cikina ai"."baya jin daɗi ne fa"."serious ne?".gwaɗa kai tayi Khadija ta tashi ta wuce ɗakin shi.tana shiga ta kalle yana kwance akan gado ya rufe jikin shi da duvet ahankali ta zo wurin shi ta zauna, ahankali yace"Khadija dan Allah ki bani magani na".se tace"nace maka yana cikina ai,na shanye gaba ɗaya"."dan Allah ki bani zan mutu".zaro ido tayi da taga abun nashi serious ne se tace"yaya Nasir sannu amma kasan likita yace kar na baka ko?"."just once Dan Allah".shiru tayi tana kallon shi se kuma ta tashi tace"just once,bari naje na kawo maka". gwaɗa kai yayi se taje ta ɗauko mishi da ruwa sannan ta shiga ta taya shi tashi se ya karɓa ya sha.khadija tace"yaya Nasir ka kwanta ka huta".gwaɗa kai yayi ya kwanta ta rufe shi sannan ta sauka wurin Arwa ta zauna,Arwa tace"kin bashi dai ko?"."me ruwan ki"."yaya nane fa". Khadija hararar wasa ta mata se tace"na bashi mana".tana faɗan haka akayi knocking na kofar parlour Arwa taje ta buɗe ai kuwa yau full house aka zo umma ne kawai bata zo ba dan tana Kaduna gidan aunty Hauwa.
Khadijah daɗi da farin ciki take ji dan ganin kowa yazo,suka wuce suka zauna Khadija tace"wannan irin surprise haka ai naɗau mommy da mama ne kawai zasu zo".Yasmin tace"daman ai muma zamu zo kawai shine muka haɗa hanya". mommy tace"yau dai Allah ya kawo Ni gidan Khadija". Khadija tayi dariya tace"daman ba ke bane kika ki zuwa". Abdul yace"nikam Khadija me sirrin ne wai?". Hafsat tace"kaima dai ka faɗa". mommy ne tace"ko abun ne yazo bamu sani ba". Khadija tace"wani abu kuma mommy?".mama dariya tayi tace"ka jita fa". mommy tace"ai kin fini sani".dariya tayi tace"kai mommy Ni ba abinda na sani kina gani na".habiba tace"mu dai Allah ya nuna mana Muzo musha suna". Khadija ta tura baki tace"chabɗijam". mommy tace"ka ji yarinyar Nan daman bakya so muga jikan mune?". Khadija tace"ga su hafsat da Yasmin zasu yi aure ai se su haifa muku". mommy tace"ja ira naki muke so".tura baki tayi tace"hmm mommy kenan toh Allah ya nuna mana".suka ce Ameen Khadija da Arwa suka tashi suka kawo ruwa da su drinks,mama tace"ina Nasir ne?". Khadija tace"na ce mishi ya huta yana ɗakin shi". hafsat tace"su masu miji manya". Yasmin tace"lafiya dai Koh?". Khadija tace"eh to yana jin zazzaɓi kaɗan shesa".mama tace"ayyah amma kunje asibiti ne?". Khadija tace"bamu jeba dan ba wani serious bane". mommy tace"da dai kunje asibitin ai ze fi". Khadija tace"ba wani serious bane yasha magani ma in yayi bacci zeyi sauki".Tahir yace"Toh Allah ya kara sauki".sukace ameen.sannan bayan minti kaɗan Khadija tace"kuzo muci abinci kuma ba'a min plako".Nana ta tashi tana cewa"daman wa zai Miki plako". Khadija tace"oho dai uwar masifa".nana tace"kika kaini". taslima tace"zaku fara ko dan Allah kuyi hakuri".mama tace"ba'a shiga tsakanin su ai yanzu se kiji kunya".taslima tace"gaskiya kam bari nayi shiru".zama sukayi Khadija da Arwa sukayi serving na abincin sannan suma suka zauna kowa se santin abinci yake yi har suka gama suka tattara kwanukan aka kai kitchen sannan suka wanke gaba ɗaya saura kuma suna parlour ana hira,haka har lokaci ya tafi wai zasu tafi gida Khadija tace"haba dai da sauri haka bari na duba yaya Nasir". upstairs ta wuce ɗakin shi direct ta shiga taga yana zaune akan gado da laptop a cinyar shi, kallon mamaki tayi mishi sannan tace"yaya Nasir harka warware kenan". kallon ta yayi yace"ai daman in Nasha magani zan warke".se tace"toh su mama suna parlour kazo ku gaisa".gwaɗa kai yayi ya tashi suka fita suka sauka ya gaisa dasu sosai har suka ɗan yi hira suka tambaye ya jikin shi yace da sauki sannan sukace zasu tafi Khadija ta dinga cewa mesa zasu tafi da wuri amma dai haka suka tafi ta raka su har mota sukayi sallama sannan ta dawo parlour ta zauna a kusa da Nasir tace"wai amma da gaske ka warke". murmushi yayi yace"ya baki mamaki ne?".gwaɗa kai tayi.dariya yayi yace"daman ai nace Miki magani na zaki bani kawai"."toh ai daga yau bazan kara baka ba wallahi". murmushi yayi yace"ai gakinan bani da matsala".hararar wasa tayi mishi yayi murmushi se Arwa tace"yaya Nasir yaushe zaka fita damu ne?"."yaushe kike so mu fita?". Khadija tace"gobe tunda ba makaranta". gwaɗa kai yayi yace"ok gobe se ku shirya mu zagaya gari".Arwa tace"an gama".Nasir ya tashi yace"bari zan fita wani wuri amma bazan daɗe ba". Khadija ta kalle shi tace"to se ka dawo". gwaɗa kai yayi sannan ya fita, Khadija kwanciya tayi akan kujera tace"Arwa in an kira sallah ki tayar dani kinji".Arwa gwaɗa kai tayi itama ta kwanta Khadija tace"toh inkinyi bacci wa ze tayar damu?".Arwa ta "oho". Khadija tace"ke kika sani". kwanciyar su sukayi har bacci ya ɗauke ke su.
Knocking na kofar parlour ne ya tayar da Khadija taga gari yayi duhu da sauri ta tashi tana mamakin irin baccin da tayi.ahankali ta tashi taje ta buɗe kofar taga Nasir ne a kofar, tsaya wa tayi tace"se yanzu?". gwaɗa kai yayi se tace"yaya Nasir se yanzu?". kallon ta yayi yace"duka na zakiyi?".shiru tayi tana kallon shi daya gaji yace"Khadija ki matsa na shiga".tace"yaya Nasir tun karfe nawa ka tafi amma se yanzu zaka dawo kuma kaga ko sallah bamuyi ba dan baka zo ka tayar damu ba". jingina yayi a kofar yana kallon ta se yace"Khadija daman se na faɗa Miki karfe nawa zan dawo ne tukunnan zan fita ko kuma daman nace Miki zan dawo na tayar da ke daga bacci".ya kara cewa"gafara min a kofar Nan kafin nayi maganin ki". harararshi tayi tace"Anki a matsa kayi abinda zakayi".wani haushe ne ya kama shi ya tura ta ahankali daga kofar yace"ki wuce kiyi sallah". kokarin ture shi waje ta fara yi Nasir da haushi ya rike hannun ta dukka biyu da kaita bango yace"don't try me!!". tsoro ta fara ji yadda idonshi ya fara chanja wa.sake ta yayi ya wuce ɗakin shi,taje wurin Arwa dake shan bacci ta fara buga ta tana cewa"ke Arwa ki tashi dare yayi bamuyi sallah ba".Arwa ta buɗe ido sannan ta zauna tace"karfe nawa ne". Khadija tace"karfe takwas na dare".Arwa zaro ido tayi da sauri ta wuce sama Khadija tayi alwala a toilet dake parlour se tahau itama ta biya sallolin dake kanta.bayan ta idar ta wuce cikin closet nata ta ɗauka sleeping dress nata da hula tace"Arwa se gobe da safe".Arwa dariya tayi tace"munafuka daman jiya isakanci ne ashe".tsaki Khadija taja sannan tace"oho dai ba ruwan ki".fita daga ɗakin tayi ta wuce ɗakin Nasir da sallama ta shiga ta samu har yayi shirin bacci,ajiye kayan ta tayi ta shiga toilet,ta fara cire riga kawai taga kenkeso a gefen ta ihu tayi ta fito daga toilet ɗin da gudu tana cewa"wayyo Allah yaya Nasir!!!".da sauri ya tashi itama tazo jikin shi ta rike shi sosai,Nasir yace"me ne ya faru?". Khadija tace"yaya Nasir kenkeso a toilet".dariya ya fara dan sosai abun ya bashi dariya ita kuwa kallon shi take kamar ta shaƙeshi tace"wai me haka ne kana min dariya".yace"yanzu akan kenkeso ne kike wannan ihun haka?".kara tura baki tayi tace"toh ai tsoron shi nake ji".yace"shikenan yanzu kin fasa wankan kenan?". girgiza kai tayi se yace"toh yanzu ya za'ayi tunda dai malam kenkeso yana toilet kuma Ni Nasir ba ruwana dashi". kallon shi tayi tace"ba ruwan ka kuma,to ya zanyi nayi wankan kenan?".se yaja hannun ta ya fara tafiya wurin toilet ɗin yana cewa"se ki nuna mishi bakya tsoron shi kawai".jan hannun ta tayi tace"toh ai ina tsoron shi kai kaje mana"." ai bani zan yi wankan ba"."Ni na fasa wankan anan,a ɗaki na zanyi abina"."tsaya toh bari naje na duba shi".gwaɗa kai tayi ya shiga toilet ɗin se ya kalle kenkeson ma fa karami ne abun ya kara bashi dariya yace"wallahi Khadija kinji kunya"."oho dai Ni ka fitar dashi".ya fitar dashi har waje ita kuma tayi wanka ta ɗaura towel ta fito Nasir yana zaune ya fara kallon ta tun daga sama har kasa se ya kashe mata ido,da sauri ta ɗauka kayan ta ta shiga closet tana cewa"yaya Nasir innan ɗan iska ne fa".ta gama se ta fito ta kwanta ta akan gadon, shi kuma laptop nashi yake dubawa har bacci ya ɗauke ta,shima bayan ya gama ya ajiye laptop ɗin ya kwanta yaja ta jikin shi har shima bacci ya ɗauke shi.
❤️
YOU ARE READING
Khadeejah💙
Roman d'amourKu biyo NI dan ganin rayuwar Khadija da Nasir cikin auren haɗi